Ticker

6/recent/ticker-posts

Jinin Ɓari Baya Hana Azumi

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam ina da tambaya, Don Allah idan mace ta yi ɓarin ciki na wata biyu wannan jinin ya zama na ciwo ko za ta daina azumi da sallah ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

 Wa alaikum assalam To dan'uwa wannan jini ba zai hana sallah da azumi ba, saboda ba jinin haihuwa ba ne, malamai suna cewa : duk cikin da ya zube kafin a busawa yaro rai, to ba zai hana sallah da azumi ba, ana busawa yaro rai idan ya kai watanni huɗu a ciki, kamar yadda hadisin Ibnu Mas'ud, wanda Bukhari da Muslim suka rawaito ya nuna Hakan,.

Saboda haka duk cikin da ya zube kafin haka, to jininsa, ba zai hana sallah ba, ba zai hana azumi ba, amma mutukar an busawa yaro rai ko kuma halittarsa ta fara bayyana, to za’a bar sallah da azumi.

Allah ne mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K1yƘoPioh30H8XeBGg4iPF

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments