Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Ɗaukar Azumi Ba A Kwana Da Niyya Ba

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu

Malam tambayata ita ce shin idan mutum ya yi azumin farillah ba tare da ya kwana da niyya ba azuminsa ya yi? Kuma shin idan mutum ya yi azumin nafila ba tare da ya kwana da niyya ba kawai ya wayi gari da safe ya ce yana azumi, shin azuminsa ya yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu wa Rahmatullah, dangane da hukuncin ɗaukar azumi ba tare da an kwana da niyya ba, hukuncin ya sha bamban tsakanin azumin Farillah da azumin nafila a wurin jumhur na malamai, wasu malaman kuma suna ganin duk hukuncin ɗaya ne:

1. Ibn Umar ya ruwaito hadisi daga Nana Hafsa cewa: Annabi ya ce: "Wanda duk bai ɗauki niyyar azumi kafin ketowar Alfijir ba, to ba shi da azumi".

Abu Dáwud (2454), Tirmizhiy (730), Ibn Majah (1700).

Kamar yadda aka faɗa cewa wasu malaman suna da fahimtar cewa wannan hadisin yana magana ne kawai a kan azumin farillah ban da na nafila, sai ya zama ke nan duk wanda bai ɗauki niyyar azumin farillah kafin ketowar Alfijir ba, ba shi da azumi.

2. Nana A'isha ta ruwaito hadisi cewa: Wata rana Annabi ya shigo wurinmu sai ya ce: "Shin akwai wani abu a wurinku?" sai muka ce: babu, sai ya ce: "To lallai kam ni mai azumi ne", sai ya sake zuwa wurinmu a wata rana ta dabam sai muka ce masa: Ya Manzon Allah an kawo mana kyautar waina, sai ya ce: "Ku nuna min shi, haƙiƙa na wayi gari ina mai azumi", sai kuma ya ci. Muslim (1154).

Jumhur na malamai sun fahimci cewa wannan hadisin yana nuna Annabi ya wayi gari ba da ninyar azumin nafila ba ne, amma da ya tambayi abinci aka ce babu sai ya ɗauki niyyar azumin nafila, sannan kuma ya nuna halascin mutum ya karya azumin nafila idan ya wayi gari ya sami abinci. Don haka ke nan wancan hadisi na farko ya keɓanci azumin farillah ne kawai, wannan kuma na biyun ya keɓanci azumin nafilah.

 

Sai dai kamar yadda aka faɗi a sama cewa daga cikin malamai akwai masu fahimtar hadisin akasin haka, su kawai suna ganin hadisin ya nuna halascin karya azumin nafila ne idan mutum ya sami abinci, amma ba yana nuna halascin ɗaukar niyyar azumin nafila da rana ba ne. Saboda haka suke da fahimtar cewa duk azumin da mutum zai yi, na farillah ko na nafilah, to dole sai mutum ya kwana da niyya saboda wancan hadisi da Ibn Umar ya ruwaito daga Nana Hafsa ya haɗa duk wani azumi ne, na nafila da na farillah, wato duk wanda bai kwana da niyya ba, ba shi da azumi.

Saboda mutum ya fita daga saɓanin malamai, duk azumin da mutum zai yi ko da na nafila ce ya tabbatar ya kwana da niyyar hakan, idan kuma hakan bai samu ba saboda wata lalura, to ya ɗauki azumin nafilar ko da kuwa bayan wayewar gari ne matuƙar bai riga ya karya ba, tun da akwai dalili a kan hakan, kuma azuminsa ya yi da ikon Allah.

Domin neman ƙarin bayani a duba ALMUHALLÁ (6/198). Da kuma Sahihu Fiƙhus Sunnah (2/88).

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/INxtR9ZhvGNC0bƘVaHCJTF

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments