𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam a kaset din malam Jafar na ji ya halatta mace ta yi wa mata yan’uwanta limanci toh in ramadan ya zo na kan tara mata na yi musu, dayake duk anguwan na dan fi su karatu, toh kusan anguwan ba malamin Sunnah ko ɗaya sai ‘yan bidi’a, shi ne suke nema na ba su aya ko hadisi a kan hakan mlm ataimakamin don Allah?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To ‘yar’uwa ina rokon Allah ya jikan malam Ja’afar, mu
kuma ya kyautata namu karshen, ya halatta mace ta yiwa ‘yan’uwanta mata
limanci, saboda abin da aka rawaito cewa: Nana A’sha da Ummu Salama –Allah ya
kara musu yarda- sun yiwa wasu mata limanci, Nawawy yana cewa wannan hadisin
Baihaky ya rawaito shi a Sunan din shi, hakan Shafi’i a Musnad dinsa da sanadi
mai kyau, Almajmu’u (4/187).
Haka nan an rawaito cewa Annabi ﷺ ya sanyawa
Ummuwaraka ladani, sannan ya umarce ta da ta yiwa matan gidansu limanci, kamar
yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 491, kuma Albani ya kyautata
shi.
Bisa dalilan da suka gabata za ki iya yiwa matan
unguwarku limanci, tun da kin fi su karatu, Annabi ﷺ yana cewa: “Wanda
ya fi iya karatun alkur’ani shi ne zai yi limanci”. Muslim 1078.
Idan za ki yi musu limanci za ki tsaya ne a tsakiyarsu in
suna da yawa, in kuma ita kaɗai ce sai ta tsaya a damarki.
Allah ne mafi
sani.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/LMfHgWHKrUG9c16dKf9ZBH
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.