KAYAN HADI:-
- CABBAGE
- CARROT
- TATTASAI DA ATTARUGU
- TOMATOES
- ALBASA
- MAGI, GISHIRI, CURRY
- KAYAN KAMSHI
- NAMA (TSOKA)
- MANGYADA
DA FARO ZA A YANKA KABEJI KANANA, SANNAN A FERE KARAS SHI MA A YANKA SHI
KANANA, SAI A HADA DA GREENBENS A WANKE, A ZUBA A TUKUNYA TARE DA MAGI GISHIRI
CURRY THYME, A BARI SU DAHU KAMAR MINTI UKU ZUWA HUDU, A SAUKE.
A GYARA KAYAN MIYA TARE DA JAJJAGA SU SOSAI KO MARKADAWA, AMMA JAJJAGE YAFI
DADI.
DAMAN KIN DAFA NAMANKI, SAI A DAKA YA DAKU SOSAI.
DAGA NAN SAI A ZUBA DAN MANGYADA A TUKUNYA, IDAN YA YI ZAFI A ZUBA KAYAN
MIYAR TARE DA DAKAKKEN NAMAN NAN SHI MA, A ZUBA MAGGI, GISHIRI, CURRY, KAYAN
KAMSHI, A BARSHI YA DAHU KAMAR MINTI GOMA SAI A SAUKE.
0 Comments
Post your comment or ask a question.