Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Halartar Sallar Idi Ga Mai Takaba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Don Allah malam ya hallata mai takaba ta je sallar Idi? Na gode Allah ya ƙara wa malam lafiya.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, Matar da mijinta ya rasu wajibi ne ta yi idda (takaba) na wata huɗu da kwana goma kamar yadda aya ta 234 na suratul Baƙara ta tabbatar. Idan kuma mai ciki ce mijinta ya rasu, iddarta za ta kasance har zuwa lokacin da za ta haifo wannan ciki ne.

Ya wajaba a kanta ta zauna a gidanta a lokacin iddar, ba za ta fita ba sai da uzuri na Shari'a, ko wata buƙata ta tilas, daga cikin uzurori na Shari'a su ne kamar zuwa asibiti neman magani, ko zuwa wurin alƙali idan ya buƙaci hakan saboda tattara bayanan dukiyar gado, ko wasu daga cikin uzurori da suka tilasta mata fita, amma idan ba wani sababi, to ba ya halasta ta fita daga gida, a bisa wannan bayani sai ya zama ba ya halasta a gare ta ta fita ziyara zuwa wurin maƙwabtanta, ko ƴan uwanta, ko halartar sallar Eidi, ko abin da ya yi kama da haka, za ta zauna a gida ne har ta kammala takabar...

Kamar yadda Sheikh Ibn Uthaimeen ya bayyana. Dubi Fataáwá Nurun Alad Darb (19/2).

Imamu Malik a cikin Muwaɗɗa ya ruwaito cewa Sayyiduna Umar ɗan Khaɗɗab Allah ya ƙara masa yarda ya kasance yana hana waɗanda mazajensu suka rasu zuwa aikin Hajji. Muwaɗɗa (2/591).

Wato wannan sai ya nuna tsananin yadda Shari'a ta buƙaci mace mai takaba ta zauna a ɗakinta ba tare da zuwa ko'ina ba. Saboda haka mace mai takaba ba ta da damar fita zuwa sallar Eidi, fitar da take da damar yi shi ne fitar da ta zama saboda uzuri ne karɓaɓɓe a Shari'a.

Kawai ta zauna a ɗakinta ta yi ta maimaita kabbarbarin da ake yi a wannan lokaci, kamar: ALLÁHU AKBÁR, ALLÁHU AKBÁR, ALLÁHU AKBÁR, LÁ'ILÁHA ILLALLAH, ALLÁHU AKBÁR, ALLÁHU AKBÁR WA LILLÁHIL HAMDU.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments