Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Yin Gyatsa Yana Karya Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaykum. malam ya ibada ? don Allah malam ka taemaka ka amsamin tambayoyi na ina cikin rudu ; malam shekaran jiya ina aikin abinci sae ita ce da nake amfani da su sae naji daya kamar yana wani kanshi wautar da na yi sae na shinshina ita cen aiko sae hayaki ya shige min cikin hanci don Allah ya ya matsayin azumina yake ? sae kuma bayan na yi sahur sae inta gyatsa wani lokacin har cikin makoshina yaya matsayin azumi na yake ? don Allah ataemaka a amsamin albarkacin wannan watan DAGA DILIBAR KA TA FACEBOOK

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullah.

1. Mace mai girki, hayakin ita ce ko Ƙamshin abinci ko tururin abinci duk basu karya mata azumi. Koda da gangan kika sheƙi abun don neman sanin ko girkinki ya dahu.

2. Gyatsa bata karya azumi sai dai idan sauran abinci ya biyo ta makogoron mutum ko kuma ta hancinsa ta sanadiyyar gyatsar, sannan kuma ya sake hadiyeshi da gangan.

 

Amai (kumallo) shi ma ba ya karya azumi sai dai idan mutum ya janyo yin aman ne da gangan, ko kuma mutum ya sake hadiye sauran aman dake cikin bakinsa, to azuminsa ya karye. Zai rama guda ɗaya.

WALLAHU A'ALAM.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/I3vXUPymspzLawMCwJ44H2

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments