Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Tashi Da Safe Na Ga Maniyyi Ajikina Alhalin Ina Azumi.

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalam alaikoom Malam barka da wannan lokacii Allah ya kara ilimi mai amfani, Malam Tambaya nake dashii dan Allah..Yau bayan sallar asuba na kwanta sai na yi mafarki wani ya harbe ni a gaba na saina kama shii da kokawa ina ƙoƙarin na rama, malam bayan na tashii daga bacci sai na fahimci maniyyi ya futo mun.. abun ya sakani a duhu. Dan Allah malam amun bayani miye matsayin azumi na. Na gode Allah ya kara ilimi mai amfani

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

To ɗan'uwa babu abin da ya samu azuminka, abin da za ka yi shi ne kawai ka yi wanka, sannan koda mutum yafarka daga barci kuma yaga alamun ya yi mafarki alhalin bai iya tuna abin da yafaru da shi amafarkin ba, to wannan ma wajibi ne ya yi wanka, amma idan mutum ya san ya yi mafarki kuma ya ji daɗi a cikin mafarkin amma ɗaya tashi bai ga komi a jikinsa ba, to wannan babu wanka akansa domin adalilin mafarki bayyanar baniyyi ne kawai yake wajabta wanka.

Allah ya sa mu dace.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments