Ticker

6/recent/ticker-posts

Ana Ajiye Yin Sahur Ne Matuƙar Alfijir Ya Fito Ko Da Kuwa Ladan Bai Kira Sallah Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam ina da tambaya na ga lokacin sallar subhi ya canza ana kira biyar da rabi zuwa shida saura minti arba'in da biyar, karfe nawa ya kamata a aje sawur? Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Waalaikis Salaam:- Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, Yana Cewa Ku Jinkirta Yin sahur, Sannan Ku Gaggauta Yin Buda-Baki Matukar Rana Ya Faɗi.

 Kowanne Gari Ko State da Yanayin Fitowar Alfijir Nasu, Ba aDena Yin Sahur Har Sai Alfijir Ya Fito, Sannan a Tsakanin Fitowar Alfijir da Dena Yin Sahur Za a Bada Ratan Minti 20/15. Shi Lokacin Ajiye Sahur ana Amfani Ne Da Fitowar Alfijir, Misali idan Alfijir Din Wajen Ku Karfe 5:00am Yake Fitowa, Toh Wajibi ne Gare Ki Domin Koyi da Sunnar Manzon Allah za ki Ajiye Sahur Naki Ne Tun Karfe 4:45am ko 4:40am a Lokacin Kin Gama Yin Komai Naki Alfijir na Fita ke Daman Kin Riga da Kin Kammala Komai Naki Ba Tare da Cewa ai Kin Ci ko Kin Sha a cikin Alfijir ba.

 

Idan Kuma Alfijir Naku Yana Fitowa Karfe 5:10am ko 5:15 Sai a Kira Sallah na Shiga Yin Sallahn Asubahi, toh indai a Lokacin da Ladan Yake Kiran Sallah Na Biyu a Lokacin ne Alfijir Yake Fitowa, toh za ki Ajiye Yin Sahur Naki Tun Karfe 5:00am a Samu Tsakanin Ki da Barin Sahur Naki da Fitowar Alfijir a Kallah yakai Minti Goma Sha Biyar ko Ashirin. Idan Bawai Kin Makara bane Kina Tashi Bai Wuce Saura Minti 15 Alfijir, toh Nan kam za ki Iya Cin Abincin ki Cikin Sauri na Minti 10, Minti Biyar ɗin Sai Ki Dena Cin Komai Domin Yanzu Alfijir Zai Fito kada Ki Ci Gaba da Cin Abinci Ki Zo Ki Ci Abinci a Cikin Rana. Domin Matukar Alfijir Yafito toh An Shiga Rana Idan Kin Yi Garaje Har Alfijir Ya Fito Kina Cin Abinci Kuma Kin Sani Bawai Ba ki Sani ba, toh Baki da Azumi Sannan idan da Gangan Kika yi Sai Kinyi Kaffara.

Saboda Haka Ki Auna Wani Masallaci Ne Suke Kiran Sallah a kan Lokacin da Alfijir Yake Fita Suke Kiran Sallah na Shiga Yin Sallahn Asubahi, idan Kin Samu Sai ki yi Amfani da Time nasu, idan Alfijir din Yana Fitowa ne Biyar da Rabi, toh za ki Ajiye Yin Sahur Naki tun Karfe 5:10am ki Samu Ratan Minti 20 ko 15 tsakanin ki da Fitowar Alfijir Wannan Shi ya fi Dacewa da Sunnah.

 Sai Ki Bincika ko Kuma Ki Duba da Kanki ki Ga Karfe nawa Alfijir Yake Fitowa. Dafatan Kin Gane???

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah. da

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/LsA4LWfGSme0umoxks5785

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi da

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments