Ticker

6/recent/ticker-posts

Mece Ce Waƙa?

  Daga taskar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya.

Abdullahi Bayero Yahya
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu ƊanfodiyoSakkwato
Email: 
bagidadenlema2@gmail.com 
Phone: 
 07031961302

Ma’anar Waƙa:

Waƙa ita ce maƙerar mawaƙi. A nan ne yake narka kalmomi ya fito da saƙonsa zuwa ga al’umma. A nan ne kuma yake narka su ya yi maganganun hikima, hikima ta harshe ko ta hanyar rayuwa.

A nazarin waƙa ana iya bayyana ma’anar waƙa da cewa:

Waƙa tsararriyar maganar hikima ce da ta ƙunshi saƙo

cikin zaɓaɓɓun kalmomin da aka auna domin maganar

ta reru ba faɗuwa kurum ba.[1]

Waƙa magana ce ta tsakanin zukata ko bayan cewa tunani ma yana naƙaltar ta. Abin nufi a nan shi ne ita waƙa takan yi tasiri ne kai tsaye kan zuciya fiye da sauran nau’o’in magana.[2]

A fayyace ana iya cewa waƙa magana ce da aka zayyana, ba wadda aka sako kara-zube ba. Magana ce wadda aka aza bisa sanannun ko ayyanannun ƙa’idoji waɗanda ke daidaita furuci da sauti, su kuma tilasta zaɓar kalmomi domin dacewar ma’ana da furuci. Ta haka ne maganar take zuwa babu kaura da juna na furuci ko kalmomi ta fuskar daidaiton tsawon gaɓoɓi, saɓanin magana ta al’ada ko yau-da-kullum.

Ta yin la’akari da bayanin da ya gabata za a lura da cewa akwai wasu muhimmam sigogi waɗanda a nan za a kira sigogin tarayya. An kira su ne da wannan suna saboda duk ana samun su ko a waƙar baka ko rubutatta.



[1] Yahya, A.B. (1997), Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna:  FISBAS Media Services, shafi na 4

[2] Duba Ɗalhatu Muhammad cikin ‘Muƙaddima’ wadda ya rubuta kan A.B.Yahya(1997) Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna:  FISBAS Media Services, shafi na v.


Post a Comment

0 Comments