Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Fitar Mata Zuwa Sallar Idi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam khamis masoyina 🥰 Da fatan kana lafiya. Na san baka san ni ba amma ina matukar sonka sosai. Muna godiya Allah Ya saka da mafificin alkhayri. tambaya ta ita ce shin mace na iya zuwa sallar idi ko da tana cikin jinin Haila. Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Daga Ummu Adiyya, yardar Allah ta tabbata a gare ta, ta ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya umarce mu da cewa 'yanmata waďanda suka isa aure, da masu haila, da killatattun 'yanmata duk su fita don su halarci idin karamar sallah da babbar sallah. Masu haila su 'kaurace wa masallacin idin; amma dukkansu su halarci alheri da addu'ar musulmi.” Malamai shida suka ruwaito shi.

Al-Shaukani ya ce: Wannan hadisin da wasu hadisan masu irin wannan ma'ana duk sun nuna halascin fitar mata zuwa masallacin idi, ba tare da bambanci ba tsakanin budurwa, da bazawara, da yarinya, da tsohuwa, da mai haila da waninta, ban da mai yin idda, ko kuma wacce akwai fitina a cikin fitarta, ko kuma mai wani uzuri. (Duba 3/306).

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya, Allah Ya ji ƙansa, ya ce a cikin Majmu'ul Fatawa (6/458-459): Annabi (ﷺ) ya gaya wa muminai mata cewa sallarsu a gida ta fi masu falala a kan zuwa sallar juma'a da sallar jam'i, ban da sallar idi. Ita kam ya umarce su da su fita don su halarce ta. Wannan kuwa a zahiri, kuma Allah ne mafi sani, saboda wasu dalilai ne kamar haka:

1. Na farko, wannan sallah sau biyu ce kawai a shekara, don haka sai aka yardar masu, saɓanin sallar juma'a da sallar jam'i.

2. Na biyu, sallar idi ba ta da sallar da take tsayuwa a matsayinta, Saɓanin sallar juma'a da sallar jam'i; domin kuwa idan mace ta yi sallar azahar a ďakinta, wannan ce juma'arta.

3. Na uku, sallar idi fita ake yi wajen gari don ambaton Allah, don haka tana kama da aikin hajji ta wasu fuskokin. Shi ya sa ma idin babbar sallah a lokacin hajji ya zamanto shi ne idin da ya fi kowanne girma ga alhazai.

Don haka mata ku yi ƙoƙari ku halarci Idi, sannan a kiyaye sanya turare ko bayyanar da wani abu na ado, ku lizimci hijabi na Shari'a kuma ku zamto masu natsuwa da kamun kai, sannan a yayin tafiya ku kasance masu bin gefen hanya ba tsakiya ba, kuma ku kiyaye cakuɗuwa da maza, idan kuka kasance haka sai dai a ce daku: MASHAA ALLAH.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments