Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba Dukkan Shaiɗanu Ake Ɗaurewa Ba A Cikin Watan Ramadan

Yabbata cewa ana ɗaure shaiɗanu a lokacin da Ramadan ya shigo, amma ana ɗaure manya-manyan shaiɗanu ne, ana ƙyale kananu.

Hakan ya sa idan mace tana da iska a jikinta koda a lokacin Ramadan ne suna iya tashi, saboda shi wannan Aljanin dake jikinta ƙaramin shaiɗani ne, ba babba ba,baya daga cikin wamda ake ɗaurewa.

Haka kuma idan kana sallah za ka ji ba ka rabuwa da wasi-wasin shaiɗan, to suma waɗannan shaiɗanun da suke zuwa suna sakawa mutum tunani a cikin sallah ba aɗauresu, saboda suma ƙananun shaiɗanu ne.

Su dai waɗannan ƙananun shaiɗanun su ne suke haddasa rigima tsakanin mijin da mata a cikin watan Ramadan harma akai ga mutuwar aure.

Su ne waɗanda suke hana mutune zagewa a kan ayyukan alkhairi a cikin watan Ramadan, su rinƙa sawa mutane kasala, kuma suke jefawa mai Azumi sha'awa harma wani yakai ga karya Azuminsa.

Su ne malaman tsubbu ke amfani da su a cikin watan Ramadan, sai suce ai Ruhanai ne, to ai duk Aljanin da mutum zai kirashi ya zo kuma ya sa Aljanin aiki ya yi koda musulmi ne Aljanin, to baya tsoron ALLAH shaiɗani ne, domin kuwa Aljani mai tsoron ALLAH baya amsa kiran kowa inba na ALLAH ba.

Su ne waɗanda idan da mace ko namiji zai kwanta bacci da rana ko dare a cikin Ramadan, sai ya zo masa da siffar mace ko namiji, taganta ana saduwa da ita, to wannan mai saduwa da mutum a cikin baccinsa shi ma ƙaramin Aljanine.

Su ne wanda inda za ka shiga banɗaki babu addu'a zai iya shiga jikinka ya rinƙa cutar dakai, manyan shaiɗanun Aljanu basa zama a banɗaki sai ƙananu, su kuwa ƙananun shaiɗanun ba aɗauresu cikin Ramadan.

Don haka zamu ga koda a cikin watan Ramadan ana saɓawa ALLAH, sai dai ba kowa ba, saboda su manyan suke umartar ƙananun da tunzura mutane a kan saɓon ALLAH,.

Su manyan su ne suke shan jinin mutum kona dabba, suke sawa ana zubar da jini, ana kashe rayuka, shiysa idan Ramadan ya zo ake samun sauƙin kashe-kashen rayuka, hatta ƴan ta adda sukan saurara sai bayan Ramadan, saboda manyan shaiɗanun dake shan jini an ɗauresu, dama kuma su ne ke tunzurasu su kashe rayuka.

Amma da zarar an ɗauresu, suma ƙananun Aljanun ba su samun ƙwarin gwiwa sosai, sai dai suna zuwa su sawa mai sallah was-wasi damai karatun Alƙur'ani su sashi hamma dssr.

 Don haka kada mu shagaltu da wasa da azhkar na neman tsarin ALLAH daga shaiɗanun Aljanu da mutane ko da a cikin Ramadan ne.

ALLAH ka kare mu daga sharrin shaiɗan babba da ƙarami.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments