Wani ɗan sanda ne mazaunin wani ƙauye daf da shiga Kano in an baro Zariya. Matansa biyu ne. Da sukuta fara 'yar daf da ƙasa da kuma siririya baƙa doguwa. Da gaske saboda sirantarta kamar iska ta kwasheta ta zubar a gefe guda sharaf irin yadda iska ke wa kayan da aka shanya.
Saboda sirantarta kuma suna yi mata ganin rashin ƙarfi,
sai ƙawayen
'yar dumadumar nan ke zuga ta wai ita ce matar gida jiki duka tsoka. Ita dai
farar matar ɗan sandan
nan bata ganin ƙibarta ko muni saboda tana da hasken fata, wannan tasa sai take ɗaukar
kanta a matsayin mowar gida musamman ganin cewa ita Allah ya bai wa haihuwar
'ya'ya maza uku da mata biyu. Ita kuwa 'yar uwarta sai ka ce juya, Allah bai ba
ta haihuwa ba duk da sun jima tare da mijin nasu.
Rashin haihuwa da sirantarta
wannan tasa ƙawayen 'yar dunduɓar
matar ɗan sandan nan
su ke yi mata kirari da DUNDUƁUSAI.
Da haka su ke yi wa abokiyar zamanta habaici. In sun so cin
mutuncinta sosai sai su ɗinga
yada magana suna ban da kwashe-kwashen namiji me ya gani a jikin muciya tsular
gida.
Kwanci ta shi rannan sai aka zo taron bikin babbar 'yar
DUNDUƁUSAI.
Ai kuwa sai ƙawayanta
suka haɗa bakin su ci
mutuncin kishiyarta wadda Allah bai ba wa haihuwa ba har zuwa wannan lokaci.
Nan suka sa Sanƙira yai shila a sa musu ƙida
suka shiga fage suna waƙa kamar haka:
Baiti: Ke ce mowa dole a bi ki.
Amshi: Dundubusai matar ɗan
sanda.
Baiti: Kaza dole ganin 'ya'yanki.
Amshi: Dundubusai matar ɗan
sanda.
Baiti: Kin ci gida kuma dole a ba ki.
Amshi: Dundubusai matar ɗan
sanda.
Baiti: Tarwaɗa
ba kaushi fatarki.
Amshi: Dundubusai matar ɗan
sanda.
Baiti: Ɓauna ba rama a jikinki.
Amshi: Dundubusai matar ɗan
sanda.
Baiti: Ɗan sanda shi ne angonki.
Amshi: Dundubusai matar ɗan
sanda.
Baiti: Taka rawa mai ƙin ki ta ganki.
Amshi: Dundubusai matar ɗan
sanda.
Baiti: Duk sharrin bora ta bar ki.
Haka dai suka ci gaba da habaici - habaicensu suna cashewa
suna juya jiki da ɗuwaiwuka
ana dariya da yi musu liƙi.
Bayan sun gama cashewarsu da shewa da shegantakarsu suna
tafa hannuwa a ganinsu sun gama da abokiyar zaman ƙawarsu.
Can sai ga ta nan ta shigo fage ta ci ɗamara kamar ƙugunta
zai tsinke.
Da ganin haka sai kallo ya koma sama, har ana shirin a fara
watsewa, sai wasa ya dawo sabo. Ta nunfasa ta ce Sanƙira yai mata shila ga
kyautar kuɗinta tana
so a buga mata kiɗa
mai taken Tsulakatai, amma ita za tai wakarta da kanta, don haka tana roƙon ai
mata amshi da cewa:
"Tsulakatai ma
sonta ake yi".
Ana kiɗa
tana waƙa
tana kuma taka rawa. Ga baitocin da ta rera a cikin wakarta kamar haka:
Amshi: Tsulakatai ma sonta ake yi.
Baiti: Tun da gidansu ya je auranta.
Amshi: Tsulakatai ma sonta ake yi.
Baiti: Don ko mijinta yana ƙaunarta.
Amshi: Tsulakatai ma sonta ake yi.
Baiti: Tuwonta yana ci ran kwananta.
Amshi: Tsulakatai ma sonta ake yi.
Baiti: Tun da yana ɗaukar
butarta.
Amshi: Tsulakatai ma sonta ake yi.
Baiti: Baya ƙin nono.da furarta.
Amshi: Tsulakatai ma sonta ake yi.
Baiti: Bai yajin kwana ɗakinta.
Amshi: Tsulakatai ma sonta ake yi.
Baiti: Wuyarta ta gimla zai kalleta.
Amshi: Tsulakatai ma sonta ake yi.
Baiti: Ɗan sanda bai ƙin maganarta.
Amshi: Tsulakatai ma sonta ake yi.
Baiti: Mowar ɗaki
ce a gidanta.
Amshi: Tsulakatai ma sonta ake yi.
Baiti: Ɗan sanda baya dukanta.
Amshi: Tsulakatai ma sonta ake yi.
Baiti: Baya bin ta yana korarta.
Amshi: Tsulakatai ma sonta ake yi.
Baiti: Ko tai bacci bai ƙyaleta....
Nan masu yi mata dariya fa suka hau sowa, su uwar amarya da
aka fara yi wa kiɗan
Dunduɓusai nan su ka
bar fage suna cizon yatsa, da borin kunya ana yi musu ihu da dariya.
Hausawa sun yi gaskiya da suke cewa, "Baki yasan me zai
faɗa, amma bai son me
za a mayar masa ba".
Ƙurunƙus.
0 Comments
Rubuta tsokaci.