Ticker

6/recent/ticker-posts

Tahamisin Wakakken Ka’idojin Rubutun Hausa

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Sadaukarwa

 

Wannan aiki dukansa mun miƙa shi,

Sukutum ɗinsa munka sadaukarwa. 

Mun ba da ga masu aiki na nagarta,

Masu guje wa dukka aikin taɓewa.

Godiya

Bismillahi Rabbana Sarkin jin ƙai,
Tilo ɗai da ke da ikon bayarwa.

Ka ƙara salati wurinsa Rasulillah,
Da iyalansa har Sahabbai ka sakawa.

Ka sa muna masu bin tafarkin sunnarsa,
Har ranar da duniya taka ƙarewa.

Mun gode wa Jalla Sarki, Mabuwayi,
Wanda Ya ba mu wagga damar tsarawa.

Shi yab ba mu juriya mui ta bugawa,
Cikin izininsa mun ka zo gun ƙarewa.

Mun yo godiya ga duk malummanmu,
Tare da jinjina gama duk da yabawa.

Ga wata gaisuwa musamman ga mahaifa,
Don da bazarsu ne rawar muka takawa.

Duk wanda ya taimaka ta kowane fanni ne,
Mun gode ƙwarai ba ma taɓa mancewa.

Za mu yi addu’a Ilahu ya kare ku,
Imani da lafiya ga ku yai ƙarawa.

 

Shimfiɗa

 

Wata rana da yammaci ban mantawa,
Muna ɗan duba littafai na karantawa,

 Sai muka zo ta kan littafin Bunza,
Farfesa Aliyu gwarzon wasawa,

 Shi ne yar rubuta duk baitocin nan,
Waƙaƙƙen ka’idar rubutun Hausawa.

 Shi yaw waƙe ƙa’idoji na rubutu,
Cikin waƙa daki-daki yai tsarawa.

 A shafin ‘X mun ka iske ya yo wani zance,
Can wuce ƙumshiya wurin su gabatarwa.

 Malam ya ce cikinsa zai yi fari in har-
Aka ɗau baitukanga domin ƙarawa.

 A yo tahamisi a ƙara buɗa bayaninsu,
A faɗaɗa ilmi ya iske masu karantawa.

 Wannan shi ne ya zam masomin aikinmu,
Ya ja hankulanmu har muka somawa.

 Mun bibiyi baitukan kakaf don gane su,
Don mu ga ko akwai wurin ɗan ƙarawa.

 Shi ilimi yawa garai babu iyaka,
Don haka mun ka gano fili na daɗawa.

 Fatanmu gudummuwa ga yaɗon harshenmu,
Ya yi tsari a samu sauƙin ganewa.

 Ba mun sauka kan tafarkin tsarin ba,
Mun bi zubinsa ne kawai ba kaucewa.

 Bayanin aikin da yaf faɗi a gabatarwa,
Ga shi a nan ƙasa idan kai dubawa.

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

Post a Comment

0 Comments