𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne Hukuncin Wanda Ya Kalli Matarsa Ba Tare Da Ya Taɓa
Ta Ba, Sai Ya Fitar Da Maniyyi Alhali Yana Azumi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Hakika Wanda ya samu Kansa a irin wannan halin zai cigaba da azuminsa, kuma
babu kome a kansa. dalili a kan haka na cikin hadisin jabir ibn zaid (ra) ya ce:
Wanda ya kalli mace ya fitar da maniyyi, ya cigaba da azuminsa, babu komai a
kansa.
Imam al-shafi'i (babban almajirin imam malik), da imam al-thauri da imam al-auza'i duk sun tafi a kan cewa babu wani dalili da ya zo a kan cewar fitar da maniyyi kaɗai yana karya azumi, ba tare da jima'i ba amma idan jima'i ne, koko an fitar da maniyyi ko ba'a fitar ba, yana karya azumi, kuma sai anyi kaffara. Haka kuma Wanda ya sumbaci matarsa (kiss) har ya fitar da maziyyi shi ma azuminsa yana nan. Wannan shi ne zance mafi rinjaye. Sai dai wasu daga cikin malaman mazhabar malikiyyah sun ce, fitar da maniyyi ta hanyar kallo ko runguma yana karya azumi, kuma akwai ramuwa da kaffara a kai. Amma idan maziyyi ne kawai akwai ramuwa ba tare da kaffara ba. sun kafa hujjar cewa abin da ake buƙata a jima'i shi ne fitar maniyyi. Saboda haka fitar maniyyi ta wannan hanya daidai yake da jima'i.
Amma sauran manyan malamai sunyi masu raddi cewa hukuncin da nassi ya zo da
shi ya ambaci jima'i ne kawai, ba fitar da maniyyi ba. Sannan suka kara da cewa
idan da mutum zai yi jima'i ba tare da ya fitar da maniyyi ba, ai zai rama
azumi ne kuma ya yi kaffara. Haka kuma da ace fitar da maniyyi ne kawai ake
lura da shi, sai ace me bacci ma idan ya yi mafarki ya fitar da maniyyi, sai ya
yi kaffara.
(Sharh sahihul bukhari, na ibn battal al-mālilī, 4 /52-56)
Daga littafin fatawoyin azumin Ramadan na abdulwahab abdullah
WALLAHU A'ALAM
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.