Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Amfani Da Kayan Kwalliya Cikin Yinin Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne hukuncin amfani da tozali ko wasu kayan kwalliya ga mata, a cikin yinin ramadana, kuma shin yana ɓata azumi, ko a'a?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Tozali baya karya azumin 'ya mace, ko na namiji, a mafi ingancin zance guda biyu na malamai, a kowani irin hali. Sai dai kuma ayi amfani da shi da daddare shi ne ya fi dangane da mai azumi mace ko namiji. Haka kuma abubuwan da mata ke ado da su na sabulu ko mayuka, ko makamancin haka; daga dangin abubuwan da su ke alaƙa da fata kawai, misalin su ƙunshi (lalle), da kayan barbade-barbade (su shafa kumatu), da makamantan hakan, dukkan waɗannan babu laifi ga mai azumi mace, ko namiji su yi amfani da shi, tare da cewa baya halatta a yi amfani da kayan shafe-shafe matuƙar zai cutar da fiska (kamar canza mata kala). Allah shi ne Majibincin dacewa!

An yada shi a cikin littafin DA'AWAH (2/170), da

MAJMU'U FATAWA WA MAƘAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 259-260)

Allah ta'ala ya sa mu dace

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/INxtR9ZhvGNC0bƘVaHCJTF

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments