Ticker

6/recent/ticker-posts

Wanda Ya Auri Mace Kafin Ta Gama Idda, Babu Aure A Tsakaninsu Har Abada

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu'alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, Dr. Yanzun nan aka aiko min da fatawa kamar haka: Wata ce take tare da mijin ta na farko, sai wani ya taimaka mata har ta fito daga gidan, kuma ya aure ta kafin iddarta ta cika. Toh tana zaune sai ta ji a Sunna TV ana maganar wannan matsalar, sai ta sanar da mijin, ta nemi su rabu, sai ya ba ta Ƙur'ani ta rantse cewar idan ta kammala iddah, za ta aure shi. Mene ne hukuncin aurenta da mutumin nan, kuma mene ne hukuncin rantsuwarta ?, domin yanzu tana so jibin nan a ɗaura mata aure da wani mutumin daban. Allah Shi ba da lada.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikum assalam, Auren da suka yi batacce ne, saboda Allah ya hana Aure a cikin idda a cikin suratul Bakara aya (235), sannan A Mazhabar Malikiyya babu Aure a tsakaninsu da wancan mijin har abada tun da ya aureta a cikin idda, saboda Ka'idar:

من تعجل شيئا قبل أوانه عوقب بحرمانه

Duk Wanda ya gaggauta abu kafin lokacinsa za a yi masa ukuba, ta hanyar haramta masa abin. Idan ta yi kaffara Shi ke nan ta warware rantsuwarta, Annabi (SAW) yana cewa "Idan ka yi rantsuwa ba za ka yi abu ba, sai ka ga aikata abin ya fi alkairi to ka yi kaffara sai ka aikata abin da ya fi alkairi"

Ya wajaba su gaggauta tuba saboda sun yi Aure a cikin Aure, Allah ya kare mu daga karkacewa da kuma son zuciya.

Allah ne mafi sani

Amsawa: Dr. Jamilu Zarewa

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇Thttps://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments