Bayani A Kan Sallar Dare (Qiyamul Laili)
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum warahmatullahi wabakaratuhu, ina fatan kowa yayini lafiya, malam Allah ya ƙara basira, dan Allah ina son karin bayani a kan sallar dare (ƙiyamullaili). na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salámu, 'yar uwa Ƙiyamul
Laili shi ne Bahaushe ke ce masa sallar dare, wato ƙiyamul
laili ibada ce da ta ƙunshi sallolin nafila da karatun Alƙur'ani da kuma sauran zikirori daga bayan sallar Isha'i
har zuwa ketowar Alfijir. a kan kira shi da 'Attahajjud' idan ya kasance sai
bayan an yi barci an farka sannan aka yi sallar.
Yin sallar dare (ƙiyamul laili) yana da falala mai yawa
da Allah Ta'ala ya keɓance shi da su kamar yadda ayoyin Alƙur'ani da
ingantattun hadisan Manzon Allah ﷺ suka tabbatar. Daga ciki akwai aya ta ɗaya zuwa ta huɗu da ke cikin
suratul Muzzammil.
Ƙiyamul
Laili ba shi da adadin raka'o'i ƙididdigaggu da dole a kansu ake
tsayawa, idan da mutum zai yi raka'o'i hamsin ko fiye da haka, sannan ya
kammala su da wutiri, to babu laifi, Ibnul Ƙaɗɗan Alfaasiy ya
hakaito cewa:
" Malamai sun yi ijma'i a kan cewa babu iyaka a
sallar dare, lallai ita nafila ce, duk wanda yaso ya yi sallar yadda yaso, ya
yi da yawa ko ya yi kaɗan".
Duba Al'iƙná'u Fiy Masá'ilil Ijmá'i (1/174).
Sai dai abin da ya fi shi ne mutum ya yi wutiri da adadin
da Manzon Allah ﷺ ya yi, wato raka'a goma sha ɗaya, ko goma sha
uku, yana yin sallama a kowace raka'a biyu, sai kuma ya yi wutiri da raka'a ɗaya, kamar yadda
hadisi mai lamba ta 749 ya bayyana hakan a cikin Sahihu Muslim. Wannan adadi
shi ne mafifici.
Kuma mafificin lokacin wutiri shi ne ɗaya bisa uku na ƙarshen dare, amma idan mutum ya yi wutirin a farkon dare,
ko a tsakiyarsa to babu laifi.
Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.
Jamilu Ibrahim, Zaria.
***
BAYANI A KAN SALLAR DARE (QIYAMUL
LAILI):
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum warahmatullahi wabakaratuhu, ina fatan kowa yayini lafiya, malam Allah
ya qara basira, dan Allah ina son karin bayani a kan sallar dare (qiyamullaili).
nagode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salámu, 'yar uwa Qiyamul Laili shi ne Bahaushe ke ce masa sallar dare, wato
qiyamul laili ibada ce da ta qunshi sallolin nafila da karatun Alqur'ani da
kuma sauran zikirori daga bayan sallar Isha'i har zuwa ketowar Alfijir. Akan
kira shi da 'Attahajjud' idan ya kasance sai bayan an yi barci an farka sannan
aka yi sallar.
Yin sallar
dare (qiyamul laili) yana da falala mai yawa da Allah Ta'ala ya keɓance shi da su
kamar yadda ayoyin Alqur'ani da ingantattun hadisan Manzon Allah Sallallahu
alaihi Wasallam suka tabbatar. Daga ciki akwai aya ta ɗaya zuwa ta huɗu da ke cikin
suratul Muzzammil:
يَا أَيُّهَا الْمُزَّمِّلُ
Yã wanda ya
lulluɓe!
قُمِ اللَّيْلَ إِلَّا قَلِيلًا
Ka tsayu
domin yin Sallah a cikin dare (duka) fãce kaɗan.
نِصْفَهُ أَوِ انْقُصْ مِنْهُ قَلِيلًا
Rabinsa, ko
ka rage abu kaɗan daga gare shi.
أَوْ زِدْ عَلَيْهِ وَرَتِّلِ الْقُرْآنَ تَرْتِيلًا
Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu´ãni, daki-daki.
Qiyamul
Laili ba shi da adadin raka'o'i qididdigaggu da dole a kansu ake tsayawa, idan
da mutum zai yi raka'o'i hamsin ko fiye da haka, sannan ya kammala su da
wutiri, to babu laifi, Ibnul Qaɗɗan Alfaasiy ya hakaito cewa: " Malamai sun yi ijma'i
a kan cewa babu iyaka a sallar dare, lallai ita nafila ce, duk wanda ya so ya
yi sallar yadda yaso, ya yi da yawa ko ya yi kaɗan". Duba
Al'iqná'u Fiy Masá'ilil Ijmá'i (1/174).
Sai dai abin
da ya fi shi ne mutum ya yi wutiri da adadin da Manzon Allah Sallallahu alaihi
Wasallam ya yi, wato raka'a goma sha ɗaya, ko goma sha uku, yana yin sallama a kowace raka'a
biyu, sai kuma ya yi wutiri da raka'a ɗaya, kamar yadda hadisi mai lamba ta 749 ya bayyana hakan
a cikin Sahihu Muslim. Wannan adadi shi ne mafifici.
Kuma
mafificin lokacin wutiri shi ne ɗaya bisa uku na qarshen dare, amma idan mutum ya yi
wutirin a farkon dare, ko a tsakiyarsa to babu laifi.
Allah S.W.T
ne mafi sanin daidai.
Jamilu
Ibrahim, Zaria.
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Lvn6zKswf8M8cnTnYUgƘny
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.