𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamun alaikum Malam nakan ji ana cewa Tarawih da Tahajjud shin mene ne
bambancinsu?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To bayin Allah Sallar tarawihi da tahajjud duk ana kiransu Sallar dare wato
tsayuwar dare ke nan illla iyaka lokacin yinsu ne kawai ya bambanta su har
sunan nasu shi ma ya bambanta.
TARAWIHI: shi ne ayi sallar dare kafin ayi barci kamar dai yadda masallatanmu
sukeyin ta bayan isha'i cikin watan ramadan to idan akayi sallar kafin ayi
bacci shi ne ake kiranta da tarawihi.
.
TAHAJJUD: ita ce ake yin ta bayan an ɗan yi bacci an
farka to wannan baccin da akayi aka farka sannan akayi sallar to shi ne ya sa ake
kiranta da tahajjud maimakon tarawihi Amma dai dukkansu A dunkule tsayuwar dare
ko kuma ince sallar dare ake kiransu.
WALLAHU A'ALAM
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DiXƘRlvdel9IbPpTvLEBYK
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.