Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanya Mafi Sauƙi Domin Sanin Hukuncin Jininki

Da yawa daga cikin mata sukan sami rikicewa jinin al'adarsu, wata a dalilin canjin abinci, wata a dalilin canjin yanayi daga sanyi izuwa zafi, wata kuma tana kwana a ɗaki mai AC sai kuma ta sami canjin guri.

Wata kuma a dalilin Allurar planning ko saka roba, wata kuma haka kawai sai ta ga jinin yana ɗigo mata ɗan kaɗan saita sami kokonta akan azuminta ko sallah ko wanin haka.

Wata kuwa zata haihu tacika kwana arba'in ɗinta amma kuma sai ta ga jinin bai ɗauke mata ba, har ta wuce adadin kwanakin da jinin haihuwa yake yi.

Duk wacce ta sami kanta a ɗaya daga cikin irin wannan matsala abinda zatayi shi ne:

Farko idan kika ga jini yazo miki ba'a lokacin da kika saba al'adarki ba, to saiki fara duba kalar jinin da ƙarninsa kiga shin kalarsa da ƙarninsa sunzo iri ɗaya sak da asalin jinin hailarki.

Idan kalarsa da ƙarninsa sunzo iri ɗaya sak, to jinin haila ne, zaki tsaya da yin azumi da sallah harsai sanda ya ɗauke.

Idan kuwa kalarsa da ƙarninsa basuzo iri ɗaya ba, to koma me kika gani, ko brown ko kalar ruwan ƙwai, ko wata kala daban, to wannan yana ɗaukar hukumcin jinin istihadha ne, wato jinin ciwo, shi kuma jinin ciwo baya hana dukkan ibadah.

Sai dai idan yana zuwa mata zuwan da ya wuce misali sai aje aga likita, domin neman magani.

ALLAH shi ne mafi sani.

ALLAH ya karɓi ibadunmu.

Duk mai neman ƙarin bayani ayi mana magana ta private.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments