Waƙar Talauci - Ta Mohammed Bala Garba

    1. Dakata mana kai talauci,
                  Gaskiya ka uzzure ni.

    2. Ni Musulmi ne ka gane,
              Ka saka ni ina ta muni.

    3. Ba ni bacci ba salati,
           Don Rasulallah ka bar ni.

    4. Na ci burin ƙara aure,
           Don mugunta ka hane ni.

    5. Babu boko babu allo,
          Ga shi dangi sun tsane ni.

    6. Babu mai kallon ƙimata,
            Ko ya tako don ya gan ni.

    7. Ga shi ni ne dai na fari,
             Kuma ƙanne sun guje ni.

    8. Babu ma mai tuntuɓa ta,
             Ko ya zo don min bayani.

    9. Ko gidana in ka duba,
               Babu damar yin sukuni.

    10. Take sai ko a ta da mita,
                Har da gaula an kira ni.

    11. Ga shi 'ya'yana ka duba,
                 Talla babu dare da yini.

    12. Da na ce ba na buƙata,
                  Aka ce mini za a sau ni.

    13. Daga nan sai na sadudu,
              Tun da babu kuɗi gare ni.

    14. Shekaru sun lulluɓe ni,
               Ga talauci ka riƙe ni.

    15. Shin da ribar da ka samu?
               In akwai ka faɗo gare ni.

    16. Na haɗaka da Rabbi Sarki,
               Don Rasulallah ka bar ni.

    17. Rabbana ƙara na kawo,
                  Don taulaci ya tsane ni.

    18. Almujibu ka yaye komai,
             Sa ya sau ni a wanga ƙarni.

    19. Rabbi ninka dubun salati,
                   Gun mafi daɗin bayani.

    20. Alihi nasa sako sahabu,
                  Ɗanbala ne kun ko ji ni?

    Mohammed Bala Garba
    13/3/2023.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.