Ticker

6/recent/ticker-posts

Sanadin Fara Waƙena

USMAN IBRAHIM BULANGU

09064862386 

 BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM

01. Da sannu-sannu na zo na fara dai ku ji,
Na dake na dage babu mai mini agaji,
Shi sha'iranci ba a yi masa kwaf-ɗaya 

02. Ni na kasance mai yawan yin bincike,
Ilimi nake nema kamar me dunduke,
Don kad da dai kaina ya zam na Ƙififiya 

03. Ni Shehina Malam Ƙani shi ne ya san,
Kishi na harshe na ya ce kai dai ka san,
Harshenka ya wuce yadda-shi-ɗauko-haya

04. Nukuɗa da dama sai ya feffeɗe mini,
Asali na kalmomi tsatsaf ya gaya mini,
Har ma da tarihin Bahaushe ɗan jiya

05. Ƙa'ida ta waƙa duk ya suranta mini,
Taza-da-tsifa duk a kanta ya yi mini,
Waƙa ta Hausa har da ma ta Arabiya

06. Na ɗauki niyyar yi da gaske a hankali,
Jifa da Kansakali na sa yo Kwalkwali,
Ɗamara ta waƙa nas saka ƙololiya

07. Dukufa na yi nazari nake na tsabbace,
Wallafar mazan jiya bi-da-bi na taskace,
Domin na dace kar na yo kandarariya

08. Abokanai ko waɗansu in suka ganni sai,
Su ɓuge da kyarata kamar Ƙwaron masai,
Wai ga Mawaƙi wassu nai mini zolaya

09. Daga na yi honƙoron na ma wai kare kai,
Sai su barni wofi kai su ma dai kauda kai,
Sun ga mai sana'a o'e wofantacciya

10. Da kaɗan idan na yo suke yin marmari,
Haka nan ta zaga kan tudu har ma kwari,
Na fitar da Diwanin Madubin Duniya

11. In na yi sai in kaiwa malumma su ji,
Har ma Furofesa na kai masa dan gwaji,
Don dai su sa ni a godaben bin gaskiya

12. Na Gusau Furofesa ya ce waƙar da kai,
Tsaf ta yi daɗi ba ko wai dan dai da kai,
Yi faɗi na sunana, kawai dan gaskiya

13. Dakta Gabari ya ce kaje maza kai ta yi,
  Domin ko jari ce watan-wata-rana yi,
Kar kai sake kan mauhibar ka ka jiya

14. Af! na yi waƙoƙi akwai Masa'uliyya,
Nai ta Manzo na yi har da Matashiya,
Ga nan ta Alƙalami da Ƙalwaiwainiya

15. Da diri na ɗango har da ma dai yan ɗiya,
Da ado na harshe har da ma dai ƙafiya,
Na kanannaɗe su a wallafa ta Ƙarangiya

16. Sau sassaƙar saƙar ka sauƙe sassaƙe,
Saƙon saƙaƙa saƙe-saƙe su sarƙaƙe,
Sarƙarsa sunƙuru siƙe surƙuƙƙiya

17. Gorin ki Kaska gun su Babe kan jini,
Ina ko ke ki ka samu naki gaya mini,
Kin huda kanki garin ki feɗe wutsiya

18. Kura ko wane za ya baki riƙon gari?
Su Kare ki ja su ki kai ki sa su a haɗari,
Tumuna a ce an bawa Kura tsangaya

19. Na yo Salatai gun Rasulu abin biya,
Har Alihi na gidansa dukka a gauraya,
As'habu tare da su akai ta ɗawainiya

20. Hamdan kasiran ɗayyiban ya Rabbana,
A gare Ka ni Usman Bulangu ga ko ana,
Tutur! a kowasshe inai ma Ka godiya.

Post a Comment

0 Comments