Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ba Ya Samun Sallar Asubahi Saboda Ƙiyamul Layli

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah. Mallam miye hukunci mutumin da yake Ƙiyamul layli, sai barci yake hanashi samun sallar asubahi.? Allah ya saka ma da gidan aljannah, ya gafartawa mahaifanka, ya sadamu da shugabanmu Annabi Muhammad(saww) daga Aminu Auwal Dambam.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Gaskiya wannan ya munana ma kansa, Kuma ya cuci kansa. A garin aikin Mustahabbi ya tozartar da ayyukan farilla.

Yin sallar Asubahi acikin jam'i kuma akan lokacinta wajibi ne. To amma shi Ƙiyamul Layli (Tahajjud) Sunnah ce ta Mustahabbi. Kuma yinta agida yafi lada fiye da yinta a masallaci. Sannan yinta kai Kaɗai yafi lada fiye da yinta cikin jam'i.

Don haka ya kamata samari su kula. Babu abinda Ubangiji yafi Ƙauna daga gareka fiye da ya ga ka bauta masa kamar yadda ya umurceka kuma ka fara bama farilla hakkinta kafin nafilfili.

Kuma Manzon Allah (saww) ya kwadaitar da al'ummah sosai game da halartar sallah cikin jam'i. Musammab asubah da kuma isha'i.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments