Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sallolin Da Ake Yi A Kowane Dare Na Watan Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne Hukuncin Irin Sallarnan da ake cewa Mutane suyi a Kowanne Daren Ramadan kamar a ce Daren Uku ga wata ayi Raka'a shida a karanta Fatiha da Ƙulhuwa ƙafa kaza???

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Toh wannan Irin Sallolin ni awajan ƴan Shi'ah nasanta sekuma ƴan Bidi'a daga cikin Sufaye da Sauransu. Amma Annabi (s.a.w) da Sahabbansa da dukkanin Magabata ba su Kasance sunayin Wata Sallah a Dukkan Daren Ramadan ba in banda Tarawihi. Hatta Irin Tahajjudin da Mukeyi a Goman Ƙarshe na watan Ramadan akwai Maganganun Malamai a kanta domin wasu Malamai suna ganin yin tama a cikin Jam'i Bidi'ane. Amma Tarawihi wadda ake yi abayan Isha'i ita wannan Tun Magabata sunayin ta kuma Annabi (s.a.w) yayi. Toh su ƴan Shi'a dasu da Majusawa su ne waɗanda basayin Tarawihi suna ƙyamarta shi ne se suke ƙirƙirowa Mutane wasu Baƙin Salloli dan saboda su ɗauke Mutane daga yin Tarawihi, shi ne za kaga duk dare akwai Sallarda zasuce kayi dakuma abunda zasuce ka Karanta. Ammafa basuda Aya babu Hadisi kawai wanine zezauna ya tsara maka yadda za kayi dan haka shi ne ya sa Malamai sukace wannan Irin Sallolin duk Bidi'a ne.

Allah ya sa mu dace

🏼Jameel Alhasan Haruna Kabo (ABU ZULAIKHA)

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Lvn6zKswf8M8cnTnYUgƘny

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments