Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene Ne Hukuncin Shakar Kamshin Abinci Ga Mai Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam in ina girki ina yawan shakar kamshin abinci wani sa'in kamar yana shigewa makogwaro. Shin Malam hakan baya karya azumi? Sannan Malam ruwa ne ya shige min kunne kuma sai na ji kamar ya tawo ta makoshina kuma ya zuba ne a bisa rashin sani. Dan Allah Malam hakan baya karya azumi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To baiwar Allah sha'kar kamshin abinci baya karya azumi kai babu laifi ki ɗanɗana abincin yayinda kike girkin Matukar dai baki haďiye ba wato kin furzar tom in Shã Allahu azumin yana nan illah iyaka ki kuskure bakin bayan ɗanɗana abincin.

Dangane da shiga ruwa cikin kunne shi ma baya karya azumi in Shã Allahu sabida haka azuminki yana nan babu abin da ya sameahi

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DiXƘRlvdel9IbPpTvLEBYK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments