𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum warahmatullahi. Malam ina da tambaya?
shin yakamata mace tafita gaban maza tana wa'azantarwa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu
lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa
sahbihi ajma'in.
Asali abin da ya fi dacewa kuma aka fi so, shi ne namiji
ya koyar da maza, mace ta koyar da mata, ta wa'azantar da su, saboda kulle
kofar ɓarna, da za ta iya
saka sashe su ya fitinu da sashe, wanda hakan sai ya haifar da lalata ko
makamancin haka. Idan ba haka ba, mace na iya wa'azi ga namiji kamar yadda
namiji na iya wa'azi, wannan shi ne asali. Allah yace
وَلۡتَكُن مِّنكُمۡ أُمَّةࣱ یَدۡعُونَ إِلَى ٱلۡخَیۡرِ وَیَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَیَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِۚ وَأُو۟لَـٰۤىِٕكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
MA'ANA: Kuma wata jama´a daga cikinku, su kasance suna
kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri, kuma suna hani daga abin da
ake ƙi. Kuma waɗannan, sũ ne mãsu cin nasara.
[Surah Aal-E-Imran 104]
Ayar ba ta iyakance jinsin da mai wa'azi zai kira ko ya
yi ma nasiha ba, kamar yadda bata ambaci maza ba kaɗai a fagen masu
da'awa ba.
Amma idan hakan bai samu ba, toh babu laifi mace ta yi
wa'azi ga maza ko namiji ya yi wa'azi ga mata, kamar yadda muka gabatar, sai
dai da sharaɗin idan hakan ba zai haifar da fitina ba, kuma babu wani
zaɓi sai hakan.
Don haka eh, ya kamata mace ta yi wa'azi ga maza, idan za
ta nisanta daga gare su, za ta nisanci yin amfani da murya mai janyo hankali ko
haifar da sha'awar ta. Allah yace
... فَلَا تَخۡضَعۡنَ بِٱلۡقَوۡلِ فَیَطۡمَعَ ٱلَّذِی فِی قَلۡبِهِۦ مَرَضࣱ وَقُلۡنَ قَوۡلࣰا مَّعۡرُوفࣰا
MA'ANA: ...kada ku sassautar da magana, har wanda ke da
cũta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri.
[Surah Al-Ahzab 32]
Bayan haka sai idan za ta ɓoye adon ta daga
ganin masu sauraro, ma'ana ta lulluɓe jiki da kwalliya ta, kuma za ta sauke ganin ta kamar
yadda Allah ya ce:
وَقُل لِّلۡمُؤۡمِنَـٰتِ یَغۡضُضۡنَ مِنۡ أَبۡصَـٰرِهِنَّ وَیَحۡفَظۡنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا یُبۡدِینَ زِینَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنۡهَاۖ....
MA'ANA: Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga
gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya
bayyana daga gare ta...
[Surah An-Nur 31]
Don haka dai idan har za’a amintu daga dukkan sabubban
fitina da ɓarna ga al'umma, kuma sai idan babu wani Mallami namiji
da yake masani a fannin da za ta yi wa'azin, toh shike nan, ya halatta mace ta
wa'azantar da maza kamar yadda muka gabatar, idan za ta kiyaye ababen da
shari'a ta wajabta a kan ta kuma ta kiyaye mutuncin ta.
WALLAHU TA'AALA A'ALAM.
Amsawa :
Malam Aliyu
Abubakar Masanawa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/LMfHgWHKrUG9c16dKf9ZBH
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.