𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam,ina da tambaya mene ne illar kwana da miji da yara a daki ɗaya, abin nufi a nan shi ne har mata da miji su raya sunna a cikin dakin da yaran, Amma bayan yaran sun yi bacci? Allah ya karawa malam basira.
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Abu na farko dai haramun ne bayyanar da tsaraici a
gaban yara ko da kuwa Ƙanana ne, mutukar dai yaron
ya fahimci bambanci mutumin da ke tsirara da wanda ke cikin sutura.
Sannan an yi hani ga ma'aurata su sadu awajen da wani
zai iya jin sautinsu ko kallon motsawarsu ko da kuwa sun lullube jikinsu.
Idan yaron yana da wayon da zai fahimci abin da ake yi,
to haramun ne yin hakan a gabansa ko da kuwa barci yake yi. Domin akwai yiwuwar
farkawarsa alokacin da iyayen nasa ke cikin yin abin da suke yi, kuma zai yiwu
yaje yana zantar da abin da idonsa ya gani, ko amakaranta ko awajen abokan
wasansa.
Duk da cewa wasu daga cikin Maluman Malikiyyah sun
dauki abun bisa karhanci, kamar Shaikh Aliyyul adawiy a cikin Hashiyarsa wacce
ya yi wa littafin Iziyyah, ya ce makruhi ne mutum ya sadu da matarsa alhali
akwai wani a cikin dakin, ko da Ƙaramin yaro ne ko babba. To
amma wasu maluman sun ce karhancin ya tsaya ne kan idan yaron Ƙarami ne wanda ba zai iya fahimtar komai game da abin da ake
yi ba, kuma idan barci yake yi ba' a farke ba.
Abin da ya fi shi ne ma'aurata idan za su sadu su keɓance kansu a wani dakin da
babu kowa sai su. Amma idan akwai larurar rashin isashen muhalli, watakila suna
kwana daki ɗaya tare da yaransu Ƙanana waɗanda basuyi hankali ba, to
wajibi ne su sanya wani labulen da zai suturcesu daga idon yaran, sannan su
kashe fitilar dakin, kuma su kiya yi bayyanar da sautin da zai iya farkar da
yaran da ke barci.
Saboda wannan ne Allah Madaukakin Sarki ya umurci
muminai su hana yaransu Ƙanana shigowa garesu
alokutan da aka kebancewa da iyali, har sai an ba su izini.
Allah ya ce: "YAKU WAƊANDA SUKA BADA GASKIYA! BAYINKU WAƊANDA DAMSHINKU YA MALLAKA, DA KUMA (YARANKU ƘANANA) WADANDA BASU BALAGA BA, SU NEMI IZININKU (KAFIN SU
SHIGO INDA KUKE) ALOKUTA UKU:
1. KAFIN SALLAR ALFIJIR (WATO KAFIN ASUBAH ke nan).
2. DA LOKACIN DA KUKE TUBE TUFAFINKU SABODA ZAFI (DA
TSAKAR RANA ke nan).
3. DA KUMA BAYAN SALLAR ISHA'I."
Wajibi ne Ma'aurata su dora 'ya'yansu a kan tarbiyyah
ta musamman game da neman izinin shigowa cikin dakin da iyayensu ke zaune, ko
da kuwa yaran basu balaga ba.
Haka nan wajen saduwa wajibi ne akiya yi yin tsirara a
gaban yara, ko saduwa a gabansu ko da kuwa barci suke yi, sai dai idan Ƙanana ne sosai wadanda basu wuce shekara ɗaya ko biyu ba, wasu maluman
sun ce za a iya saduwa a gabansu ko da ba barcin suke yi ba.
WALLAHU A'ALAM.
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.