Ticker

6/recent/ticker-posts

Mamaren Manazarci Kan Wane Ne Mawaƙi

  Daga taskar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya.

Abdullahi Bayero Yahya
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu ƊanfodiyoSakkwato
Email: 
bagidadenlema2@gmail.com 
Phone: 
 07031961302

1.0      Gabatarwa

1.1 Ƙimar Nazarin Waƙa

Ɗaliban waƙa da dama na wannan Jami’a, wato Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, suna sane da cewa nazari ko sharhin waƙa ba abin da za a iya gamawa ba ne. Haka nan kuma malamansu sun sha jaddada musu cewa ra’ayin kowane manazarcin waƙa bai taɓa kasancewa dil ba. Kai! Hasali, ilmi gaba ɗayansa ba gama neman sa ake yi ba. A dalilin haka ne a kowace jami’a ake da Maƙalar Ƙaddamarwa, ko kuma “Bukin Shimfiɗa Buzun Karatu”, kamar yadda Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya raɗa mata suna. Jami’a ta kallafa wa duk wanda ya zama Farfesa da ya gabatar da wannan maƙala. Abin nufi shi ne a lokacin ne zai shiga neman ilmi, ba wai sannan ne ya kai aya ba.

1.2              Tarihin Maƙala

Haƙiƙa an yi shekaru masu ɗan dama ina lalabe da tawan yadda taken wannan maƙala zai kasance. Akwai tunanin tsara waƙa wadda za ta bayyana wa talakkawan ƙasashe masu tasowa kisisina da makircin da Turai da Amerika suke yi tare da tsoratar da shugabannin ƙasashen masu tasowa don su kitsa ƙullalliyar wasashe dukiyar ƙasashensu. Kuma sai wani tunani ya zo yana cewa, kai rubuta maƙala a kan zalunci da munafucci da baki-biyun waɗannan ƙasashe ke yi a siyasar duniya tattare da tilasta mana bin hanyar rayuwa da tsarin siyasa ɗaya tak wadda suka ƙirƙiro, kuma wai ko kusa kada mu yi tunani da ƙwaƙwalwarmu har mu bi akasin haka. Addinin Nasara ke nan! Haka kuma sai wani tunani ya mamaye ƙwaƙwalwata kan in gudanar da bincike mai ƙudurin samo amsoshin tambayoyi guda biyu:  Shin littafi nawa ne na Shehu Usmanu ɗan Fodiyo da mabiyansa ake karantar da su a makarantun furamare da sakandare na aƙalla jihohin Sakkwato da Kabi da Zamfara? Shin kuwa ana karatun tarihin waɗannan bayin Allah a waɗannan makarantu na jihohin nan? Wani tunani yakan zo min na in rubuta a kan yadda neman ilmi musamman na addini yake neman kuɓuce mana a dalilin yadda iyaye da shugabanninmu suke ƙyale ko ingiza matasa ga yin ƙwallo. Na sha ƙirga yawan filayen ƙwallo daga bakin gidana na Runjin Sambo, in bi titin da ya zagaye Sakkwato zuwa shiyyarmu ta Giɗaɗawa. Ƙidayar sai ta ɓace mini saboda yawan filayen na ƙwallo. Kuma lokacin da filayen ke cika shi ne daga Azzuhur zuwa goshin Magariba. Wannan kuwa shi ne daidai lokacin karatun makarantun allo na yaran da ke cika waɗannan filayen ƙwallo maƙil a Sakkwato! A yau makarantun da wasu suka kakkafa waɗanda, wasun nan da ba al’adunsu ko addininsu ɗaya ba da iyayen waɗannan yara da ake ingizawa filayen ƙwallo, sun kusan riɓanya makarantun allon Sakkwato!!! Haka kuma na so in yi maƙalar ƙaddamarwar tawa a kan Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, ina mai bin diddigin tarihinta ta fuskar shugabannin da suka samar mata suna, in kuma ambaci rawar ‘yan ɓangarancin ƙungiyoyin addini, ba wai addinin ba; da waɗanda suka haskaka jami’ar da kuma ‘yan ka-fi-gwamna!! Tunani ya zo na in tsara waƙa mai cusa zimmar da za ta sa ɗalibai su yi ta ƙirƙiro na’urorin kimiyya da fasahar ba tare da sun bukaci kayan haɗi daga ƙasashen waje ba. A cikin wannan waƙa in bayyana wa matasanmu irin ciyyon da nake ji na kuɓucewar da dama ta yi min ta yin nazarin kimiyya da fasaha. Kai!, da a yayin gabatar da wannan waƙar a yau, kuma a wannan dandali ne zan gabatar da makamin da sai da izninsa (danna wata ƙusar makamina) ne duk wani makamin ƙare-dangi zai iya tashi!!!

Cikin irin wannan hali ne na kasance har wasu ɗalibaina suka tunatar da ni cewa, “Don Allah Mallam!, mu dai ka fayyace mana, da mu da sauran ɗaliban waƙa shin shi mawaƙi wane ne shi?” Nazarin waƙa suka san ni da shi. Kome kuwa son da nake da na in yi rubutu kan waɗancan abubuwa, ai ba fagagena ne ba. Waɗannan masana (yanzu kam sun zama yadda na yi gurin su kasance) su ne Farfesa Aliyu Muhammad Bunza da Dokta Ibrahim S.S. Abdullahi. Ba su son a bar A.B. Yahya a baya. A wurina su ne waɗanda baitocin nan ke magana a kai:

11.Akwai daɗin da yaz zam ba irinai

 Fa sai ko ɗan da yaz zam salihi na

 

12.Kana yawo cikin duniya ga san nan

 A ce gwarzon ga ɗalibu naka shi na

 

13.Ku san haka ya fi albashin ƙasag ga

 Mutum biyu ɗai ka son haka ‘yanuwana

 

14.A ce wannan da kat tayas shi fi ka

 Mahaifa su da Mallam ag ganina

 

Watakila waɗannan ‘ɗalibai-malamai’ sun tursasa wa ‘mallam-takwaransu’ ne domin a gaba su yo sharhi kan wannan maƙala, kamar dai yadda ya umurce su fiye da shekaru ashirin da suka wuce:

 

16.Mutun duk ajizi ne ko wane na

 Bale ni Abdu Bayaro nai shuruna

 

17.Ku yo gyara ga aikin nan da niy yo

 Maƙaluna da laccocin ajina

 

18.Mafaa’iilun mafaa’iilun mafaa’il

 Ma’auni ne na waƙaɗ ɗalibaina

 

19.Na ce lale adabo sai adabo

 Hazaj ne sai ku auna sha’iraina.

(A.B.Yahya:  Bankwana da Ɗaliban Waƙa na 1987/88)

 

Amsa wannan kira na Bunza da Abdullahi ya haifar da wannan maƙala ta yau, mai take, “Mamaren Manazarci Kan Wane ne Mawaƙi ”. Zai dace idan muka fara da sanin fagen shi mawaƙin kamin mu san shi wane ne shi. Da ma dai idan kana neman mutum gidansa ne za ka je.

2.1              Ma’anar Waƙa:

 

Waƙa ita ce maƙerar mawaƙi. A nan ne yake narka kalmomi ya fito da saƙonsa zuwa ga al’umma. A nan ne kuma yake narka su ya yi maganganun hikima, hikima ta harshe ko ta hanyar rayuwa.

A nazarin waƙa ana iya bayyana ma’anar waƙa da cewa:

Waƙa tsararriyar maganar hikima ce da ta ƙunshi saƙo

cikin zaɓaɓɓun kalmomin da aka auna domin maganar

ta reru ba faɗuwa kurum ba.[1]

 

Waƙa magana ce ta tsakanin zukata ko bayan cewa tunani ma yana naƙaltar ta. Abin nufi a nan shi ne ita waƙa takan yi tasiri ne kai tsaye kan zuciya fiye da sauran nau’o’in magana.[2]

A fayyace ana iya cewa waƙa magana ce da aka zayyana, ba wadda aka sako kara-zube ba. Magana ce wadda aka aza bisa sanannun ko ayyanannun ƙa’idoji waɗanda ke daidaita furuci da sauti, su kuma tilasta zaɓar kalmomi domin dacewar ma’ana da furuci. Ta haka ne maganar take zuwa babu kaura da juna na furuci ko kalmomi ta fuskar daidaiton tsawon gaɓoɓi, saɓanin magana ta al’ada ko yau-da-kullum.

Ta yin la’akari da bayanin da ya gabata za a lura da cewa akwai wasu muhimmam sigogi waɗanda a nan za a kira sigogin tarayya. An kira su ne da wannan suna saboda duk ana samun su ko a waƙar baka ko rubutatta. Ga bayaninsu daki-daki:  

2.1.1Zaɓen kalmomi

Wannan yana nufin cewa mawaƙi (na baka ko mai rubutawa) gwani ne wanda ke tsayawa ya zaɓo kalmomin da suka dace da abin da zai faɗi cikin waƙarsa (zai zaɓo su kamar yadda masaƙi yake zaɓo zaren da zai dace da saƙar da zai yi). Mawaƙi mafaraucin kalmomi ne. A koyaushe shi mai zaɓo kalmomi ne cikin rumbun kalmomin harshe domin ya yi amfani da su ya saƙa saƙonninsa zuwa ga al’umma ko ya bayyana abin da ke cikin zuciyarsa, abin da ya ɗanɗana a rayuwarsa.

Zaɓin ya dogara ne kan ma’ana da haliyya da siffofin da kalmar da mawaƙi ya zaɓo za ta haifar a zukatan masu sauraren sa. Mawaƙi zai yi la’akari da tasirin da yake nufin kalmar da zai zaɓo za ta yi kan mai sauraren ko karanta waƙarsa. Dubi wannan baiti:

Ban da kowa birnin ga baicinka

Ba ni bin kowa sai da yardakka

Wanda dut yac ce za shi soke ka

Yanzu in ya ga ni sai ya lele ka

Ya sani fuskata takobi ta

 (Alƙali Haliru Wurno: Yabon Sarkin Musulmi Abubakar III, Safiya Da Gaskiya Taka Aiki)

 

Kalmar ‘lele’ ta dace ainun cikin wannan baiti saboda tsananin kishin da ta yi da kalmar ‘soke’ a ɗango na uku. Mutum ne ya tsayu ga sai ya soki Sarkin Musulmi amma da ganin Haliru Wurno tilas sai ya yi watsi da batun sukar Sarkin Musulmi. Ba nan ya tsaya ba, nan take ya rikiɗe ya zama mai tsananin begen Sarkin. Wannan shi ne abin da kalmar ‘lele’ take dasawa cikin fahimtarmu.

Haka nan kuma kalmar ‘takobi’ ta dace ƙwarai domin irin ma’anar da ta ba fuskar Haliru a zuciya da idon mai son ya soki Sarkin Musulmi. Takobi dai makami ne wanda nan take zai fille kan mutum kuma don haka aka yi shi. Saboda haka ganin sa zai tsoratar da duk mai hankali, musamman idan ya san cewa takobin a hannun ɗan adawa yake. To da mai sukar sarki ya ga Haliru sai tsoro ya kama shi saboda sanin cewa fuskar nan ta shi Haliru yanzu tana gamawa da shi - wato za ta yi sanadin tafiyarsa Lahira ba da shiri ba, tamkar yadda takobi kan yi wa mutum.

Da wuya mutum ya iya samo wasu kalmomi biyu waɗanda za su fi waɗannan dacewa a wuraren da Haliru ya kawo su. Zaɓin ya dace ainun.

Musa Ɗanƙwairo a nasa zaɓen kalmomi ya ƙulla wannan ɗan waƙa:

Gulbi ya cika ya ba daji

Sai wawa sai baƙo

Kowas shiga ya ɓace ba ya tasowa

 (Alhaji Musa Ɗanƙɓwairo:  Shirya Kayan Faɗa)

Idan gulbi ya yi cikowa har ya mamaye wuraren da ba nan ne hanyar da ya saba da bi ba, to kuwa rashin sani ko na rashin hankali kurum zai kai mutum shigarsa. Duk gulbin da ya kasance haka to kuwa duk wanda ya shiga cikinsa shi tasa ta ƙare. Mutanen da gulbin ya bi ta garinsu sam ba su ko mafarkin shiga cikinsa a irin wannan hali. Saboda haka ne Ɗanƙwairo ya kawo maganar wawa, (kalmar da ma’anarta ta haɗa da wauta da hauka ko rashin hankali) da kuma baƙo.

Waɗannan kalmomi na ‘gulbi’ da ‘cika’ da ‘daji’ da ‘wawa’ da ‘baƙo’ da ‘ɓace’, kalmomi ne da suka taimaki mawaƙi ga ƙirƙiro ko zayyana yanayin cikowwar gulbi da kuma wawan da ya zo zai auka cikinsa. To duk wannan salon zayyana da na kinaya suna nufin wato, maigidan Ɗanƙwairo ne, ‘Yandoton Tcahe Alu. Shi ne gulbin, mai shiga cikin gulbin kuwa shi ne ɗan sarkin da ke jiran sarautar wanda kuma ke jin yana iya taƙalar ‘Yandoto. ‘Yandoto, basaraken Tcahe, sarki ne wanda ya ƙasura ga sarauta, martabarsa da ƙarfi da ikonsa sun kai ko ina a ƙasar Tcahe da duk inda ake faɗa a ji kamar a fadar Sarkin Musulmi da ofishin Sardaunan Sakkwato, Firimiiyan jihar Arewa. Saboda haka ‘gulbi’ ne wanda ya cika har ya batse (wato, har ya ba daji). Shi kuwa ɗan sarautar Tcahe shi ne ‘wawa’ ko ‘baƙon’ da ke son ya zama mai riƙon Tcahe. Ya ce wai ya tunkari riƙa wannan sarauta ta ‘Yandoton Tcahe, alhali wannan ‘gulbi’ (‘Yandoto Alu) yana a kai, haƙiƙa wauta ce ko rashin sani da hauka!

2.1.2        Tsara magana

Mawaƙi bai zuba magana haka kara zube. Wato dai furucin da ke cikin waƙa a tsare yake, cikin tsari fitacce ba kamar na wasan kwaikwayo ko rubutun zube ko labari ko tatsuniya ba. Ba a samun tuntuɓen harshe (karo da juna) a furucin waƙa, idan kuwa aka samu to ba waƙa ce ba. Manazarta zube ko wasan kwaikwayo su yi min afuwa, amma wannan siga a ganina ita ke sa mawallafa fagagensu sanya waƙa cikin fagagensu don ƙoƙarin yin kwalliya da jan hankali da jaddada saƙo. Wannan tsari aunanne ne, shimfiɗe kuma baje kamar tsarin saƙar gwado ko hula ko zana, inda ba za ka sami rikicewa ko cakuɗewar zubin zare ko gamba ba. Dubi wannan misali:

Na kiraye Ka Mai agaji Wahidun

Ka yi horo a roƙe ka baiwa Kakai

 (Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu:  Yadda Ya Kamata Najeriya Ta Arewa Da Mutanenta Su Zamo)

 

A wannan baiti za a lura da cewa furuci na tafiya bai ɗaya ba tare da tuntsurewa ba. Abin nufi shi ne, akwai wani tsawon furuci da ke maimaita kansa a duk tsawon baitin, babu ƙari babu ragi. Tsawon furucin kuwa shi ne doguwar gaɓa da gajera da kuma doguwa, waɗanda a ma’aunin waƙa ake alamtawa da –v-.

Irin haka ne za mu lura a wannan ɗan waƙa:

Amadu diba mazan gaba dibi na baya

Ka diba dama ka diba hauni

Ka san jama’ag ga da an nan

Ƙauye da birni ba su da jigo sai kai

Maɗi bai kai ga zuma ba

Kowal lasa shi ka hwaɗi

Kwandon wake bai kai ga damen gero ba

Ai ɗan akuya ko ya yi ƙahoni

Ya san bai yi kamar rago ba

Ɗan sarki komi yaƙ ƙasura

Kak ka raba shi da bawan sarki

 (Ibrahim Narambaɗa: Waƙar Sarkin Gobir na Isa, Amadu Bawa – Gogarman Tudu Jikan Sanda) .

 

 

2.1.3        Rerawa

Rerawa ita ce furta magana cikin daidaitacciyar kuma aunannar murya wadda ba ta karyewa. Rerawa ita ce babban gimshiƙin da ke shafuwar magana ta rikiɗe ta zama waƙa. Rashin wannan gimshiƙi shi ne rashin waƙa, tamkar dai idan babu azara da gimshiƙi ga shigifar zamanin Narambaɗa, domin /Mi aƙ ƙarhin shigifab ba su ba/.

Tsari da awon da mawaƙi kan yi wa furucin maganarsa su ke sa maganar ta zama waƙa. Muddin waɗannan abubuwa guda biyu, wato tsari da awo, ba su haifar da iya rera maganar ba, to kuwa ba ta kai ga zama waƙa ba. Abin nufi shi ne, duk waƙar da ba ta reruwa to ba waƙa ce ba.

Lura da cewa rerawa wani rauji ne na furuci da murya na magana da ke fita bai ɗaya ba tare da gargada ko karabkiyar baki ko tuntuɓen harshe ba. Daidaitaccen tsarin sauti ne “kamar yadda zuciya ke bugawa a kan kari, a tsare ba barkatai ba.”[3] Dubi wannan baiti na Alhaji Garba Gwandu:

Hafizu Ka ɗamre bakin la’imi in ya so yi min sharri

Sharrin dud da yaƙ ƙulla bayyane ko cikin sirri

Banye ƙulle-ƙullenshi mai sam min suwa tamkacin hairi

Ko da ya rubuta a kece hissai ma cikin tsari

 Daƙushe ƙoƙarin duk da yay yi na sharri Jalla don salla

(Alhaji Garba Gwandu; Ijababbiya Ta Biyu)

 

Duk da cewa ɗangogin wannan baiti suna da matuƙar tsawo, wannan bai hana furta su su tafi miƙe totar ba, ba tare da karo da juna na furuci ba. Wannan kuwa shi zai sa ɗangogin su reru.

Haka nan kuma idan muka duba abin da Shata yake furtawa a nan ƙasa za mu lura da cewa rerawa ta tafi bai ɗaya ba tare da gargada ko tuntuɓen harshe ba. Idan aka saurari Shata a yayin da yake rera waƙar za a lura da cewa yana jinkirta furta wasu gaɓoɓin kalmomi kafin kalmomin su kammala. Wannan shi ne tasirin tsari da awon kari waɗanda gimshiƙai ne masu haifar da reruwar waƙa. Ga ɗiyan waƙar:

Da yai haka sai na ga*no yai haka

Malam Babba na Ƙofag Gabas

 

Ya kimtsa sai na ga* ya yo haka

Malam Babba na Ƙofag Gabas

 

Ya sake shiryawa na ga yai wani haka

Malam Babba na Ƙofag Gabas

 

Ya fid da uku ya ɗauke shida

Malam Babba na Ƙofag Gabas

Sannan ya ɗauke huɗu ya ɗauke tara

Malam Babba na Ƙofag Gabas

 

 Na ga yai dib da ni yana al’ajab

Malam Babba na Ƙofag Gabas

 

Ya ce man kai makaɗi mai kiɗa

Sha shagalinka cikin duniya

Dub ba abin da* zai tamma ka

Gidan tara kake

Gani kuma nike

Malam Babba na Ƙofag Gabas

(Alhaji Muhammadu Shata:  Malam Babba na Ƙofar Gabas)

 

A wurin da aka yi alamar * ana nufin Shata ya ɗan tsaya kafin ya furta gaɓar da ke biye, ko da kuwa gaɓoɓin sun kasance masu ba da kalma ɗaya ne, misali ga*no kalma guda suke bayarwa.

2.1.4Saƙo

A fagen Nazarin Rubutacciyar Waƙa an fi kiran wannan da ‘jigo’, yayin da Nazarin Waƙar Baka mabiyan Sa’idu Gusau ke cewa ‘turke’. Jigo yana nufin manufar da waƙa take son isarwa ga mai karanta ta ko sauraren ta. Kowace waƙa tana ɗauke da saƙo kuma wannan saƙon ne ake ƙoƙarin a isar ta yin amfani da duk abubuwan da muka ce waƙa ta keɓanta da su na musamman. Misali waƙar da Alƙali Haliru ya yi wa Alhaji Giɗaɗo Yabo mai suna ‘Gudale’ tana ɗauke da jigon yabo ko ƙauna.

Akwai babban jigo akwai kuma ƙarami. Babban jigo shi ne wanda ya mamaye waƙa, ƙarami kuwa shi ne wanda da shi ne mawaƙi ya gina babban jigon waƙarsa. Misali, waƙar da aka yi ɗauke da babban jigon yabo kan iya ƙunsar ƙananan jigogi kamar kyauta da asali da kyawawan halaye da riƙon addini da bajinta da dai makamantansu.

A nazarin waƙar baka an fi kiran jigo da sunan turke ko tubali. Turke shi ne a nazarin rubutattar waƙa ake kira babban jigo, a yayin da tubali shi ne ƙaramin jigo.

2.1.4        Hikima

Hikimar waƙa kashi biyu ce. Akwai hikima wadda ta jiɓinci ilmi, wato kamar bayyana hanyar rayuwa. Misali cewar da mawaƙi ya yi:  

Idan dabba tana sauri ga turke

 Da amfanin da tas san za ta iske

 (Alƙali Bello Giɗaɗawa: A Bi Gaskiya Ad Daidai),

 

ai ya kawo hikima ta ilmin da ke bayyana rayuwa ne. Wato mutum da hankalinsa ba zai kai kansa ga halaka ba. Idan kuwa ka ga ya fuskanci abin da kake ganin yana tattare da halaka, to ka tabbata cewa shi ya san ribar da zai ci, kai ne ba ka gane ta ba sai dai halaka. Ƙoƙarin maƙalewa ga mulki bayan wa’adin shugaba ya cika, musamman a ƙasashe masu tasowa, tattare take da haɗarin gaske. To amma sai ka ga wasu sam wannan farar gaskiya ba ta dame su ko misƙala zarratin ba. To da walakin goro cikin miya. Shi ya san daɗin da ke tattare da mulkin, wanda mu ba mu san da shi ba.

Hikima ta biyu ita ce wadda ta jiɓinta da harshe. A nan mawaƙi kan nuna gwaninta ta amfani da salailai da dama ya kawo maganar da ba a saba da ji ba amma kuma ta ba da ma’ana. Dubi yadda aka gwama fushi da murna a lokaci guda (duk kuwa da cewa ba a iya kuka da dariya a lokaci guda!):

 Mallam Makama ina fushi

Na kwaɓa murnata da shi

Na sami ‘ya mai murmushi

 (Alƙalio Bello Giɗaɗawa:  Zuwa Ga Kyaftin Makama)

 

A ƙarshe za mu lura da cewa waƙa magana ce mafi tatuwa daga ƙwaƙwalwar ɗan’adam kuma mafi garɗi da laushi daga bakinsa. Abin nufi shi ne, babu wata magana ta ɗan Adam da zai furta da za ta zarce waƙa ta fuskar tsaruwa da lailuwa da laushi da azanci da hikima.

3.0              Wane ne Mawaƙi?

 

Mawaƙi a ƙasar Hausa mutum ne wanda mutane ke yi masa kallo aƙalla ta fuskoki biyu:  ko dai su ce yana da azanci ko mace ne ko kuma su ce yana da fasaha da ilmi. Idan suka ce mace ne to mai kiɗa da waƙa suke nufi a yayin da marubucin waƙa suke yi wa ɗaukar malami, wato mai ilmi mai fasaha.

Wannan kallo da Hausawa kan yi wa mawaƙi ya tuzgo ne sakamakon kasancewarsu musulmi da kuma fahimtar da suke yi wa matsayin sabgar mawaƙi da shi kansa a Musulunci. Ba ƙudurin wannan maƙala ba ne ta nuta cikin wannan magana domin masana a fagen ilmin addini ne ke da wannan gona. Maƙalar kuma tana sane da cewa a Musulunce, gara a cika cikin mutum da ruwan gyambo da a ce ya durmuya cikin sauraren waƙa; sannan kuma akwai hikima cikin waƙa[4]. Hikimar ce maƙasudin wannan maƙala.

 

3.1 Mawaƙi Ne Tun Asali

Mawaƙi mutum ne amma yana da wasu ɗabi’un da ya keɓanta da su waɗanda kuma sakamakon kasancewarsa mawaƙi yake da su. Shi mutum ne wanda Allah ya yi wa baiwar tsara waƙa. Baiwa kuwa a nan tana nufin kyautar Allah Maɗaukaki ga bawansa, ba don wani ƙarfi ko dabara ko sani ko ƙoƙari nasa ba. Ba kuɗi ya sa ya sayo wannan iyawa ba. Ba koyo ya yi ya iya wannan iyawa ba, ba kuma gado ne wanda malami ko alƙali ya raba ba, kai tsaye sai iyawar ta faɗo a kansa. Mai ba da kyauta, Allah Mai iyawa kuma Ma’ishi, shi ne wanda ya yi masa wannan iyawa. Wannan shi ne dalilin da ya sa Haliru Wurno ya ce:

Waƙe fasaha ne da yac cuɗe ka

Kuma ba karatu na ba in an ba ka

Ilmi dubu sai ka biɗo wani nasa

(Alƙali Haliru Wurno:  Ma’anar Waƙa)

 

Abin da Haliru ke nuni da shi a nan shi ne, waƙa dai ba za ka je ka zauna a koya ma tsara ta ba domin fasaha ce, wato wai don mallam ya fahimtar da kai cewa abu kaza da kaza da kaza su ne suka haɗu suka yi waƙa kuma duk wanda ya tashi tsara waƙa sai ya bi su, wannan ba zai sa ka tsara ta ba. Mawaƙi idan yana tsara waƙa bai ma san da cewa yana bin ƙa’idojin ba. Ganin cewa ɗalibin ya tsara waƙa to da ma Allah ya yi shi cikin waɗanda ya yi wa baiwar tsara waƙa. Abin da Mallam ke iya yi kurum shi ne ya zaƙulo wannan baiwa, amma ba ya cusa ta ba[5].

Idan mun fahimta da cewa mawaƙi mutum ne wanda aka yi wa baiwar tsara waƙa sai kuma mu duba mu gani ta yaya ne wannan baiwa ke tasiri a kansa? Waɗanne ɗabi’u ne ke bayyana ga mawaƙi ya kasance mawaƙi?

3.2 Mawaƙi Mulkin Harshe Yake Yi

Mawaƙi yana da wata ɗabi’i wadda ke sanya ya kasance mutum mai mulkin harshen da yake waƙarsa da shi. Shi ba bawan harshe ne kamar mu ba. Mawaƙi mutum ne mai jan harshe kamar mai jan alewa[6]. Mutum ne wanda a wajen sarrafa harshe ya kai har a kan ƙereriyar bangonsa, wato maƙurar harshe. Abin nufi a nan shi ne idan harshe wata duniya ce tamkar daro ko kamar duniyar wata da muke kallo, sannan kuma duniya ce wadda mutum zai iya tattaki har ya kai ga gaɓarta, to duk ƙoƙarin da sauran mutane za su yi na yin tattaki cikin duniyar nan ta harshe, maƙurarsu inda suke walawa ita ce cikin da’irar duniya, ba za su iya kai a kan gaɓa ba. Mawaƙi ne kurum zai iya hawan gaɓar, ya wakita, ya yi tsalle har ma ya iya shatawa da gudu ba tare da ya tuntsure ba! Togensa guda ne tak:  idan ya bugu da giyar ‘yancin sarrafa harshen![7] Wato dai shi mawaƙi ko bayan tarayyar da ya yi da sauran mutane na walawa a tsakiyar duniyar harshe, yana da ƙarfin yin tattakin zuwa bangon duniyar, ya yi yadda yake so. Ga dai taswirar wannan duniyar harshe don ƙarin bayani ga wannan manufar:

DUNIYAR HARSHE

Mawaƙi

Mawaƙi 

JA = Filin rawar mawaƙi SHUƊI = Filin rawar sauran mutane da kuma mawaƙi

Jan fili shi ne wanda mawaƙi yake iya shiga, shi kuwa shuɗin fili shi ne na sauran mutane da kuma shi kansa mawaƙi.

Waƙoƙin da al’umma ke ji kuma ta lamunta da lafazinsu, ba ta ji mawaƙi ya saɓa mata ba ta fuskar harshenta (ta yadda za ta kasa gane ma’ana da sauri) da al’adunta da addininta, su ne ke cikin filin da mutane ke saurin fahimta nan da nan ba da wahala ba. Misali:

 

In za ka faɗi faɗi gaskiya

 Kome taka ja maka ka biya

 

Haka ne editanmu na Gaskiya

Wadda ta fi dubun zinariya

 

Sai mu gode Allah shi ɗaya

Don shi ne Sarkin gaskiya

 

Ya mallaki dukkan talikai

Na kwari da tudu da samaniya

 

Da mutum aljan da mala’ika

Dabbar sarari da ta maliya

 

Mulki iko daula duka

Na ga Sarki Allah shi ɗaya

 

Shi yake ba wanda ya so duka

Ya sarautu a lardin duniya

 

Shi yake karɓe ta ga taliki

Don ya ɗanɗani wahalar duniya

(Sa’adu Zungur:  Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya)

Duk da yake Sa’adu Zungur ya saɓa wa ƙa’idar harshen Hausa ta sanya kalmar ‘da’ tsakankanin jerin sunayen da aka rattaba (kalmomi masu gicciyen rubutu a baiti na 5 da na 6), wannan bai hana mai saurare ya fahimci manufarsa ba. Wata ƙa’ida da Zungur ya karya ita ce sauya kalmar ‘sarauta’, ya kawo lamirin ‘ta’, (bt 7) kurum. A ganin mawaƙin tunda a baya kaɗan ya ambaci aikatau na sarauta, wato ‘sarautu’, ba lalle ne tababa ta shigo kan manufarsa don ya yi amfani da lamirin sunan ba.

Ga kuma wani misali:

Ban da kowa birnin ga baicin ka

Ba ni bin kowa sai da yardakka

Wanda dut yac ce za shi soke ka

Yanzu in ya ga ni sai ya lele ka

 Ya sani fuskata takobi ta

 (A. H. Wurno:  Sarkin Musulmi Abubakar III, Safiya Da Gaskiya Taka Aiki)

 

A wannan baiti mawaƙi ya yi amfani da kalmomi a muhallin da Hausawa ba su amfani da su da kuma inda suke amfani da su, amma shi da abin da yake nufi. A duk wuraren nan biyu Hausawa sun fahimce shi ba da wata matsala ba.

A wuri na farko Haliru ya yi amfani da kalmar ‘lele’ wadda Hausawa ke jinginawa ga nuna tsananin ƙauna da tattali zuwa ga ɗa ko ɗiya daga mahaifi ko mahaifiya. To amma shi Haliru ba wannan yake nufi ba. Manufarsa ita ce ‘mutum ya kwanta wa wanda a da can sukar sa yake yi; mutum ya ayyana tsoro da taushi da girmamawa da ladabi da biyayya ga wanda a da can yake ci wa mutunci’.

A wuri na biyu kuwa Haliru ya ce fuskarsa takobi ce. Haƙiƙa Hausawa sun san da irin wannan fasahar magana. To amma idan suka yi la’akari da abin da Haliru yake gabatar musu, wato waƙa, za su fahimci cewa shi harshensa wanda ke cikin bakinsa wanda yake waƙa da shi, shi yake nufi. Wato harshen Haliru takobi ne ga mai sukar Sarkin Musulmi Abubakar III. Abin nufi shi ne, sukar da Haliru zai yi da harshensa zuwa ga mai sukar Sarkin Musulmi Abubakar III ta fi kaifi da gauni da zafi. Take wannan suka daga Haliru za ta fille kan duk mai sukar Sarkin Musulmi, ta fitar masa da rai, wato ta fille shi ko ta tabbatar wa jama’a cewa wannan mutum ba ya cikin jama’ar Musulmi da Sarkin Musulmi ke shugabanta, hasili ta kafirta shi.

Duk waɗannan misalai suna cikin filin da mawaƙi ya yi tarayya da sauran mutane. Suna iya fahimtar sa kai tsaye ba tare da wata matsala ta harshe ba. Mawaƙi bai tafi can kan iyakar duniyar harshe ba, bai hau kan bangon duniyar harshe ba.

Idan mawaƙi ya kai a kan bangon duniyar harshe ko kuma kusa da shi, to nan kam sai sauran mutane sun yi kamar suna yi kafin su fahimce shi sosai da sosai. Misali:

Kai ka isa1 da isa2rka kai ne mai isa3

Ka isa4d da masu isa5 isa6 in sun isa7

(Mu’azu Haɗeja:  Halayen Mutane)

A wannan baiti mawaƙi ya fito daga da‘irar da ya yi tarayya da sauran mutane, ya koma cikin da’irarsa ta gwanin na gwanaye. Da’irar da yake nuna ikonsa a kan harshe, ya ja kalma ko kalmomi yadda yake so. A baitin nan Mu’azu Haɗeja ya ja kalmar ‘isa’ tamkar yana jan alewa. Ya yi amfani da ita har sau bakwai tattare da ma’anoni mabambanta (salon dibilwa ke nan). Ga yadda watakila manazarci zai fassara kowace kalmar ‘isa’ a jere:

1. isa – yin abin da aka so ba da la’akari da ko akwai abin da

ko wanda zai hana ba.

2. isa – iko.

3. isa – cikakken iko.

4. isa – kai wani zuwa ga wani abu.

5. isa – samun iko.

6. isa – kai wa zuwa ga wani matsayi.

7. isa - ikon da mai cikakken iko ya yarda da shi don ganin

 damarsa.


A taƙaice Mu’azu Haɗeja yana ƙoƙarin bayyana ƙarfin ikon Allah Maɗaukaki, tare kuma da yin addu’a. A maganar yau-da-kullum watakila ga abin da zai ce:

Ya Allah Kai ka yin abin da Kake so babu mai tare Ka saboda

 Kai ne Mai cikakken iko, Ka kai waɗannan da Ka yarje wa

 su kai ga matsayin ɗaukaka (irin ta bayinKa).

Irin wannan zaren tunani ya ginu ne a kan abubuwa guda uku:  na ɗaya shi ne ilmin Tauhidi; na biyu shi ne sanin kalmar da ke iya sarrafuwa; sannan na uku shi ne amfani da salon dibilwa wanda da shi ne mawaƙi ya tsallaka daga filin da ya yi tarayya da sauran mutane zuwa cikin filin da shi ne kurum ke iya zuwa gare shi a duniyar harshe.

Haka shi ma Haliru Wurno ya yi amfani da ilmin Tauhidi da na sarrafa kalma da salon dibilwa don ya tsallaka ya shiga da’irar bangon duniyar harshe. A nan ne ya bayyana siffar Allah Maɗaukaki ta alƘadimu la auwala lahu[8], ya ce:

15. Azal1 yake tun azal2 yake ko azal3 ma

Ga Allah ba azal4 don babu kowa

(A.H. Wurno:  Wa’azi)

 

Kalmar ‘azal’ ita ce Haliru ya yi rawarsa da ita ya ba ta wata ma’ana daban. Manufar Haliru a nan ita ce ya kawar da ƙumshiyar lokaci daga tunanin mai saurare gaba ɗaya don gane siffar nan ta Allah Maɗaukaki, wato al-Ƙadimu la auwala lahu. Yadda za a iya fassara wannan baiti a jumlace da kalmomi biyu ko uku, watakila shi ne:  Allah ne Azal don ya gabaci komi da kowa. Lura da cewa Haliru bai kawo kalmar ‘komi’ ba saboda kalmar ‘kowa’ ta isar mata. Kowa mai rayuwa ne saboda komi, idan kuwa aka kawo ‘kowa’ to lalle ‘komi’ ya wanzu don shi ne ‘kowa’ zai ci ya rayu. A wata fuska ana iya cewa Haliru ya kawo kalmar ‘kowa’ domin waɗanda ke cikin ƙumshiyar (misali, ɗan Adam) sun fi na cikin ‘komi’ ɗaukaka.

Kalmar ‘azal2’ ta cikin ɗangon farko sokakkiya ce wadda ‘azal’ ta uku da ta huɗu da kuma yankin jimlar ‘don babu kowa’ suka soke. A ƙarshe dai kalmar azal ta farko ita ce kurum wanzajjiya.

Mu’azu Haɗeja da Haliru Wurno waɗanda marubuta waƙoƙi ne sun yi amfani da salon dibilwa suka hau kan ƙereriyar bangon duniyar harshe. To su ma mawaƙan baka sukan hau ƙereriyar. Dubi wannan misali:

Fadawa ku bugan in buge ku

Mui ta faɗammu gidan duniya

Kun san ba a faɗa lahira

Ko don ku ka zuwa lahira

Narambaɗa ba ya zuwa lahira

Zama ya san ɗauke mai akai

Ko ya zo dawowa yakai

(Ibrahim Narambaɗa:  Toya Matsafa sadauki na Abdu/Baban Isa baban Buwai/In don na ka gama lafiya)[9]

 

Ba za mu ce Narambaɗa yana inkarin tafiya lahira (mutuwa, a taƙaice) ba. Haka kuma ba za mu ce Narambaɗa ya furta waɗannan ɗiya ba tare da wata ma’ana ba. To amma mece ce ma’anar? Marubucin wannan maƙala yana ganin furucin Narambaɗa bai rasa nasaba da zamanin da mawaƙin ya tsara waƙar. Watakila Narambaɗa bai daɗe da zuwa wani gidan rediyo ba, musamman Gidan Rediyo na Kaduna. A shekarun da Narambaɗa ya rayu rediyo da fayafayen naɗiyar magana na garmaho ba su daɗe da bayyana a ƙasar Hausa ba. Haka kuma Kaduna da wuraren naɗiyar magana wurare ne masu nisa ga Narambaɗa. Wannan sabuwar hikima ta ƙirƙiren zamani mai ban ta’ajibi ce ga Hausawa. To shi kuma Narambaɗa wata hikima da ya hango cikin wannan ƙirƙiren zamani ita ce da zarar aka naɗi muryarsa ko ta duk wani mutum, to za a ji muryarsa har abada ko bayan ya mutu, kamar dai yana a gabanmu da ransa yana rera waƙarsa. A nan ke nan ko Narambaɗa ‘‘ya zo (lahira) dawowa yakai’’!!!

A irin wannan tattaki kan ƙereriyar bangon harshe ne mawaƙi kan tuntsure ya afka cikin amfani da harshe ta hanyar da ta saɓa wa al’adun Hausawa. Misali shi ne waƙar da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa Na Gidan Duwa in da yake faɗin wai wannan gwarzo ya je lahira amma saboda ba a tauri a can sai aka bar shi ya dawo duniya! Yadda Kassu ya bayyana wannan lamari ko kusa bai saɓuwa ga Hausawa domin ya saɓa wa addininsu.

 Ta amfani da wasu salailai kamar dibilwa (wanda muka gani a sama) da luguden sautuka (ƙarangiya) da kuma kacici-kacici, mawaƙi yana iya ƙulla magana mai ma’ana ta amfani da salon ƙarangiya ba tare da wata matsala ba. Dubi yadda Garba Gwandu ya yaba Sarkin Yaƙin Gwandu, Abubakar Koko, cikin kirari da zuga:

Garba sinadari abin haɗa manyan gadaje

Zaki zaburo ka kai zama gun mazaje

Gwarzo garzaya ragargaji gabrin gwaraje

 Alhaji Garba ɗan bani mulki ƙi garaje

(Alhaji Garba Gwandu:  Yabon Sarkin Yaƙin Gwandu Abubakar Koko)

 Sautin /z/ = /j/ shi ne Garba Gwandu ya yi lugudensa da shi a ɗango na biyu, a yayin da a ɗango na uku ya lugudi sautin /z/ = /j/ da na /g/ da kuma na /r/. Mallakar da mawaƙin ya yi ma harshe ce ta ba shi damar harhaɗa kalmomi masu makamantan sautuka har ya tayar da maganganu masu tsari da ma’ana. Lalubo waɗannan kalmomi daga duniyar harshe ba mawuyacin abu ba ne a wurinsa.

Mawaƙi mai iya dagula hankalin mai saurare ko karatu ne ta wasa da ma’anonin kalmomi waɗanda kowa ya san su, amma ya riƙe ɗaya daga cikinsu. Wato ta amfani da salon kacici-kacici sai ya bar kowa cikin zuzzurfan tunani kan ko me yake nufi.

A wani lokaci mawaƙi kan yi amfani da wannan salo na kacici-kacici sannan shi da kansa ya yi bayanin abin da yake nufi. Aƙilu Aliyu ya yi haka inda yake cewa:

1.                  Ƙulun ƙulufit abu dunƙule

 Ƙalau na ƙale ƙalubale

 

2.                  Ka cinci ka-ci miye abin

 Da ke yaɗo kuma dunƙule

 

 

3.     Ya watsu ya barbazu tattare

 Da rassa ga shi a mulmule

 

4.                  Kadan ka ture zuciya

 Da ilmu ake ƙalubale

(Alhaji Aƙilu Aliyu:  Waƙar Ƙalubale)

 

A baiti na ɗaya ne Aƙilu Aliyu ya fara siffanta mana abin da yake son mu gane. Ya ce wani abu ne wanda a cure (dunƙule) yake. A kuma baiti na biyu sai ya ƙara siffa ɗaya don ƙarin bayani, wato shi wannan abu bayan zamansa dunƙule, to kuma yana yin yabanya (yaɗo). Ko kuwa har yanzu ba mu gane ko mene ne ba? Don ya ba mu amsar wannan tambaya sai mawaƙin ya ƙara shigar da mu duhu ya ce wannan abu da yake a dunƙule amma yake yaɗo, shi ne kuma ke watsuwa ya bazu sannan kuma ya yi rassa da yawa amma ya kasance a mulmule. Wannan amsa ita ce baiti na uku yake ɗauke da ita. A baiti na huɗu ne Aƙilu Aliyu ya fito fili ya faɗa mana cewa ai wannan abu dai shi ne ilmi.

Da wannan bayani ne za mu iya gane cewa siffofin nan sun dace da ilmi. Ilmi ne kurum dukiyar da mai ita zai iya ya ɗiba ya ba wani amma kuma ba ta ragu ba. Shi ne kurum zai yi rassa (wato ɗaliban mai ilmi) su bazu cikin duniya amma kuma shi yana nan da haibarsa.

To amma a wani lokaci mawaƙi yakan sa bayaninsa a mala, su kuma manazarta ko masu saurare su yi ta shafar ƙwalluwar kansu don su gano wannan bayani. Dubi wannan waƙa mai baitoci shidda kacal:

 

1.                  Ina da garibi wa ka son in sanas sasa

Biɗah hankali ba za shi sa wa ka sama sa

Bale tafiya ko kai gudu ba ka cimma sa

Ku gai min da sab’in nunu deli ku ce masa

 Akwai ni da tsuntsu ko fa ya san kama tasa

 

2.                  Idan bai sani ba shi zo shi tambayi aƙili

Shi zage zuwa can tambaya inda kamili

Mutum shi yi biɗa da’ ahiri har ga awwali

Idan fa ya gane na sani ya yi hankali

 Ga tsarassa duk ba za ta samun kama tasa

 

3.                  Ana dafuwatai ammanin ba shi yin miya

A ci shi da nau’o’i akan ci shi shi ɗaya

Akan yi kamatai wane kaka tambaya

Misalin jikinai haɗɗalas da suhuliya

 Akwai shi ga daji har gida ana sama sa

 

4.                  Akwai shi ga dutsi mai biɗatai shikan fake

Ga icce shi hau kul ya zamo ba shi yin sake

Akwai shi ga ramu har tudu har cikin haki

Kurun ba jini ga jikinsa ba shi da fiffike

 Kurum babu gashi ko guda ga jiki nasa

 

5.                  Shina da ciki ai babu hanji shina da bai

Akaifa ƙashi har jijiya ba su zam garai

Kurum ba idanu ba wuya gunsa babu kai

Kurum babu nama babu rai kuma dai da rai

 Zama ba shi motsi gun jiki ya isam masa

 

6.                  Asuta da halbi ba shi sawak ka sama sa

Idan kay yi jifa kom matso taka far masa

Idan ka ganai ka zaburammai ka tsar masa

Idan kaf fake wai don shi haike ka kamma sa

 Waɗanga ba sun sa mai biɗatai shi sa masa

(Wazirin Sakkwato Muhammadu Buhari:  Ina Da Garibi)

 

Mene ne ko kuma wane tsuntsun ne Waziri Buhari ke nufi? Marubucin wannan maƙala har yanzu bai samu amsa mai gamsarwa ba, tun kuwa fiye da shekaru goma sha bakwai ne ta shiga hannunsa.

Wasu suna da ra’ayin cewa iska marubucin waƙar ke nufi, wasu kuma suka ce duniya a yayin da wasu suka ce zuciya ce, zuciya mai guri ba zuciya tsoka ba. Waɗannan ra’ayoyi watakila za su karɓu ta yin la’akari da, da kuma sanin zuhudu da sufanci, musamman ganin cewa Waziri Buhari mallami ne kuma malizimcin zuhudu da sufanci.

To amma Sambo Waliyyi Giɗaɗawa yana da ra’ayin cewa abin da Waziri Buhari ke nufi shi ne ƙwai. Ya kafa hujjarsa da cewa watakila shi Waziri Buhari ya samu tasirin wasu littattafan faslsafar Larabci, domin a cikin irinsu ne shi kansa Sambo Waliyyi Giɗaɗawa ya ce ya taɓa cin karo da wani baiti wanda ya yi kama da tunanin da ke cikin wani ɓangare na wannan waƙa. Baitin Larabcin yana cewa:

Wa yu’kalu maɗbukhan lazizaan wa taratan

 Wa yuukalu mashwiyyan idha halla fil lahabi[10]

 

 Ma’ana:  Kuma wani lokaci akan ci shi dafaffe zad daɗi,

Kana akan ci shi soyayye lokacin da mai ya nashe shi

3.3 Mawaƙi Yana Ɗaukar Kalmomi Da Rai

Mawaƙi mai jin kalmomi ne ta amfani da kunnuwansa da zuciyarsa da jikinsa da kuma ɗanɗanonsa. Haka kuma yana ganin kalmomi idan ya kalli abubuwa da abin da suke yi, har ya kawo kalmomin domin su ƙawata ko su munana ko su daɗanta, da dai makamancin haka. Yana iya ya jinjina kalmomi ya gane mai nauyi ko ‘yan lahe-lahe, ya gano masu gauni da kaifi da waɗanda dallasassu ne. Yana iya gane kalmomi masu zurfin ciki, waɗanda ba tasiri guda ko ma’ana guda sukan kawo ga mutum ba. Shi ke jinjina kalmomi ya gano masu laushi da ƙarfi da garɗi da daɗi, kai har ma da masu ɗaci ko bauri. Sannan ta fuskar ƙararsu yana iya gano masu amo da marasa amon. Misali, yayin da Haliru Wurno ya so ya kawo hoton yadda motarsa ta faɗi tare da shi ciki, ga yadda ya ce:

Da tab birkita taw wakita taƙ ƙara zubewa

Da tam mazaya tak karkata tak koma jicewa

Da taw wantsala tam mulmula niƙ ƙara ɗimewa

Da nif firgita nit tsorata kaina ka kaɗawa

Malakul mautu ga sannan nika hange da isowa

 

Ina kwance tana nan bisa taro bisa kanmu

Da manyansu da yaransu da kyar sunka cire mu

Gani na haka can kwance kamar za ta kashe mu

Duhu nata ƙaruffanta kujeri ka jice mu

Da saura na ka sha ma’u dalilinka fitowa

 

Na zabura na jirkita na koma ɗimewa

Ban gane gabas yamma bale dama arewa

Ji kaina ka ta motsi katarata ka kaɗawa

Idona ka hawaye ciki ƙalbi ka bugawa

Ganin na aza guri cike raina ka tunawa

 (Alƙali Haliru Wurno:  Babban Bajini Bello Ƙanena)

A waɗannan baitoci Haliru ya yi amfani da salon amfani da kalmomi masu kaifin ma’ana da masu zurfin ma’ana domin ya ƙirƙiro salon zayyana wanda kuma da shi ne ya cusa mana hoton haɗarin da motarsa ta yi da shi ciki. Haka kuma kasancewar kalmomin nan kusa da juna a tsarin waƙar takan sa mai saurare ya ji irin yadda abubuwa suka auku da sauri kamar da ƙiftawar ijiya, abin da kuma shi ne ke aukuwa a yayin haɗarin mota. Kalmomin ‘birkita’ da ‘wakita’ da ‘zubewa’ da ‘mazaya’ da ‘karkata’ da ‘jicewa’ da ‘wantsala’ da kuma ‘mulmula’ duk su suka bayyana hanzarin wannan mota. Tashin hankalin da Haliru ya shiga ciki ya fito cikin kalmomin ‘ɗimewa’ da ‘firgita’ da ‘tsorata’ da ‘kaɗawa’ da kuma hangen mala’ikin mutuwa kusa, a baiti na 3, da kuma gaba ɗayan na 4 zuwa na 5, waɗanda suka haɗa da taron ‘yan ba da ɗoki suka yi ga Haliru. Rinchaɓin da ya auku ga Haliru da ƙarafan motarsa, salon zayyana ne mai kaifin ma’ana. Shi yana kwance a ƙasa bai iya taɓuka kome, motarsa ita kuwa tana a kansa sannan su kuma masu ƙoƙarin ceto shi suna a kan motar da shi kansa Halirun. Nauyi bisa nauyi!

Wannan ɗabi’a ta mawaƙi ita ta tilasta shi zama mafaraucin kalmomi. Idan ya farauto su to a can cikin ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa zai dinga ƙalailaice su ta hanyoyin da muka ambata ɗazu. Sai dai fa idan waƙa ta zo masa ba kiran su ko tono su zai yi ba. Zuwa suke yi cikin tsarin da ya dace da haliyyar da yake ciki ko ya sa kansa ciki.

3.4.Mawaƙi Maƙerin Maganganun Hikima Ne

Akan ce maganganun hikima na harshe gadon al’umma ne. Suna daga cikin al’adun al’umma. Waɗannan al’adu sun haɗa da tatsuniya (gatana) da kacici-kacici da gagara-gwari da salon magana da karin magana da ishara da dai sauransu. To wai shin wane ne ya ƙirƙiro waɗannan maganganun hikima a Hausa? Cikin rukunonin Hausawa wane rukuni ne ya ƙirƙiro su? Ko kuwa mu ce wane rukuni cikin rukunonin da suka ƙirƙiro maganganun hikima ake ganin shi ne a kan gaba?

Amsoshin waɗannan tambayoyi a mala suke a nan. Sai dai muna iya cewa idan ba mawaƙa ne a kan gaba ba, to kuwa ba za su zamo a baya ba. A nan za a dubi mawaƙa a matsayin rukuni daga rukunonin da ke ƙirƙiro karin magana da ishara.

 3.4.1Maƙerin Karin Magana

Mawaƙi kan yi amfani da karin magana a matsayin salo. Salo kuwa hanyarsa ce ta isar da saƙonsa ga mai karatu ko sauraren waƙarsa. Akwai hanyoyi aƙalla guda huɗu da mawaƙi kan saka karin magana cikin waƙa ko bayan kawo ta kamar yadda Hausawa ke faɗar ta. Waɗannan kuwa su ne faɗaɗa karin magana da gutsure karin magana da kambama karin magana da kuma ƙirƙiro sabuwar karin magana. Yakan bi waɗannan hanyoyi saboda dalilai da dama, kamar ƙarin bayani da yin ishara da fitowa da saƙo a sarari da cika wasu ƙa’idojin waƙa kamar yawan gaɓoɓi.

3.4.1.1Faɗaɗa Karin Magana

Idan za mu yi wa abokinmu nasiha da cewa ya kalli ko ya yi la’akari da haɗarin da ya auku ga wasu mutane a da, muddin dai a maganar yau-da-kullum ce muke yi masa nasihar, to muna iya cewa:  Wane ka dai ji abin da masu fasahar magana suka ce, in ka ga gemun ɗan’uwanka ya kama da wuta to shafa ma naka ruwa, ko kuwa? To amma shi mawaƙi ga yadda ya faɗi wannan karin magana da manufar guda:

122.Sai ku hango gemun ɗan’uwa

 Da ya kama wuta da gaganiya

 

123.Don ku nemi ruwa ku yi yayyafi

 Kada ku ma naku ya sha wuya

(Sa’adu Zungur:  Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya)

 

A nan Sa’adu Zungur ya yi amfani da karin maganar, amma fa ya sake mata kama ta hanyar bayyana mana yadda aka yi gemun ya kama da wuta, wato ‘‘da gaganiya’’. Ma’ana, ko dai shi ɗan’uwan ne ya yi gaganiya, ya kasance da rashin natsuwa, ko kuma gemun ne ya kama da wuta balbalbal, babu ƙauƙautawa. Haka kuma Sa’adu Zungur ya ci gaba da ƙara sake wa karin maganar kama da cewa mu nemo ruwa kamar na hadari masu yawa mu yi yayyafi kan namu gemu. Ya ƙara da cewa idan muka yi haka to namu gemun ba zai halaka ba.

Abin lura a nan shi ne cewa Sa’adu ya warwatsa wannan karin magana a cikin baitoci biyu. Wato sai ka tsittsinto kalmomin sannan ka iya tayar da karin maganar. Wannan kuwa manuniya ce ga cewa mawaƙi kan lallanƙwasa ko daddatsa karin magana. Yana iya lanƙwasa ko ya datsa ko ya gutsure ko ya faɗaɗa karin magana. Dubi yadda wani mawaƙi shi ko ya kawo wannan karin magana:

In ka ga gemun ɗan’uwanka cikin wuta

 Nemo ruwa ka zuba ma naka shaɓe-shaɓe

  (Alƙali Bello Giɗaɗawa:  Hannunka Mai Sanda)

 

Alƙali Bello shi ma a nan amfani ya yi da salon kambamawa, kamar Sa’adu Zungur, domin ya ƙara fitowa da muhimmancin saƙonsa zuwa ga jama’a. Wannan saƙo shi ne kare gemunka daga kamawa da wuta. Ya ce cikin wuta ba ‘ya kama da wuta’ ba kamar yadda karin maganar take a maganar yau-da-kullum. Zuba ruwa za ka yi ba ‘shafa’ su za ka yi ba, kuma don gemun ya yi shaɓe-shaɓe ba ya kasance da ruwa sama-sama ba.

Alƙali Haliru Wurno a wata waƙarsa da ya kira ‘‘ Ko Ba Ka Raƙumi Ka San Cau’’, cewa ya yi:

Ji kai in ka ganai yashe

 Kutumbun ba shi tserewa

 

Jinin kai na gami da wuya

 Da sun rabu ba su komowa

Tumun dare ba ni zaɓen ka

 Tsaya in sake ɗaukowa

Ana iya shafa kan mussa

 Na jibda ba ka farawa

 

Ana iya kama ɗan buku

 Mijirya ba ka damƙowa

 

Fura aka kwankwaɗa amma

 Kunu kam sai da kurɓawa

Mutum in ya biɗo canji

 Abinai an na renawa

(Alƙali Haliru Wurno:  Ko Ba Ka Raƙumi Ka San Cau)

 

Ga wasu ƙarin misalai:

(i)

Giwa du’ abin da tah haifa

Ai an shedi bai zama taffa

Domin ya wuce shiga kwalfa

(Alhaji Garba Gwandu:  Yabon Bajini Ya Zama Tilas, Waƙar Makaman Gwandu Balarabe)

(ii)

Inda Waziri nij ji swan giwa bai ɓacewa

Bai da awan na raƙumi ko a wajen taɓawa

Giwa du’ abin da tah haihwa bai ɗimewa

   Duka daji gidansu birni ab bai shigowa

 (Alhaji Garba Gwandu:  Yabon Sarkin Yaƙin Gwandu Abubakar Koko)

(iii)

Alu namijin zuma mai wuyac cima

Kowah hi ka harbi shi sha kainai

(Alhaji Musa Ɗanƙwairo:  Shirya Kayan Faɗa, Waƙar ‘Yandoton Tcafe Aliyu)

(iv)

Ƙarya ce sukai

Wanda duk ka hwaɗin za ya yi ba ya yin kome

 (Ibrahim Narambaɗa: Amadun Bubakar Gwarzon Yari/ Dodo Na Alƙali)

3.4.1.2 Ƙirƙiro Karin Magana

A zamansa na mai mulkin harshe kuma maƙerin maganganun hikima, mawaƙi lalle yakan ƙera wa jama’arsa karin maganganu. Wato mawaƙi kan faɗaɗa rumbun karin magana a tsawon zamani, ya ƙirƙiro sababbin karin maganganu. Dubi wannan:

Mota idan ta ƙiya kura akai da ita

 In mas’ala ta yi tsauri sai a sake wata

 (Alƙali Bello Giɗaɗawa:  Zuwa ga ‘Yan’uwa Maasu Tunani...)

Tabbas ɗango na farko a wannan baiti sabuwar karin magana ce. Hausawa sun kasance a duniya tun zamanin zamunna. To amma ba su san abin da ake kira ‘mota’ ba sai a ƙarni na ishirin bayan da Turawan mulkin mallaka suka ci ƙasar Hausa. Haka kuma faɗaɗa ma’anonin kalmar ‘kura’ su haɗa da katakon ɗaukar kaya mai tayoyi huɗu, bai auku a harshen Hausa ba sai a cikin ƙarnin. Sabnoda haka, mota idan ta ƙiya kura akai da ita, magana ce wadda ta zo ga Hausawa a wannan baiti cikin ƙirar karin magana kuma sabuwar karin magana a lokacin da aka yi waƙar da wannan baiti yake ciki.

Haka nan kuma a wata waƙa Alƙali Bello Giɗaɗawa ya ce:

Bari son ka rena ƙafarka don motad daɓe

 In ka ga an koro ka nemi wuri laɓe

(Alƙali Bello Giɗaɗawa:  Hannunka Mai Sanda)

 

Bayanin da ya gabata game da karin maganar ‘mota’ ya wadatar ga bari son ka rena ƙafarka don motad daɓe.

Shi ma mawaƙin baka ba ɗan tashi ka rama ne ba:  

Ni Amadu Gwanna Ɗakingari

Haƙon bisa bai kama kumare

 

Jirgin sama ba a sa mai sanke

Ko an sa mai ana ɗebewa

 

Zama kusa maganin mai tcince

 

Manguro karuwa’ icce ta

Ga ta baƙa ɗiya jajjaye


In na tuna goro Gwanja za ni

Na tuna R.K, Ɗakingari

Malam Anaruwa wan Jaɓɓi

 

Muhammadu ɗan su Sarkin Gobir

Ya ka na Saudi ‘yar mallammai

Sanyin ruwa ba shi kama bado

(Amadu Gwamna Ɗakingari:  Yabon Abubakar Ruwa Ɗakingari (R.K.))

Jirgin sama sabon abu ne cikin al’adun Hausawa saboda da farko dai, ba Hausawa ne suka ƙirƙiro shi ba. Hasili kamar yadda mota ta zo masa cikin ƙarni na ishirin, shi ma a lokacin ne ya zo kuma daga baya. Ita ma ɗabi’ar sanya sanke a kan hanyar mota ga dukkan alamu an fara ta ne a ƙasar Hausa saboda yadda ruwan sama ke ɓata hanyar mota[11].

Ke nan a wannan baiti shi ma Amadu Gwamna Ɗakingari ya ƙirƙiro sabuwar karin magana ko kuma aƙalla ya taskace sabuwar karin magana.

Ga wani misali:

Tarago mai jan kaya

Jirgin bisa mai yat tcela’ uway yaya

Kana gaba rigimakka na biya dab baya

Ɗan Sanda

(Abubakar Kassu Zurmi:  Mamman ɗan Sale/Tayin Kura kare ba ya son goyo nai)

Ta yin nazari kan irin rurin da jirgin sama ke yi ne Kassu Zurmi ya lura da abubuwa biyu. Na ɗaya babu wani abu da Bahaushe ya ƙirƙiro kuma babu wata dabba a ƙasar Hausa da ke ruri irin na jirgin sama. Na biyu, Kassu ya lura da cewa sai jirgi ya wuce sannan zai ji wannan ruri. Sai da jirgin sama ya shigo cikin duniyar Hausawa sannan suka lura da waɗannan abubuwa, kuma sanin haka ya ba Kassu Zurmi damar ƙirƙiro wannan karin magana.

3.4.1.3 Gutsure Karin Magana

Mawaƙi kan yi amfani da karin magana ta hanyar gutsure ta. Zai ambaci muhimman kalmomin da karin maganar ta ƙunsa, ya bar saura mai saurare ko karatu ya cike. Waɗannan muhimmam ƙumshiyoyin tunani ko kalmomi kan iya kasancewa ɗaya ko biyu ko uku, gwargwadon yadda karin maganar ba za ta shige duhu ba. Misali, Hausawa kan ce ‘‘Dila sarkin dibara’’ ga mutumin da aka ga wayonsa ya faifaye. To domin mai saurare ya tuna da wannan karin magana ga abin da mawaƙi ya ce:

Na yi gabas wajen yanyawa

 Kila dibaratai ta ishe ni

(Alƙali Haliru Wurno:  Gudale)

A nan sunan dila ne aka kawo da kuma abin da ya shahara ta ita, wato dibara. Lura da cewa ‘yanyawa’ wani suna ne na dila. Mawaƙin ya yi watsi da kalmar ‘sarki’, amma ya ambaci dibara da kuma shi dilan.

4.5 Mallamin Al’umma

Babu ja-in-ja cikin iƙirarin da ke cewa mawaƙi mallamin al’umma ne tun bayan da Musulunci ya zo ƙasar Hausa. Mun ga yadda waƙoƙin Wali Ɗanmasani, da ma wasu kamin shi, suka yi ƙoƙarin bayyana wa Hausawa sira (tarihin Manzo s.a.w.). To balle a ƙarni na 18 da 19 da Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da malamai kamar Shehu Usmanu ɗan Fodiyo da Malam Muhammadu na Birnin Gwari da Malam Shi’itu ɗan Abdurra’ufu[12] da ƙanen Shehu, wato Mallam Abdullahi ɗan Fodiyo da ɗansa Muhammadu Bello da ‘yarsa Asma’u (Nanuwa ‘yar Shehu) da tarin magoya bayansa. Duk waɗannan sun rubuta waƙoƙi domin su ilmantar da al’ummarsu addinin Musulunci da fannonin ilmi waɗanda ke da alaƙa da shi. Waƙoƙi kamar waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ da ta ‘Lalura’ na Shehu da waƙar ‘Tsarin Mulki Irin na Musulunci’ da ta ‘Wa’azu’ na Abdullahi duk misalai ne da ke tabbatar da cewa mawaƙi mallamin al’umma ne. Wannan lamari ya ci gaba har zuwa ƙarni na 20 da wannan na 21 da muke ciki. Ta fuskar marubuta waƙoƙi ke nan.

Zaman mawaƙi mallamin al’ummar Hausawa bai tsaya ga marubuta waƙoƙi ba, kuma bai fara gare su ba. Mawaƙan baka su ma mallaman wannan al’umma ne. Hasili sun riga takwarorinsu marubuta. Abin nufi shi ne waƙar baka ta riga rubutatta samuwa a ƙasar Hausa domin ita ce wadda ta fi rubutattar zama ta gargajiya.

Kafin Musulunci ya bayyana a wannan ƙasa waƙoƙin baka ne kurum Hausawa suke da. To amma wannan tangarɗa ba ta zama dalilin a ce mawaƙi bai kasance ɗaya daga cikin mallaman Hausawa ba. Wannan magana a fili take idan aka tuna da cewa mawaƙi maƙerin maganganun hikima ne ta fuskokin harshe da hanyar rayuwa?

Rashin ingantacciyar hanyar taskace waƙoƙin baka ya kasance babban dalilin da ya hana waƙoƙin Hausa na zamani mai tsawo kawowa gare mu a yau. To amma wannan ba zai raunana has ashen cewa waƙoƙin da muke da su waɗanda aka yi su a wannan zamani, musamman na ƙarni na 20, madubi ne na waƙoƙin ƙarnukan da suka shuɗe ba.

A kan wannan hujja ce muke iya kawo misalan da ke gabatar da mawaƙi a matsayin mallamin al’ummarsa ta ƙasar Hausa. Ibrahim Narambaɗa ya ce a wata waƙarsa:

Ai sarauta ban da nufin Allah ta

Da ɗibat ta akan yi da ƙarfi

 

Waɗanga da nag gaza ganewa

Da sun ga

 

Ana haka nan da sun yi

 

Gogarman Tudu jikan Sanda

Maza su ji tsoron ɗan Mai Hausa

 

Ku dangana tun ga uwaye

Ba duka ɗan sarki ba ka samun sarki

Wane ku dangana tun ga uwaye

Ba duka ɗan sarki ba ka samun sarki

 

Ɗan sarki duka yag ga sarauta

Ga ta kamak kusa tai mashi nisa

In dai bai yi sarautan nan ba

Sai ya kwana da mikin zucci

 

Ɗan sarki duka ab ba kowa

Ɗan sarki duka ab ba komi

Sannan yat tcira yawon ƙarya

Ya san ba ya sarauta

Sai fa shi kwan nan

Gobe shi kwan nan jibi

Dangi nai mashi Allah-waddai

Baƙam magana ba ɓaci ta ba

Amma ta ɗara ɓaci zahi

(Ibrahim Narambaɗa:  Gogarman Tudu jikan Sanda/Maza su ji tsoron ɗan Mai Husa)

Waɗannan ɗiyan waƙa cike suke da ilmantarwa ga ‘ya’yan sarauta na ƙasar Hausa. Haka nan kuma suna ɗauke da karantarwa ga al’umma gaba ɗaya ta fuskar harshe da kuma rayuwa. A wannan ɓangare Narambaɗa ya taskace wa al’ummarsa kalmomin ‘‘Mai Hausa’’, waɗanda ke nufin Sarkin Musulmi. Haka kuma a ɓangaren Gobir da Kabi da Zamfara na ƙasar Hausa idan aka ce ‘Hausa’ abin da ake nufi shi ne Sakkwato saboda ita ce cibiyar ƙasar Hausa kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.

A sashi ɗaya kuma Narambaɗa ya bayyana wa Hausawa cewa su lura cewa a cikin ma’amala baƙar magana duk da yake ba zagi ce ba, amma fa a lokacin da aka yi wa mutum ita zai ji ta da zafi fiye da zagi. A Musulunce mutum yana iya jure zagi ya ƙyale domin ramawa daidai take da zagin kai da kai. To amma baƙar magana fa?

A inda Narambaɗa ya ɓarje guminsa shi ne wurin ‘ya’yan sarauta. Nan ne ya fara da yin tsokaci kan wani mugun halinsu da suke arewa su yafe wai sai sun gaji gidansu. Hakan ko yana faruwa ne ko da ɗan sarki ya san bai cancanta ba. Shi dai tun da ɗan sarki ne kamar ‘yan’uwansa to ya cancanta. Hasili da ya san ana yin sarauta da ƙarfin tuwo da kuwa ya hau gadon sarautar nan! To saboda wannan rashin aiki da hankali na ‘ya’yan sarauta ne Narambaɗa ya yi musu nasiha yana cewa shin wai me ya sa ba su lura da cewa ai ba dukkan iyaye da kakanninsu ne suka yi wannan sarauta ba. Ya kamata su sa idon basira su fahimci cewa fa a kowane lokaci mutum ɗaya ne tak ake naɗawa a matsayin sarki. Saboda haka, inji Narambaɗa, su bar wa Allah zaɓi.

Daga nan kuma sai Narambaɗa ya ilmantar da jama’a game da irin rayuwar ‘ya’yan sarauta ta fuskar tsananin gurin da suke da na zamowa magadan iyayensu. Ya faɗa mana cewa shi fa duk ɗan sarkin da ya ga sarautar gidansu ta faɗi kuma yake ganin shi ne mafi cancanta (kuma mafi yawan ‘ya’yan sarauta haka suke), amma kuma sai Allah ya ƙaddara ba shi aka naɗa ba, to lalle ko shakka babu wannan ɗan sarki zai kasance cikin mummunan baƙin ciki.[13]

Narambaɗa ya ƙara ilmantar da mu cewa duk ɗan sarkin da ya kasance bai da wani girma a idon jama’a, sannan kuma ya yadda girman ta hanyar zama ɗan raraka, to shi kam da shi da zama sarki haihata-haihata. Matsayinsa cikin ‘yan’uwansa shi ne abin takaici, abin Allah wadan naka ya lalace kuma abin yi wa tir!

4.6  Mai Gyaran Al’umma ne

Mawaƙi mutum ne wanda ke amfani da baiwar da Allah ya yi masa ya tsawaci al’ummarsa dangane da taɓarɓarewar halaye da al’adu na gari, kuma ya yi kashedi kan munanan abubuwan da ke ƙoƙarin zama jiki ga al’ummarsa. Haliru Wurno ya yi irin haka a waƙarsa mai suna ‘‘Yaƙi Da Rashin Tarbiyya’’. Gaba ɗayan waƙar a kan ƙoƙarin gyaran al’umma take. Ga kaɗan daga cikinta:

8. Ji takaici ni kam ya isan

Sarkin sata mai son shi zan

Shi riƙe samu gona ta zan

Mulkinai mu ko duk mu zan

 Banzar banza Najeriya

 

 9. Mis sa haka wai ba a lura ba

Amsar rashwa ba a bar shi ba

Yau mallammai su ag gaba

 Su ci hanci had da bugun gaba

 Imani ya fita zucciya

 

10. Wa’azin da sukai na a ba su na

Suka suka yi ga sarakuna

A rufe bakinsu da riguna

Ko tafsirin dodoru na

 Ƙudurinsu su mallaki duniya

 

 11. Shafin kwalli ko karuwa

Ga biɗar mata ‘yan ga-ruwa

Da gida daji ko anguwa

An san haka balle karuwa

Wannan ita ak kan angaya

16.  Wac ce a yi mulki langadam

A ci irlin babba shina sudum

Riƙa garwashi hauninka dum

Tsare girma yanzu ka zam Sadam

 Shi ɗai ka riƙon Najeriya

...

 34. Ikon banza na shi akai

A ci rashwa hanci ci akai

Manyan nan su nay yad da kai

Fadar kowa yau shi akai

 Yi da gaske ɗumi bari dariya

 36. Cewa mulkin ga ka san na kai

Ba mulki na ba da za shi kai

Ga bukata kowa ba shi kai

In babu biyayya sariƙai

 Ka zama manya Najeriya

(Alƙali Haliru Wurno:  Yaƙi Da Rashin Tarbiyyas)

Alhaji Mamman Shata shi kuwa ya soki al’adar Hausawa ta yi wa ‘ya’yansu auren dole. Ya yi kira da cewa su daina wannan domin hanya ce ta lalacewar yara maza da mata. Ga yadda ya yi gyaran:

Amma na tambayi ‘ya’yan birni

Na tambayi ‘ya’yan ƙauye

Kowanne ya bi zancen Shata

Ka ji ‘yan matanku zuwa ga mazanku

Kowanne ya bi zancen Shata

Baba idan za ai man aure

Goggo idan za ai man aure

Inna idan za ai man aure

A bar ni in zaɓi fari kyakkyawa

Kadda a ba ni baƙi mummuna

Auren tilas ba aure ne ba

Shi ke sa wasu yawon banza

Don salla da Salatil Fati

Kai don Allah mata ku yi aure

(Alhaji Mamman Shata:  Mata Ku Yi Aure

5.0 Wani Ɗigon Taddawar Manazarcin Waƙa

Nazarin waƙa fagen ilmi ne mai ban sha’wa da kaifafa tunani da zukata. Yana zurfafa da inganta yadda mutum zai kalli rayuwa. Haka kuma fagen ilmi ne wanda marubucin wannan maƙala ya ɗauka kandami da ba a ganin ƙasansa. Saboda wannan kallo marubucin yake da ra’ayin cewa bai kyautu ba manazarcin waƙa ya tsaya a da’irar taƙalidi. Abu mafi kyawo shi ne manazarci ya gina a kan ayyukan magabata. Wato ya kasance a koyaushe da idonsa a buɗe domin zaƙulo wani abu sabo ko ƙari ga manazarta dangane da nazarin waƙa.

Gamon katar ne marubucin wannan maƙala ya yi na samun karantarwar manyan malamansa guda uku:  Farfesa M.K.M. Galadanci da Farfesa Ɗalhatu Muhammad da kuma Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo. Kowanensu ya shafa wa marubucin kuma ɗalibinsu albarkarsu ta fuskar tono sababbin abubuwa.

Galadanci shi ne ya hasko zumuntar da ke tsakanin karin waƙoƙin Larabci da na Hausa. A kan wannan aiki nasa ne sauran manazarta karin waƙoƙin Hausa suka duƙufa har suka gina a kai.

Shi kuwa Ɗalhatu shi ne wanda jagorancinsa ya haifar wa manazarta da kalmomin fannu na nazarin waƙa da ma Hausa gaba ɗaya.[14] Hasili, duk wani manazarcin Hausa zai lura da wannan baiwa tasa ta tono abubuwan da can ba a lura da su ba a fagen nazarin Hausa, harshe ne!; ko adabin baka ne!; ko kuwa rubutaccen adabi ne!!! Allah ya sahhale ma wannan bawa nasa.

Tsananin kishin Hausa ya sa Ɗangambo ɓullowa da hanyar nazarin waƙa a Hausance kuma a ilmance. Duk wani ɗalibin waƙa bai da ‘lauwalin Nazarin Waƙa’ wanda ya wuce Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa.

Shaƙuwa da hikimomin waɗannan masana ta sa a kai a kai marubucin wannan maƙala yakan ɗan ɗiga taddawa cikin tekunsu. Ga wasu ɓangarorin da ya yi ɗiɗɗigen.

i.Kalmomin Fannu.

ii.Nazarin salo.

iii.Tasirin Maƙalu.

iv.Ƙara son Harshen Hausa.

v.Buɗa wani fiffiken Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya

i.                    Kalmomin Fannu

A wannan ɓangare akwai kalmomin da na Hausa ne, akwai kuma waɗanda asalinsu na Larabci ne. Na Larabcin ba lalle ne ma’anoninsu da aka ba su cikin Hausa su kasance haka nan suke cif da cif a Larabci ba. Ga wasu daga cikinsu:

i.Jinsarwa (abin da Ɗangambo ya kira jinsintarwa):  Ma’ana guda ce da yadda ya bayar cikin Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Salo ne da ya kasa zuwa kashi huɗu, ya ce akwai mutuntarwa da dabbantarwa da abuntarwa da kuma abuntarwar abuntarwa.

ii.                  Na huɗu ɗin nan shi kuma mai maƙala ya sauya sunansazuwa ‘kurwantawa.

iii.               Haliyya:  Abin da Hausawa ke nufi da labarin zuciya. Shi ne wanda waƙa ke sa mai karatu ko sauraren ta ya ji shi cikin farin ciki ko baƙin ciki ko raha ko ƙauna da sauransu.

iv.     Zayyana:  Wannan salo ne cikin waƙa wadda ɗangoginta ko baitocinta ke kawo hoton abin da ake bayani a kai ga zuciyar mai saurare ko karatun waƙa.

v.     Kinaya:  Salon da waƙa ke kiran wani mutum ko wani abu da sunan da ba nasa ba domin mai saurare ko karatu ya kalle shi da siffa ko siffofi ko halayen da aka san wancan da su.Misali, idan aka kira Bello da ‘damishe’, to abin da ake nufi shi ne mai karatu ko saurare ya kalli Bello a matsayin mara sabo kuma wanda bai ɗaukar reni, domin waɗannan su ne halayen da Hausawa suka san damisa da su.

Wasu kuma su ne ‘shillo’ da ‘tsattsafi’ da ‘bin sawu’ da ‘dibilwa’ da sauransu.[15]

ii.Nazarin salo.

Maƙalar da ke da take, ‘Siffantawa Bazar Mawaƙa:  Wani shaƙo cikin nazarin waƙa’ da aka ambata cikin ɗure mai lamba 15, maƙala ce wadda ta yi ƙoƙarin sake duba salon siffantawa. A ciki an faɗaɗa salon ya komo mai raffu kamar haka:

Siffantawa

Siffantawa 

Akwai kuma magana a kan salon tsattsafi da salon bin-sawu cikin maƙalun 2004 da aka buga a 2013.

Tattare da nazarin salo akwai wani zubin waƙa da marubuta waƙoƙin Hausa suka kwaikwayo daga waƙoƙin Larabci. Wannan zubi shi ne wanda yake cikin waƙar da Larabawa suka kira ‘ghazal’. Sambo Junaid (1985) ya bayyana cewa marubuta waƙoƙi a ƙasar Hausa, duk da shike Hausawa ne ko Fulani musamman a ƙarni na sha tara, sun san da ghazal amma cikin harshen Larabci suka rubuta shi.[16] To a wata muƙala ta mai gabatar da wannan laccar ƙaddamarwa an nuna cewa a ƙarni na 20 marubuta waƙoƙin Hausa sun fara rubuta ghazal da harshen Hausa[17].

iii.Tasirin Maƙalu.

Abu ne mawuyaci mutum ya iya tantancewa da iyakar inda tasirin rubuce-rubucensa ya kai domin ba zai iya sanin dukkan waɗanda suka sadu da ayyukansa ko ra’ayoyinsa ba. Wasunsu ko taɓa sanin su bai yi ba.

Duk da wannan tarnaƙi akwai maƙalu biyu da suka kamata a ambata a nan. Waɗannan kuwa su ne, ‘‘Tattalin Zaɓen Rubutattaun Waƙoƙin Hausa Domin Yara’’, wadda aka rubuta a shekarar 1986, da kuma “Dangantakar Waƙa Da Tarbiyyar ‘Ya’yan Hausawa”.[18]

Waɗannan maƙalu, musamman ‘‘Tattalin…’’, sun yi tasiri kan aiwatar da bincike na neman digiri na uku (Ph.D.), wanda kuma ya tabbata sannan ba da daɗewa ba ne wanda ya yi aikin ya zama Farfesa.[19]

A cikin maƙala mai take, “Tsattsafin Raha Cikin Waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno”, akwai ambaton salon bin-sawu.[20]

Bayanin wannan salo ya kasance wa wani manazarci tamkar faɗar Hausawa, ‘Rashin sani ya sa kaza ta kwana da yunwa a kan damen gero’. Manazarcin yana gudanar da binciken neman digirin Ph.D., sai ya ci karo da misalai da dama na wannan salo cikin waƙoƙin da yake nazari, kuma yawan waɗannan misalai ya fi ƙarfin a sa su a mala a wuce a irin binciken da yake gudanarwa. Rannan haka girshi sai ya ambaci waɗannan misalai daidai yadda marubucin wannan maƙala ke ganewa. Nan take ya nuna masa maƙalar ‘‘Tsattsafin raha…’’ wadda a lokacin ake rubuta ta.

Tuni dai wannan malami ya sami digirinsa. Shi ma ya daɗe da zama ‘Ustaz Mushariƙ’, in ji Larabawa. Ba ni shakkun a kira shi Farfesa ko a yanzu da yardar Allah Masani.[21]

iv. Ƙara Son Harshen Hausa

Samun shiga Jami’ar Bayero da ke Kano da na yi a 1978 ya zamo tushen sha’awata ga Harshen Hausa. A cikin Jami’ar ne na haɗu da malamai masu tsananin kishin Hausa waɗanda suka yi iya ƙoƙarinsu don ganin sun cusa wannan kishi ga ɗalibansu a koyawar da suke yi da kuma gayyatar masana irinsu domin su kama musu. Waɗannan malamai sun haɗa da marigayi Farfesa M. K. M. Galadanci da marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya, Allah Ya yi musu gafara, da Farfesa Abdu Yahaya Bici da Farfesa Bello A. Salim da Farfesa Ibrahim Mukoshy da Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo da Dokta Garba Magashi da Malam (yanzu Farfesa) Isma’ila Junaidu da Malam M. B. Umar, Allah Shi gafarta masa, da kuma Malam Wada Hamza. Haka kuma akwai Farfesa Ɗalhatu Muhammad wanda shi ɗan gida ne daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Bai taɓa fashin halartar gayyata daga Jami’ar Bayero ba.

Haƙiƙa waɗannan malamai sun cusa min ƙaunar harshen Hausa ainun. Cikinsu babu wanda bai ƙware ga Harshen Ingilishi ba. To amma fa sun karantar da mu Hausa cikin Hausa, duk kuwa da cewa wasunsu cikin Ingilishi aka karantar da su Hausar, bisa dalilai na rashin Hausawa ƙwararru a lokacin karatunsu, da kuma kishin Ba’ingile na harshensa.

A bisa dalilin karantarwa da tarbiyyar da waɗannan haziƙan malamai suka yi min, ni kuma da Allah Maɗaukakin Sarki Ya kawo ni Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo a matsayin mallami, sai na tarar da ina da jan aiki a gabana. Ba wai mafi yawan malaman Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya a shekarun 1980 zuwa na farko-farkon rabin 1990 da Ingilishi ne suke koyar da fannonin fagen Hausa ba kurum, a’a akwai ma ƙyama da waɗansua ke yi a lokacin na a kira su malaman Sashen. Abin mamaki kuma da yawansu a Jami’ar Bayero ko ta Ahmadu Bello suka yi nasu karatun. To cikin irin wannan yanayi ne, yayin da ake gudanar da wani taro a Sashen na fara jan magana, inda na ce wai tun da fannonin Hausa muke karantarwa me zai hana Sashen ya kafa dokar karantarwa da Harshen Hausa? Nan take sai muhawara ta kable. Wasu su ce ai ƙarancin kalmomin fannu ke hana yin haka nan. Wasu sai su ce harshen da gwamnatin Najeriya ta yarda a yi amfani da shi a matsayin harshen ƙasa shi ne Ingilishi. Wasu su ce ai sai aƙalla an yi taron ƙasa a kan samar da kalmomin fannu sannan za a yarda da ra’ayin da na kawo. Duk wannan na zuwa ne alhali kuwa da yawa suna sane da cewa har taron ƙasa da ƙasa an yi kan kalmomin fannu. A wata shekara, domin in nuna da gaske nake wannan fafutuka, sai na amince da in ɗauki wani kwas na Dabarun Gudanar da Bincike. Na kuma nemi amincewar Sashe da in yi wannan karantarwar cikin Hausa, aka kuma amince. Farfesa Dauda M. Bagari shi ne Shugan Sashe a lokacin kuma da shi da Farfesa Ibrahim Mukoshy sun yi ta ba ni ƙwarin gwiwa. Alhamdu lillahi, a waccan shekarar ce ɗalibai da dama har ma da waɗanda ba su ɗauki kwas na Hausa ko ɗaya ba sun halarci laccocina daga tsangayoyi kamar na Ilmi. Yau kuma a wannan Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya wani daga tsoffin ɗalibaina, Farfesa A. M. Bunza ya wallafa littafi a kan dabarun gudanar da bincike cikin Harshen nan na Hausa mai kwarjini. Farfesa Salisu Ahmad Yakasai ya ci a jinjina masa. Watakila da ba don shekarun da na ba shi ba a duniya da shi zai shige gaba a wannan fafutuka. Tuni Yakasai ya rungumi wannan gwagwarmaya. Aƙalla akwai littafi biyu da mai wannan lacca ya sani waɗanda Yakasai ya wallafa kwanan nan, da a nan gida Najeriya da kuma can ƙasar Sin. Mai laccar yana da yaƙinin cewa akwai wani littafin Imam Abu Hamid Muhammad al- Ghazzali da Yakasai yake ƙoƙarin ya fassara zuwa harshen Hausa. Alhamdu lillahi.

A wasu tarurruka, na ci gaba da wannan taƙala har na kai ga tsokana kamar haka:  Don Allah idan lokacin sauka daga aiki ya yi ga ɗayanmu aka tambaye shi da ya nuna gudunmuwar da ya ba Harshen Hausa, ashe ba abin kumya ne ba idan aka tarar duk muƙalu da littattafan da ya rubuta cikin Ingilishi ya rubuta su ne? Ashe ba Turawa ne ya taimaka ga bunƙasa harshensu ba, da kuma su fahimci Hausa ba? Ashe ba barin gida ne a ba daji ba? Iccen giginya ke nan ko ma indararo!

Sannu a hankali ga shi yau Allah ya kawo mu a rana mai kamar ta yau ana iya gabatar da Laccar Ƙaddamarwar Farfesa na Hausa cikin Harshen Hausa a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta Sakkwato. Da ba don tarnaƙin ‘yan adawa ba da wannan jami’a ta zamo ta ɗaya, ta kasance wadda ta ba Jami’ar Bayero mamaki!!!

v.                  Buɗa wani fiffiken Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya

 

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya sashe ne wanda ko bayan da a gaba zai karɓi cikakken sunansa, a halin yanzu fagage uku ne ake karantarwa cikinsa:  da harshe da adabi da al’ada na Hausa. Wannan Sashe ya yi rawar gani da fiffike guda tun kafa shi har zuwa shekarar 2013. Wannan fiffike shi ne mujallar ƊUNƊAYE. Da shi ne ya yi ta fiffikawa zuwa wurare daban daban cikin uwa duniya har aka san shi. To a ranar Assabar 24 ga watan Maris na shekarar 2013 mai wannan lacca ya yi wa abokansa ƙyas cewa wannan Sashe fa ba lalle fiffike ɗaya ne yake da shi ba, ya kuma nemi goyon bayansu da aƙalla a buɗe wani fiffike daga cikin waɗanda ya hango. Madalla da Dokta B. B. Usman da Dokta Hamza A Ainu (yanzu Farfesa fyas kuma ful) da kuma Dokta Yahaya Idris. Waɗannan gwaraje su ne suka fara ba ni wannan goyon baya. Shugaban Sashe na lokacin, Farfesa Salisu A. Yakasai, wanda tuni ya karɓi buhuhun ilmin waƙa, da kuma Hukumar Jami’a ɗungurumgum sun ba da kyakkyawan goyon baya. A taƙaice dai wannan fiffike da muka baiwa suna, ZAUREN WAƘA, ya samu shiga, duk kuwa da gamuwa da muka yi da gardama da adawa daga ‘yan na-iya. Ƙari ƙaƙaf! Aikin gama ya gama don kuwa mafi yawan malaman Sashe da Hukumar Jami’a sun amince. Alhamdulillahi, a wannan ƙarni mai alamun yana da kama da ƙarnin babban bajini, Farfesa Tijjani Muhammad Bande, ina iya faɗi da babbar murya cewa ZAUREN WAƘA shi ne fiffike na biyu na Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, wanda Allah cikin ikonSa da yardarSa Ya ban basirar ƙirƙirowa ba tare da alfahari ba. Alhamdulillahi.

6.0Gaba Da Gabanta: Kowane Mai Ilmi Akwai Finsa

6.1Malaman Marubucin Maƙala da Suka Cusa Masa Sha’awar Waƙa

*                  Makarantar Furamare

1.                  Malam Muhammadu Kwalkwali

2.                  Malam Abdurrahman Okene

3.                  Mr. Olayinka

 

*                  Makarantar Sakandare

1.                  Malam Idi Ka’oje

2.                  Mr. Richard Alexandra Ross

 

*                  Makarantar Gaba da Sakandare

1.                  Mr. Williams

 

6.2Malaman da Suka Yi Tasiri kan Marubucin Wannan Maƙala ta

 Fuskar Nazarin Waƙa

*                  A Jami’a

1.                  Farfesa M.K.M. Galadanci – Ƙalailaice abubuwa cikin nazarin waƙa.

2.                  Farfesa Ɗalhatu Muhammad – Zaƙulo sabbin abubuwan nazari kan waƙa.

3.                  Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo – Nazarin salon waƙa.

4.                  Farfesa Mervyn Hiskett – Zurfafa bincike kan nazarin waƙa.

 

6.3  Ɗaliban da Suka Fi Tsima Marubucin

1.                  Ɗaliban aji biyu na 1972 a Town Primary School Kware. Sun sa min ƙaimin son koyon hanyar karantarwa.

2.                  Ɗaliban aji 1,3,4 da 5 na 1975, 1976 da 1982 a G.S.S. Anka, sun buɗa min basirar gane cewa baiwar yin waƙa zaƙulo ta ake yi ba koyo ba.

3.                  Ɗaliban waƙa na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na shekarun karatu na 1987/1988 da 1991/1992 da 1992/1993 da 1993/1994 da 1994/1995 sun ƙara sa min ƙaunar ɗalibai da karantarwa.

 Kammalawa

A cikin wannan maƙala an yi ƙoƙarin a biya bukatar wasu masu sha’awar ayyukan mai ita, bukatar da ta tuzgo tamkar faɗuwa ce ta zo daidai da zama. Abin nufi shi ne a yayin da ake mamare a kan mene ne wannan lacca za ta kasance sai su kuma suka ‘umurci’ mallam da ya yi ta a kan bukatar tasu, wadda kuma ta dace ainun da manufofin Laccar Ƙaddamarwa ta wannan jami’a.

An fara da share fage kan gurace-guracen marubucin da kuma musabbabin taken maƙalar. Daga nan kuma sai aka je gidan mawaƙi ko maƙerarsa domin a tantance da shi idan aka gane shi. Wato aka fara duba ma’anar waƙa da muhimman sigoginta, musamman waɗanda aka kira na tarayya. Ba a shiga cikin keɓaɓɓun sigogin kowace ba, wato ta baka da rubutatta. An yi haka ne domin a nuna cewa abu ɗaya ne ake magana don kuwa kome bambace-bamcen da ake samu tsakanin mace da namiji duk dai mutane za a kira su.

Wane ne mawaƙi? Tambayar da ke nan da ta aza harsashin kashi na gaba. A ƙoƙarin amsa ta an kalli mawaƙi ta fuskokin talitta da gwaninta da kuma rawarsa cikin al’umma.

A ƙarshe kamin wannan ɓangare na kammalawa marubucin ya ayyana abin da ya ɗan tarfa a fagen Nazarin Waƙoƙin Hausa. Haka kuma can a ƙarshen ƙarshe an kawo sunayen waɗanda suka yi tasiri a kansa mai maƙalar. Malamansa su ne kan gaba sannan ɗalibansa.

An kawo waɗannan masana ba don kome ba sai don marubucin wannan maƙala a koyaushe ya riƙa tunawa da cewa an yi, kuma har yanzu da gobe akwai na gaba da shi. Yin haka kuwa la’alla Allah Mai jinƙai ya kare shi daga sharrin alfahari da hasada waɗanda su ne manya-manyan munanan masu halaka malami. Allah ya kare mu, amin. Alhamdu lillahi wa Sallallahu ala man la nabiyya ba’adahu.

MANAZARTA

1.      Ainu, H.A., (2006), ‘Rubutattun Waƙoƙin Addu’a na Hausa:  Nazarin Jigoginsu da Salonsu’, kundin digiri na uku (Ph.D)., Sakkwato:  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

2.      Aliyu, A., (2007), Fasaha Aƙiliya, Zariya:  N.N.P.C. ltd.

3.      Bunza, A.M. (2009), Narambaɗa, Lagos:  Ibrash Islamic Publications Centre ltd.

4.      Dunfawa, A.A, (2002) ‘Waƙa a Tunanin Yara’, kundin digiri na uku (Ph.D)., Sakkwato:  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

5.      Department of African and Nigerian Languages, (1978), Harshe I, Zariya:  Ahmadu Bello University.

6.      Ɗangambo, A, (2007) Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa, Kano:  Amana Publishers.

7.      Furniss, G. (1996), Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa, Edinburgh:  Edinburgh University Press.

8.      Galadanci, M.K.M. (1975), “The Poetic Marriage Between Arabic and Hausa”, cikin Harsunan Nijeriya V, Kano:  Bayero University.

9.      Gusau, S.M., (2003), Jagoran Nazarin Waƙa, Kano:  Benchmark Publishers Limited.

10.  Gusau, S.M., (2008), Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa:  Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu, Kano:  Benchmark Publishers Limited.

11.  Gusau, S.M., (2009), Diwanin Waƙoƙin Baka:  Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa, Kano:  Century Research and Publishing Limited.

12.  Haɗeja, Mu’azu, (1980), Waƙoƙin Mu’azu Haɗeja, Zariya:  Northern Nigerian Publishing Co. ltd.

13.  Junaidu, I.S., (2007), Tsarabar Waziri Buhari da Waziri Junaidu ga Manazartan Waƙoƙin Hausa, Sakkwato:  Al-Amin Printing ltd.

14.  Khan, M.M. (b.s.), Sahih al-Bukhari-Arabic-English Translation vol. 8, Ankara:  Turkey.

15.  Magaji, B. (2009), “Nazarin Aron Kalmomi a Waƙoƙin Muhammadu Sambo Wali Giɗaɗawa”, kundin digiri na ɗaya (B.A.), Sakkwato:  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

16.  Muhammad, Ɗ., (1973), ‘‘A vocabulary of Literary terms in Hausa’’, cikin Harsunan Nijeriya na III, Kano:  Jami’ar Bayero.

17.  Muhammad, Ɗ. (1977), “Individual Talent in the Hausa Poetic Tradition:  a study of Aƙilu Aliyu and his Art”, kundin digiri na uku (Ph.D.), London:  Jami’ar London.

18.  Muhammad, Ɗ., (1978), ‘‘Structural tension in poetry:  case notes on enjambment and run-on in Hausa’’, cikin Harsunan Nijeriya na VIII, Kano:  Jami’ar Bayero.

19.  Muhammad, Ɗ., (1984), ‘‘Waƙa Bahaushiya’’, cikin Studies in Hausa Language, Literature and Culture I, Kano:  Bayero University.

20.  Muhammad, Ɗ., (1979), ‘‘Intraction between the oral and the literate traditions of Hausa poetry’’, cikin Harsunan Nijeriya na IX, Kano:  Jami’ar Bayero.

21.  Muhammad, Ɗ., (1980), ‘‘Zumunta Tsakanin Marubutan Waƙoƙin Hausa da Makaɗa’’, cikin Harsunan Nijeriya na X, Kano:  Jami’ar Bayero.

22.  Muhammad, Ɗ., (1982), ‘‘The Tabuka epic in Hausa:  an Exercise in Narratology’’, cikin Studies in Hausa Language, Literature and Culture II, Kano:  Bayero University.

23.  Muhammad, Ɗ., (1990), (editor), Hausa Metalanguage-Ƙamus Na Keɓaɓɓun Kalmomi 1, Ibadan:  University Press ltd.

24.  Sheme, I., Albasu, T.Y., Ƙanƙara, A.I. da Malami, A., (2006), Shata Ikon Allah, Kaduna:  Informart Publishers.

25.  Usman, B.B. (2006), “Hikimar Magabata:  Nazarin Ƙwaƙƙwafi a kan Rayuwar Malam (Dr) Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu (1916 – 2000) da Waƙoƙinsa”, kundin digiri na uku, Sakkwato:  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

26.  Yahya, A.B.(1986)“Tattalin Zaɓen Rubutattun Waƙoƙin Hausa Domin Yara”, in FAIS JOURNAL Of HUMANITIES Vol. 3/ N0.1 (2004), Kano:  Jami’ar Bayero, shafi na 217 – 232. An gabatar da wannan maƙala a 1986 a taron ƙara wa juna sani wanda Hukumar Raya Wallafar Littattafai ta Nijeriya (wato Nigerian Book Development Council, NBDC) ta gudanar a Durbar Hotel a Kaduna daga 5 zuwa 8 ga watan Mayu, 1986.

27.  Yahya, A.B. (1987) ‘The verse category of madahu with special reference to theme, style and the background of Islamic sources and belief’, kundin digiri na uku (Ph.D.), Sokoto:  University of Sokoto.

28.  Yahya, A.B. (1988), “Hikima A Cikin Waƙoƙin Hausa”, Sakkwato:  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

29.  Yahya, A.B (1997), Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna:  Fisbas Media Services.

30.  Yahya, A.B (2001), Salo Asirin Waƙa, Kaduna:  Fisbas Media Services.

31.  Yahya, A.B (2002), ‘Siffantawa Bazar Mawaƙa:  Wani Shaƙo Cikin Nazarin Waƙa’, cikin Studies in Hausa Language, Literature and Culture 5:  220-240, (ed.) Bichi A.Y., Kafin Hausa, A.U. and Yalwa, L.D., Kano:  Jami’ar Bayero.

32.  Yahya, A.B, (2004), “Tsattsafin Raha Cikin Waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno”, maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Sokoto : Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

33.   Yahya, A.B, (2013), ‘Waƙa:  Ma’ana Da Ɗabi’a Da Gimshiƙanta’,in Amfani, A.H. et al (editors) Champion of Hausa Cikin Hausa:  a Festschrift in Honour of Ɗalhatu Muhammad, Zaria:  Ahmadu Bello University Press Ltd, p.230-240.

34.  Yakubu, A.M. (1999), Sa’adu Zungur:  an anthology of the Social and Political Writings of a Nigerian Nationalist, Kaduna:  Nigerian Defence Academy Press.

35.  Wasu daga waƙoƙin Alƙali Haliru Wurno da aka rubuta da rubutun ajami da kuma na boko waɗanda marubucin maƙalar nan ya mallaka. Mai maƙalar ne ya tattara su cikin diwani uku.


[1] Yahya, A.B. (1997), Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna:  FISBAS Media Services, shafi na 4

[2] Duba Ɗalhatu Muhammad cikin ‘Muƙaddima’ wadda ya rubuta kan A.B.Yahya(1997) Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna:  FISBAS Media Services, shafi na v.

[3] Ɗalhatu Muhammad (1997) cikin ‘Muƙaddima’ wadda ya rubuta kan A.B.Yahya(1997) Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna:  FISBAS Media Services, shafi na v.

[4] Don ƙarin bayani sai a dubi Sahih al-Bukhari, juzu’i na 8, fassarar Khan, M.M. (1976)., Ankara:  Turkey, babi na 90, hadisi na166 zuwa 170, babi na 91, hadisi na 171 zuwa na 174 da kuma babi na 92, hadisi na 175,shafi na 106 zuwa 113.

[5] A wani littafi na marubucin wannan maƙala wanda ke kan hanya an bayyana ra’ayi cewa ba a koya wa mutum waƙa sai dai a zaƙulo masa baiwar yin ta.

[6] Cikin Giɗaɗawa, (2006), Bargon Hikima, tacewar Muhammad, Ɗ. da wasu, Sokoto:  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, shafi na 88 da musamman na 172, 

[7] Kamar cewar Mamman Shata,  /A sha ruwa ba lahani ba ne/ /Kun ga Alhaji Shata shi ma sha yake/; ko cewar Kassu Zurmi, /Tauri ya kyauta mai duniya/Tauri ya kyauta mai lahira/Yanzu wani ya ce ƙarya nikai/…./Nakiri ya’ izo yaronai Musa Kirca-Kirca/ ko /Nakiri yaz zaka yat tutture mai ido/ /Ya aza wai shi tsoro nai yakai/.

[8] A dubi Turjamanu ta Shehu Usman Ɗan Fodio (1959), bugun Gaskiya Corporation, Zariya wanda Yahya Nawawi ya fassara, shafi na 6, da sunan Alƙalin Sokoto M. Yahaya; akwai kuma:  ɗan Fodiyo, U., Usul al-Din, mai sharhin Malam Bello Ƙofa (2012), Sokoto:  al-Maktabat al-Malikiyyah, shafi na 12.   

[9] Domin ganin gaba ɗayan matanin wannan waƙa sai a dubi, Gusau, S.M. (2003), Jagoran Nazarin Waƙar Baka, Kano:  Benchmark Publishers ltd, shafi na 75 zuwa na 77; da Bunza, A.M. (2009), Narambaɗa, Lagos:  Ibrash Islamic Publications Centre ltd, shafi na 366 zuwa na 370.

[10] Rashin ganin littafin da ya ƙunshi wannan baiti ya hana wannan marubuci zurfafa nazari dangane da wannan matsayi na Sambo Waliyyi Giɗaɗawa.

[11] A lokacin mulkin mallaka ba kowace hanyar mota ce ke da kwalta ba. Idan aka ga alamun hadari ko aka yi ruwan sama sai mai tsaron hanya (ɗan bita) ya sanya sanke. Duk motar da ta zo tilas ta tsaya nan har sai hanyar wadda aka yi da tsakuwa ta tsane.

[12] Lura da cewa da Shehu da Na Birnin Gwari da Shi’itu duk sun rayu a ƙarni na 18 da na 19, saɓanin yadda za a fahimta a shafi na 45 zuwa na 49 cikin Ibrahim Yaro Yahaya (1988,2001), Hausa a Rubuce:  Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Hasili Shehu Usman ya girmi Muhammadu na Birnin Gwari da shekaru huɗu, ya girmi Shi’itu ɗan Abdurra’ufu da shekaru uku. Yahaya ya faɗa cewa duk waɗannan malamai biyu sun ziyarci Shehu a Sakkwato, kamar kuma yadda ya nuna shekarun da aka haife su,  duk a cikin littafinsa.  

[13] Akwai labarin da ke nuni da cewa a irin wannan hali har imanin ‘ya’yan sarauta yakan taɓu. An ce irin haka ya faru a shekaru da dama da suka shuɗe ga wani ɗan sarki. Ya halarci fada lokacin da Sarkin Musulmi zai yi naɗin sarautar da shi ɗan sarkin ya sa ran shi za a naɗa. To a yayin da Sarkin Musulmi ya yi jawabi ya ambaci wanda aka ba sarauta, ya ƙara da cewa wannan shi ne Allah ya ba, sai aka ji wancan ɗan sarkin da ya sa ran shi za a ba yana cewa, ‘‘Kad dai ba shi’’!!!

[14] Ina magana ne kan ƙoƙarinsa na ganin an yi taruruka don nemo kalmomin fannu tun 1973 har zuwa ga wallafa ƙamus kan kalmomin, mai suna Hausa Metalanguage-Ƙamus Na Keɓaɓɓun Kalmomi, a 1990. Wannan gudunmawa ta ƙara cusa kishin Hausa cikin zuciyar marubucin wannan maƙala, abin da ya sa shi nacewa na lalle sai Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, ya sa ana koyar da, ba waƙoƙin Hausa kurum ba, har ma gaba ɗayan fannonin nazarin Hausa:  harshe da adabi da al’adu. Yanzu haka wannan sashe ya zamo tangam da baƙinsa uku - Larabci da Ingilishi da kuma Faransanci. Watakila hakan ya cire kumyar ban takaici da wasu suke da na a ce Hausa suke nazari ko karantarwa. A madadin su ce Hausa sai ka ji su suna kame-kame wai ‘languages’ ko ‘linguistics’ ko ‘stylistics’ ko ‘cultural studies’ ko ‘literature’ ko ‘poetry’ da makamantan haka.

[15] Domin cikakken bayani sai a duba Yahya, A.B. (2001), Salo Asirin Waƙa da ‘Siffantawa Bazar Mawaƙa:  Wani shaƙo cikin nazarin waƙa’, cikin Studies in Hausa Language, Literature and Culture 5:  220-240, (ed.) (2002) Bichi A.Y., Kafin Hausa, A.U. and Yalwa, L.D., Kano:  Jami’ar Bayero, da kuma (2004) (cikin kuskure editoci suka rubuta kalmar ‘salo’ madadin ‘shaƙo’), “Tsattsafin Raha Cikin Waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno”, maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da (2013), Tsattsafi:  Wani Ɗigo Cikin Gulbin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, maƙalar taron ƙara wa juna sani a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Sakkwato:  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo. Maƙalun biyu kan ‘Tsattsafi’ duk an buga su cikin mujallun ƊUNƊAYE da ZAUREN WAƘA na shekarar 2013

[16] Duba Junaidu, S.W. (1985), “The Sakkwato Legacy of Arabic Scholarship in Verse Between1800-1890” Ph.D. dissertation, London:  University of London, p.62.

[17] Duba Yahya, A. B. “Gudale Waƙar Soyayya:  Misalin Gazal (Ghazal) Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa” cikin Sa’idu Muhammad Gusau da wasu (editoci), GARKUWAN ADABIN HAUSA:  a Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo,

[18] Yahya, A.B   (2001)        “Dangantakar Waƙa Da Tarbiyyar ‘Ya’yan Hausawa” – cikin HARSUNAN NIJERIYA XIX, Centre for The Study of Nigerian Languages, Kano:  Bayero University, shafi na 94-109 da kuma Yahya, A.B.(1986)    “Tattalin Zaɓen Rubutattun Waƙoƙin Hausa Domin Yara”, in FAIS JOURNAL Of HUMANITIES  Vol. 3/ N0.1 (2004), Kano:  Jami’ar Bayero University,, shafi na 217- – 232. An gabatar da wannan maƙala a 1986 a taron ƙara wa juna sani wanda Hukumar Raya Wallafar Littattafai ta Nijeriya (wato Nigerian Book Development Council, NBDC) ta gudanar a Durbar Hotel a Kaduna daga 5 zuwa 8 ga watan Mayu, 1986.

[19] Aikin shi ne, Dunfawa, A.A, (2002) ‘Waƙa a Tunanin Yara’, kundin digiri na uku (Ph.D)., Sakkwato:  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

[20] Yahya, A.B, (2004), “Tsattsafin Raha Cikin Waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno”, maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Sakkwato:  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo. An buga ta cikin ZAUREN WAƘA 1: 1 (2013).

[21] Kundin digirgir/digirin na uku na wannan manazarcin waƙoƙi shi ne, Usman, B.B. (2006), “Hikimar Magabata:  Nazarin Ƙwaƙƙwafi a kan Rayuwar Malam (Dr) Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu (1916 – 2000) da Waƙoƙinsa”, kundin digiri na uku, Sakkwato:  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Post a Comment

0 Comments