𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam dan Alllah idan miji ya sumbaci matarsa da azumi shin haka zai iya ɓata
azuminsu ko ba zai iya ba. na gode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Zance mafi inganci shi ne ya halatta ga mai azumi ya sumbaci (kissing) ɗin
matarsa, amma da sharadin idan za su iya control ɗin
sha'awarsu ta yadda hakan ba ze sa su yi jima'i ba ko maniyyi ya fita.
An karɓo hadisi daga Aisha (r.a) ta ce:
“Manzon Allah ﷺ ya kasance yana sumbanta alhali yana
azumi, kuma yana runguma alhali yana azumi, amma shi ya fi ku mallakan
sha'awarsa”. Bukhary da Muslim.
Wannan hadisin na nuna mana: Halas ne mutum ya rungumi ko sumbanci (kissing)
ɗin iyalinsa a cikin watan Ramadan
matukar zai iya kare kansa daga jima'i ko fitar da maniyyi.
Runguma da sumbanta ya halatta, amma ba jima'i ba.
Wanda ya sumbanci matarsa kuma maniyyinsa ya fita, to azuminsa ya lalace,
kuma zai kame bakinsa daga ci da sha har sai rana ta fadi, kuma zai rama
azumin, bayan ya nemi gafarar Allah da tuba zuwa gare Shi.
Amma idan madziyyi ne kawai ya fita, to azuminsa bai lalace ba kamar yadda
mafi yawan malamai suka yi bayani.
Don haka, sumbanta na iya karya azumin mutum matukar maniyyinsa ya fita.
WALLAHU A'ALAM.
✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.