𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Idan Mutum Ya Samu Raka'a Daya A Sallar Idi Yaya Zai
Cikasa Dayar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Abun da yake ingantacce daka cikin Magan-ganun Malamai shi
ne Abun da wanda aka tserewa wani Abu A Sallah ya riska, shi ne farkon Sallah a
wajansa.
Abun da zai cikaso shi kaɗai shi ne ƙarshen Sallar sa,
Wannan shi ne mazhabar imamu Shafi'i da ruwaya daka Ahmad
duba Al-Maj-mu'u Na nawawi (4/420).
Dalili a kan Haka
shi ne faɗin Annabi Sallallahu Alaihu wasallam (Idan Kunji iƙamar sallah ku
tafi zuwa sallah, ina horanku da nutsuwa da Kamala, kada ku yi gaggawa, abun da
kuka Samu ku sallata, wanda kuka rasa ku cikaso) Mana'a ku cikaso, ku ƙarasa.
Bukhari (636) da Muslim (602) kamar yanda ya zo a fatah (2/118).
Ma'anarsa shi ne Abun da masbuƙi ya riska tare da liman shi
ne farkon Sallar sa.
Babu Ban-banci tsakanin sallar farillah da Sallar idi, ko
sallar roƙon ruwa ko waninsu, idan ka riski raka'a ɗaya tare da liman a sallar
idi, wannan raka'ar ita ce ta farko a wajanka, bayan Liman ya yi Sallama za ka tashi
ka kawo raka'a ta biyu, zakayi Kabbara a farkonta guda biyar, domin ita ce
raka'a ta biyu awajanka.
Haka A sallar roƙon ruwa.
Idan Kuma Ka riski sujjada a raka'a ta biyu ko ka riski
tahiyar Ƙarshe, za ka tashi kayi
raka'a biyu, ta farko kayi kabar-bari bakwai ko shida, bayan kabbarar harama, a
raka'a ta biyu kuma kayi Kabbara biyar, bayan kabbarar miƙewa.
WALLAHU A'ALAM.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.