Ticker

6/recent/ticker-posts

Burkitantan Na Burkitato

Burkitantan na burkitato!

Nai lakwab-kwab nai sakato

Na yi jangwam nai lakwato

Yau na yi tsinkin ragi, kaito!

‘Yar ɗiya na zo na rawaito

Tuni ta laɓaɓo tai kwanto

Iwa hawainiya ta marabto

Ta shige ta zuciya ta ƙarato

Tai kane-kane ga kokwanto

Mamakin dirinta na hankalto

Kyawunta ya wuce na hakaito

Mai kyan diri har da daidaito

Ko ba kamar ta, nace Eh to

In har akwai to ta zo ta fito

Ba tsatsuba ko ƙulumboto

Kin fanshi zuciya kin ceto

Mun daddale mun yi sasanto

Ruhi da kece ya cancanto

Ɗan muzguɗo gareni kusato

Fakuwarki na saka na ɓakalto

Na dabalbale har na ragaito

Maƙiyanmu sun bar kwaroroto

Sun sangarce da bulunbito

Caɓ! Duk ƙalata ta wani ƙato

Mai ɗaure ƙugu da ɗan gyauto

Sam ban bari har ya min rinto

Sai na faɗa yau na maimaito

Sungumi ko ba ya jure kufurto

Mai min habaicin ya habaito

Ko in kula ko na waiwaito

Sai ku dangane ku haƙurto

Ingare ga Allah nace da'uto

 10 ga Maris, 2023.

USMAN IBRAHIM BULANGU

09064862386

Post a Comment

0 Comments