Ticker

6/recent/ticker-posts

Da Wanne Lokaci Ake Fitar Da Zakkar Fidda-kai?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Da Wanne Lokaci Ake Fitar Da Zakkar Fidda-kai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Abun da yake wajibi shi ne fitar da zakkar fidda-kai kafin fita zuwa sallar idi, saboda hadisin Abdullahi dan Abbas yardar Allah takara tabbata agareshi yace: (Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya wajabta zakkar fidda-kai dan tsarkake mutane daga kazantar zancen banza da sukayi da kuma na sha'awa lokacin azuminsu da kuma ciyar da miskinai, wanda ya bayar da ita kafin sallar idi lallai zakkace karbabbiya, wanda ya bayar da ita bayan sallar idi to sadakace daka cikin sadakoki) Abu dauda(1609) da Ibnu majah (1827) Albani ya ingantashi acikin sahihu Abu dauda.

Wannan hadisi ya nuna da zarar limamin dake yiwa mutane sallah ya idar da sallah lokacinta yafita.

Saidai idan wajen daba'a sallar idi kamar kauyuka misali, to zasuyi amfani da lokacin fitarwar mutanen garin dake kusa dasu.

Albuhti ya ce: Abun da yafi shi ne fitar da ita kafin fita zuwa sallar idi, ko kuma ƙaƙƙara lokacin dayake kafin fita sallah aguraren daba'a sallar idi, Domin Annabi sallallahu Alaihi wasallam yayi umarni afitar da ita kafin mutane su fita zuwa sallar idi, acikin hadisin ibnu umar.

Malamai sukace: Abun da yafi shi ne fitar da ita yayin da mutum zai fita zuwa sallah, Kashshaful Ƙina'i (2/252).

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments