𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, ya hukuncin yin sallama ɗaya a cikin sallar
shafa'i da wutiri? Ma'ana ka haɗa su guda uku kayi tahiya ɗaya da sallama ɗaya, ya halasta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salám, ya halast a yi sallar wuturi da
raka'o'i uku, ko da raka'o'i biyar, ko da raka'o'i bakwai, ko da raka'o'i tara.
Amma idan mutum zai yi wuturi da raka'o'i uku ne, to tana
da siffofi guda biyu ne kamar haka:
1. Siffa ta farko ita ce mutum ya jero duka raka'o'i ukun
da yin tahiya guda ɗaya a ƙarshe, sai ya yi sallama.
2. Siffa ta biyu kuma ita ce ya yi tahiya ya yi sallama a
raka'a biyu, sannan ya miƙe ya yi wuturi da raka'a ɗaya.
Dukkan waɗannan siffofi Sunnah ta zo da su, idan yau mutum ya yi
wannan siffar gobe kuma ya canja, to hakan ya yi kyau.
Ya halasta mutum ya yita da sallama ɗaya da tahiya ɗaya, amma ba da
tahiya biyu ba, saboda idan ya yita da tahiya biyu, to ta yi kama da sallar
Magriba, kuma haƙiƙa Manzon Allah ﷺ ya hana a kamanta
ta da sallar Magriba.
Dubi Assharhul Mumti'u Ala Zhádil Mustaƙni'i (4/ 14 - 16) don ƙarin
bayani.
Allah S.W.T ne mafi sanai.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Lvn6zKswf8M8cnTnYUgƘny
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.