KAYAN HADI:-
NAMA KO KIFI
ZOGALE
KAYAN MIYA
TAFARNUWA DA THYME
CURRY DA MANJA KO MANGYADA
MAGGI DA GISHIRI.
KI SILALA NAMANKI DA THYME DA TAFARNUWA DS KAYAN KAMSHI, IDAN YA SILALu, ki SAI KI KWASHE KI AJIYE A
GEFE.
KI ZUBA MAI A TUKUNYAR, IDAN YA YI ZAFI, KI ZUBA KAYAN MIYARKI, KI DAN
SOYA, SAI KI ZUBA NAMAN NAN DA RUWAN
CIKIN SA KI QARA RUWA DAIDAI YADDA ZAI YI MIKI.
KI ZUBA KAYAN HADI SU MAGGI DA KAYAN KAMSHI DAIDAI, IDAN YA FARA DAHUWA KI
ZUBA DAKAKKIYAR GYADARKI, IDAN DA HALI KI SAKA KIFI. +
IDAN KOMAI YA YI DAIDAI YA KAMA JIKINSA, SAI KI ZUBA TSOGALENKI DA KIKA GYARA KIKA WANKE, BAYAN YA DAHU SAI A SAUKE.
(IDAN DA HALI A SAKA TSOGALEN DA YAWA AN FI SON MIYAR TA YI KAURI, DA GYADA.)
0 Comments
Rubuta tsokaci.