Ticker

6/recent/ticker-posts

Wanda ya nemi matar da take idda, zai iya auren ta bayan ta kammala idda?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum.malam ina kwana ya aka ji da jama'a, Allah ya kara ma malm lafiya da tsawan rai mai albarka. Tambayata shi ne idan wani ya nemi macen da take idda ya ce mata yana son ta kasance matar shi nan gaba wai aure ya haramta a gare su in ta gama iddan?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa'alaikum assalam, ya aikata saɓon Allah, tun da Ubangiji ya haramta neman auran wacce take idda a cikin suratul Bakara aya ta: (235).

Ya halatta a gare shi ya aure ta bayan ta kammala idda, saboda wancan saɓon ba zai haramta masa ita ba.

Idan har aka ɗaura aure a cikin idda, malaman Malikiyya suna wajabta raba auran da kuma haramta ta ga wanda ya auretan har abada.

Da fatan kun fahimci bambanci tsakanin neman aure da kuma ɗaura aure a cikin Idda.

Allah shi ne mafi sani

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments