Shin kowace mace mai ciki ko mai shayarwa na iya ajiye azumi ta ciyar?

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin wai gaskiya ne cewa duk Mace Mai-Ciki ko Mai Shayarwa za ta iya ajje azumi ta ciyar kawai a madadinsa ko kuma ya abin yake??

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Ko Shakka bābu cewa wannan magana ba gaskiya bace domin kuwa bahaka Shari'a tace ayiba, danhaka dai da farko yana dakyau musani cewa bawai haka kawai dan saboda kasancewar Mace tana da Ciki ko tana Shāyarwa hukuncin yin azumi yafāɗi akantaba, domin dayawa daga cikin 'Yan'uwa Mātā sunyiwa wannan hukunci mummunar fahimta, kodai wasu saboda Jāhilcinsu ko saboda son zuciya kokuma saboda ƙarancin bayani daga wajen su Mālaman da suke basu fatawa akan hakan, domin dayawa daga cikin Ɗāliban-Ilimi zaka samu suna bada fatawane kawai akan cewa Mai-Ciki da Mai Shāyarwa zasu ciyarne kaɗai amadadin azuminsu, wanda kuma bahaka hukuncin yake a Sake ba Ƙaidi ba.

    Idan Mai-Ciki ko Mai Shāyarwa kokuma Maras lāfiya sunājin ƙarfin jikinsu yadda zasu iyayin azumi ba tare da sun galabaita irin galabaitar da ta sāɓāwa yadda akasaba gani abisa al'āda ba, to wajibi ne akansu suyi wannan azumin, idan kuma sukaƙiyi to susani cewa sunbar wani wājibi da Aʟʟαн() Ya wajabta musu suyi, kuma Sai Aʟʟαн() Yākamasu da laifin hakan domin Shidai Aʟʟαн() baza a iya yimasa ƙarya ko wayoba, amma idan ya kasance Mutum yana cikin laulayin da idan ya yi azumi zai tagayyara irin tagayyarar da yawuce na al'ada, kamar misalin Mutum yafita daga hayyacinsa ko yariƙa suma saboda wahala ko wani abu makamancin haka, kokuma yin azumin zai iya ƙāra cutar datake dāmunsa ko ta yi jinkirin warkewa kokuma yakamu da wata sabuwar rashin lafiyar adalilin azumin dayayi, to a nan sai Shari'a tayimasa rangwame akan cewa zai iya cin abincinsa, daga baya kuma idan yawarke sai yarama adadin azumin da yasha, amma ba dalili bane wai kaji Mace tace wai azumi yana bata wahala danhaka bari tasha ruwa itama bayan Sallah sai taciyar, wannan wasane da addini kawai, domin kuwa ana maganane akan irin wahalar da ta sāɓāwa irin wahalar da aka saba ji a al'ada, amma inba hakaba ai koma waye zaiyi azumi dole sai ya ji ajikinsa

    Danhaka kuskurene babba Mutum yarika wasa da lamarin addininsa, Sannan wasu daga cikin Mutāne kuma sukayi wani wāyo na son zuciya, yāyin da akace Mālamai sunyi Saɓāni akan wata Mas'ala ta Fiƙhu, to kawai sukan dubane suga wanne ɓangarene yafi sauƙi sai su ɗauka suyi amfani dashi, ko shakka babu wannan kuskurene babba, domin kuwa idan Mālamai sukayi Saɓāni to anasone Mutum yaɗauki ɓangaren da yake da Dalilai da Hujjoji masu ƙarfi koda kuwa shi ne ɓangaren da yafi wahala ɗin, Aʟʟāн() Ya gānar damu gaskiya ya bāmu ikon aiki da'ita Āmīn-Yā-Rabbi.

    шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

    AMSAWA

     Mυѕтαρнα Uѕмαn

     08032531505

    Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.