Ticker

6/recent/ticker-posts

Azumi 29 Za A Yi Bana (Ƙiɗiddigar Adamu Ya'u Ɗan America)

Ga Yadda Tsayuwar Jinjirin Watan SHAWWAL (1444AH) zai kasance cikin ikon Allah. 

Daga

Adamu Ya'u Dan America

Idan ba ku manta ba a cikin posting din da na yi muku a wancan shekara a kan ɗaukar Azumin bana na nuna muku cewa bana Azumi_29 ne za a iya samu, dalilai da yasa na Fadi hakan suna cikin Wannan posting din, saboda haka sai kun daure kun karanta duka, saboda zaku fita daga duhu akan abubuwa da dama, musamman akan shin wani lokacin Watan ne ake gani da gaske? ko kuma ana yadda da wandanda suka ce sunga Watan ne kawai?

Bari mu fara da Kasar Saudiyya Wanda sune Rana zai riga Faduwa kafin Nigeria.

A takaice Kasar_Saudiyya Za su iya Ganin Jinjirin Watan Shawwal da Telescope 🔭 nasu a ranar Alhamis mai zuwa (20/04/2023) idan akwai yanayi mai kyau, saboda bayan Faduwar Rana Hasken Jinjirin Watan Shawwal zai Kasance (0.3%) a Kasar Saudiyya, saboda a (0.1%) ma sun taba bada Sanarwan cewa sun ga Jinjirin Wata da Telescope 🔭 nasu, kun ga kenan indai akwai yanayi mai kyau a (0.3%) za sufi gani da sauki ma.

Mu dawo nan gida Nigeria kuma,

Idan Allah ya kai mu ranar Alhamis mai zuwa (20/04/2023), wanda zai zo daidai da (29 ga Ramadan 1444AH) wato ranar Duban_Fari kenan, Duniyar_Wata zai yi Crossing_Conjunction tsakanin Duniyar Earth da Rana, da misalin karfe 05:12am na Asubahi agogon Nigeria, wanda hakan shi ne Samuwar Sabon Jinjirin Wata, amma a wannan lokaci na Asubahin babu Haske ko kadan a jikin Jinjirin Watan, wato yana (0.0%). 

Kuma a wannan conjunction din za a Samu Kisfewar_Rana a Kasashen dake Gabashin Duniya Kamar Australia, Philippines, Indonesia da sauran su.

Amma bayan an yini zuwa Faduwar Rana Ga Yadda Hasken Jinjirin Watan zai Kasance da kuma tsakanin Faduwar Rana da Jinjirin Watan a Nigeria Kamar Haka;

Anan Jimeta-Yola Nigeria a ranar Alhamis din Rana Zai Fadi da misalin Karfe 6:20pm na yamma, 

Jinjirin Watan kuma zai Fadi karfe 6:45pm na yamma, wato minti 25 tsakani. 

A Jihar Sokoto Rana zai Fadi karfe 6:52pm, Jinjirin Watan kuma zai Fadi karfe 7:19pm na yamma, minti 27 tsakani.

A Jihar Kano Rana zai Fadi karfe 6:38pm, Jinjirin Watan kuma zai Fadi karfe 7:04pm na yamma, minti 26 tsakani.

A Potiskum Rana zai Fadi karfe 6:25 pm, Jinjirin Watan kuma zai Fadi karfe 6:51pm na yamma, minti 26 tsakani 

A Abuja Rana zai Fadi karfe 6:39pm, Jinjirin Watan kuma zai Fadi karfe 7:05pm na yanmma, minti 26 tsakani.

A Lagos Rana zai Fadi karfe 6:54pm, Jinjirin Watan kuma zai Fadi karfe 7:20pm na yamma minti 26 tsakani

A Port Harcourt Rana zai fadi karfe 6:38pm, Jinjirin Watan kuma zai Fadi karfe 7:03pm na yamma, minti 25 tsakani.

A Bayelsa-Yenagoa Rana zai Fadi karfe 6:41pm, Jinjirin Watan kuma zai Fadi karfe 7:06pm na yamma, minti 25 tsakani.

A Kaduna Rana zai fadi karfe 6:41pm, Jinjirin Watan kuma zai Fadi karfe 7:07pm na yamma, minti 26 tsakani,

Da sauran su.

Daga lokacin da Watan yayi Conjunction zuwa faduwar rana a Nigeria Musamman a Jihar da rana Zai Fadi a karshe wato Lagos, Watan zai samu Awa 13 da mintuna 42 daga yin conjunction, a lokacin kuma Hasken da zai bayyana ajikin Watan zai kasance (0.4%) kun ga Hasken Jinjirin Watan zai karu da digo 1 akan na Saudiyya, Sannan bayan Faduwar Rana watan zai yi mintuna daga 25, 26, zuwa 27 ne kafin ya fadi a bisa yanayin faduwar rana a Mabanbantar Jihohin Nigeria, hakan na nuna cewa idon Dan_Adam ba zai iya Ganin_Jinjirin_Watan a ranar Alhamis ba, a duk fadin Nigeria, ko da akwai yanayi mai kyau, sai dai da da na'urar Telescope 🔭, amma duk da haka za a Samu wasu da za suyi ikirarin cewa sun ga Jinjirin Watan a Garuruwa Daban-Daban, Saboda indai a Nigeria ne, ko ranar 20 ga Watan Ramadan ne aka ce a fita Duban Jinjirin Watan Shawwal sai an samu Wanda za su ce sunga Jinjirin Watan, ballentana kuma ace akwai Jinjirin Watan kawai yayi Matukar Kankanta ne kawai yadda ido ba zai iya gani ba sai dai da Telescope 🔭.

Saboda Awannin da Watan yayi da kuma Hasken da yake jikin Watan bai kai yadda idon Dan Adam zai iya gani ba, ko akwai yanayi mai kyau, Saboda sai an samu akalla Awa 15 da mintuna 42 zuwa Awa 18 bayan Conjunction din, kafin Jinjirin Wata ya samu Hasken da zai kai daga (0.6%) zuwa sama da hakan, a (0.6%)din ma sai Nisan Watan da Duniya yana kusa sannan idan an hada da na'urar wanda zai nuna location din da watan yake kafin sannan idon Dan Adam zai iya ganin Jinjirin Wata a (0.6%) din. 

Sannan sai an samu akalla mintuna 35 zuwa 40 tsakanin Faduwar rana da Faduwar Wata Kafin idon Dan Adam zai iya Ganin Jinjirin Wata.

Amma a Washe gari ranar Jumma'a (21/04/2023) bayan Faduwar Rana idan akwai Yanayi mai kyau Ma'ana idan babu Hadari ko Gajimare ko Hazo_Hazo za'a iya ganin Jinjirin Watan da idon Dan Adam cikin sauki, Saboda a Wannan lokacin Jinjirin Watan zai samu Awa 34 da mintuna 14 anan Jimeta-Yola, a wasu jihohin zai kai Awa 37 da mintuna zuwa 8 har zuwa 52, daga yin Conjunction. 

Hasken da zai bayyana a jikin Watan zai kasance daga (3.0%) zuwa (3.2%).

Sannan a wannan rana na Jumma'a bayan faduwar Rana Watan zai kai Awa 1 da mintuna 20 Kafin ya Fadi.

A ranar duban fari din idan Majalisar Koli ta Addinin_Musulunci Karkashin Jagorancin mai Alfarma_Sarkin_Musulmi ta Amince da Ganin Jinjirin Watan a Maraichen ranar Alhamis (20/04/2023) hakan zai sa washegari ranar Jumma'a (21/04/2023) zai Kasance 1 ga Shawwal a Nigeria, kuma mafi yawanci a irin Wannan yanayin Majalisar mai Alfarma sarkin Musulmi tana Amincewa da Ganin Jinjirin Watan musamman ma idan Saudiyya sun sanar da nasu ganin Jinjirin Watan, saboda akwai Jinjirin Watan a sama bayan Faduwar Rana a wannan rana na Alhamis.

Sannan yanayi na Wannan Shekara ya banbanta da na shekaru uku da suka gabata wanda aka cika Azumi 30, Saboda a wanchan lokutan babu Jinjirin Wata a sama Bayan Faduwar rana a ranar Duban Fari, shi yasa a wanchan lokutan ko mutun Dubu ne suka ce sun ga Jinjirin Watan ba za'a Amince ba. 

Saboda Wadannan dalilai ne yasa nace bana Azumi 29 za mu samu.

Ga Hotunan Yadda Tsayuwar Jinjirin Watan zai kasance bayan Faduwar Rana.

Hoto na farko a ranar Alhamis kenan (20/04/2023) Yadda Jinjirin Watan Hasken sa yana (0.4%) a Nigeria yayi matukar kankanta, nayi misali da Faduwar rana a anan Jimeta-Yola, da sauran dalilan dana bayyana muku a baya, shi yasa idon Dan Adam ba zai iya gani ba, amma duk da haka za a samu Wanda za suce sun gani, kuma za a amince da ganin su din.

Hoto na biyu a ranar Jumma'a kenan (21/05/2023) Yadda Hasken Watan yana (3.0%) Yadda za a iya gani cikin sauki, amma idan akwai yanayi mai kyau a inda ka ke, kuma za a ganshi da Girma.

Da fatan Allah ya sa mu dace. 

Post a Comment

0 Comments