Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'a Idan Mai Azumi Zai Buɗa Baki

 ذَهَبَ الظَّمَأُ، وَابْتَلَّتِ العُرُوقِ، وَثَبَتَ اْلأَجْرُ إِنْ شَاءَ اللهُ.

Zahabaz-zama-o wabtallatil-'urooƙ, wathabatal-ajru in sha ALLAH.

Ƙishirwa ta tafi, an yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in ALLAH ya yarda.

 Abdullahi bin Amr bin Al-As (R.A) ya ce:

 Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce:

Mai Azumi yana da addu'a da ba'a mayar da ita idan yazo buɗe baki.

 Abdullahi bn Amr (R.A) ya kasance idan yazo buɗa baki sai ya ce:

اللّهُمَّ إِنَّي أَسْأَلُكَ بِرَحْمَتِكَ الّتي وَسِعَتْ كُلَّ شَيْءٍ، أَنْ تَغْفِرَ لِي.

Allahumma inne as-aluka birahmatikal-latee wasi'at kulla shay'i, an taghfira lee.

Ya ALLAH Ina roƙon ka saboda Rahamarka data yalwaci komai, Ka gafarta mini.

ALLAH ka karɓi ibadunmu ka biya mana dukkan buƙatunmu.

ALLAH ka gafartarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen ya ALLAH.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments