(01) Na gode Allah Sarki mai zamani,
Alƙahharu gwani na mai mulki
(02) A yau Samari ku lura da
kyan gani,
Don ku gane da birgimar-hankaki
(03) ‘Yan mata masu siffa ta
Hawainiya,
Yau su suke sauya launi na jiki
(04) Sai ta shafo mai tana
kwarkwasa kuma,
Tana ta tafiya kamar ma Gwanki
(05) Kai duk ta jeme fuska ta koɗe sarai,
Kash! me zai saka ki sauya
sifarki?
(06) Kin jeme kuiɓi gami da kaya-kayai,
Har magyaftanki har da haɓarki
(07) Ƙwabrinki ba maraba da
na Jimina,
Duk kin yi mai rini shin wa zai
so ki?
(08) Kin gawurta ke ba ki ji ba
kya gani,
Ke cimakar ki a kullum mugun
aiki
(09) Bursinsina mai shafe-shafen
mayika,
Wai burin ki dai ki ɓadda kamar ki
(10) Domin ki samu Miji ki yi auruwa,
Kin manta Tabara shi ne zai baki
(11) Ke dai kawai ki yi fari ya
Baturiya,
Kin mance baiwa Zuljalali yai
miki
(12) Kasantuwar ki baƙa ba aibu bane,
Tunda dai haka Allah ya aje ki
(13) To ma nace wai hasken me
kike biɗa?
Bayan Musulma Jallah ya iyo ki
(14) Sai ki fake da juyin fuskar
zamani,
Ki shantake babu ragin ɗan ɗaki
(15) Ukubirtini ma gurratki ha
kaza,
Ya ayyatuhan nafsu ma baluki?
(16) Iz kanatid duniya sijnun
lana,
Wa kaifa jahadti an tabki?
(17) Ma tara fi kalƙir Rahmanu min tafa,
Wutin, ga tambayar Mahaliccin
ki?
(18) Farji'il basari hal tara
min fuɗur,
Sai ki duba ki ganta bata da
miki?
(19) Kin ji ko a kan sama Allah
yai gwaji,
Na irin misalin nan na sifarki
(20) Ya kamata ki yi yo
karatun-ta-nutsu,
Don ki samu tsira nan ga tafarki
(21) Alhamdu lillahi ni zan
gimtse a nan,
Usman Bulangu na maida Ƙoƙo Masaki
USMAN IBRAHIM BULANGU
09064862386
Masha Allah, Allah ya saka da alheri.
ReplyDelete