Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin wanda ya shiga jirgi lokacin da aka yi kusan shan ruwa, sai kuma ya rinƙa ganin rana a sama, zai iya shan ruwa?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne Hukuncin Wanda Ya Hau Jirgin Sama Daga Kasar Sa, Rana Ta Kusa Faɗuwa, Amma Bayan Ya Tashi Sai Ya Rinka Ganin Rana, shin zai iya buɗa baki?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ba zai buɗa baki ba har sai rana ta faɗi a idanunsa. Hakama kuma idan ya tashi akwai sauran rana a kasarsa amma sai ya shiga wani garin wanda yanayin kasarsu ya saɓawa na kasarsa. Ma'ana su a wurinsu rana ta faɗi, to sai ya yi buɗa baki. Domin hadisi ya tabbata daga Abu Umamata Albahiliy yace, naji manzon Allah yana cewa "Naji sauti mai tsanani a bayan wani dutsi sai na Tambaya wannan wane irin ihu ne? Sai akace kukan waɗanda ake yiwa azababne a cikin wuta domin suna yin buɗa baki kafin rana ta faɗi". Anan ma'ana tunda yana ganin rana to a wurinsa rana bata faɗi ba ke nan. Kuma Allah (S.W.T) yana cewa "sannan ku cika azumi zuwa dare"

Allah ta'ala ya sa mu dace.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GlolWn2ocAj0vaFZxHKhbL

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments