Hukuncin Wanda Ya Ci Abinci Ko Abin Sha Da Rashin Sanin Cewa Al-Fijir Ya Keto

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamualaikum Inna kwana mallam. Nine zan yi azumi sai na makara na tashi ankira assalatu Amma ba a shiga sallah a anguwanmu ba Kuma ban ji Ana sallah a wani waje ba Sai nace bari nasha ko ruwane Ina sha kawai sai naji an tada kabbara, Shin zan ci gaba da azumin ne ko Babu azumin?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumussalam Warahmatullahi Wabarakatuh,

    Mallamai sun yi saɓani game da wanda yaci wani abu ko ya sha a kan rashin sanin cewa alfijir  ya riga ya fito zuwa maganganu guda biyu:

    1. Kashin farko na mallamai suna ganin wanda ya ci wani abu ko yasha a tsammanin shi alfijir bai fito ba sai daga baya  ya san cewa alfijir ya riga ya fito  to zai cigaba da azumin shi sannan zai rama wannan yinin. wannan shi ne ra'ayin Imamu Abi haneefa da Malik bin Anas da Imamushshafi'i da Imamu Ahmad bin Hanbal.

     

    2. Kashi na biyu na mallamai suna ganin zai cigaba da azumin shi sanna azumin ya yi ba zai rama ba. Wannan shi ne ra'ayin Ishaƙ bin Rahawaihi da  riwaya daga Imamu Ahmad bin Hanbal da Imamul Muzani da  Ibnu Taimiyya da  Dawuduzzahiri da Ibnu Hazmi, dawasu daga cikin magabata, dalilansu fadin Allah (S.W.T):

     ربنا لا تؤاخذنا إن نسينا أو أخطأنا'

    Ya Allah kada Ka kama mu da laifin da mukayi a kan mantuwa ko kuskure, Suratul baƙara, Aya (286).

    Shiyasa sukace wannan shi kuma ya yi ne a kan rashin sani kuma duk wanda ya yi abu a kan rashin sani ba'akamashi da laifi.

    Sannan suka kara kafa hujja da fadin Allah SWT

     'وليس عليكم جناح فيما أخطأتم به ولكن ما تعمدت قلوبكم'

    Babu laifi a kan abin da kuka yi shi a kan kuskure matukan bakuyishi da gangan ba.

    Sai kuma suka kafa hujja da hadisin Asma'u bintu Abibakar wanda ta yi tafiya da Annabi (s.a.w) sai suka yi buɗa baki a kan kuskure sai daga baya suka gane cewa rana bata fadi ba, Imamul Bukhari a cikin littafin shi Aljaami'ussahih hadisi da (1959).

    Amma Abin da Mallamai suka rinjayar ra'ayi na biyu cewa azumin shi ya yi ba zai rama ba.

    والله تعالى أعلم.

    DR NASIR YAHYA ABUBAKAR BIRNIN GWARI

    Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/EYxwmBW9U2o1wckaƙ48MƘ4

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.