Tuni intanet ya zama wani ɓangaren rayuwar ‘yan’adam. A yau, ba za a
iya ƙiyasin mizanin ɗumbin
munanan matsalolin da za su auku ba idan aka ce babu intanet daidai da minti
guda. Ɓangarorin ilimi da harsuna da dama sun rungumi al’amarin intanet ka’in-da-na’in. Hausa na ɗaya daga cikin harsunan da suke tasowa a
duniyar intanet. A zuwa ƙarshen shekarar 2020, akwai a ƙalla
manyan kafofin intanet na Hausa guda arba’in da huɗu (44). Lura da haka, ya zama dole a
gudanar da nazarce-nazarce a wannan fanni domin daidaita al’amarin wanzuwar
Hausa a duniyar intanet. Maƙasudin wannan bincike shi ne nazartar (i)
yanaye-yanayen al’adun Hausawa cikin duniyar intanet da (ii) ci gaba da ƙalubalen
da ke dabaibaiye da kafafen intanet na Hausa, da kuma (iii) hanyoyi da matakan
amfani da intanet wajen bunƙasawa da yayata al’adun Hausawa. Farfajiyar binciken ba ta
wuce al’adun Hausawa da ke cikin
duniyar intanet ba. An yi amfani da manyan hanyoyi biyu domin gudanar da
binciken. Hanya ta farko ita ce hira. Ta biyu kuwa ita ce nazarta da ƙwanƙwance ƙunshiyar
kafafen intanet kai tsaye. An yi amfani da ra’in Pulatoriyya (Platonism) wajen gudanar da binciken
inda aka ɗauki intanet a matsayin
duniya mai zaman kanta wanda kuma al’amuranta ke da alaƙa da abubuwan da ke gudana a duniyar yau da
kullum. Sannan an yi amfani da hanyar ɗora aiki da ta
dace da tunanin Bahaushe cewa “zamani riga ce.” Lallai kuwa ya zama wajibi
Hausawa su taka rawar kiɗan zamani domin
tabbatar da wakilcinsu a duniyar intanet bai faɗa hannun waɗanda za su masa riƙon sakainar kashi ba. Binciken ya tabbatar da cewa, a yau babu wani al’amari da zai iya ci gaba, ya ɗaukaka, duniya ta san shi kuma ta karɓe shi, ba tare da an haɗa da intanet ba. Har ila yau, binciken ya gano cewa, tuni
al’adun Hausa suka yaɗu a duniyar
intanet. Bayan haka, ya fahimci cewa akwai matsaloli da dama da ke dabaibaye da
kasancewar Hausa a duniyar intanet, ciki har da matsalolin da suka shafi ƙarancin ilimin Hausar ga
masu gudanar da kafafen intanet na Hausa. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da kira ga waɗanda abin ya
shafa, ciki har da hukumomi da malamai da manazarta, da su waiwaici al’amarin
Hausa a duniyar intanet domin samar da kyakkyawan wakilci.
- Home-icon
- Al'ada
- _Maguzawa
- _Zamantakewa
- _Abinci
- _Magunguna
- _Sana'o'i
- _Gine-Gine
- _Tufafi
- _Bukukuwa
- _Addini
- ADABI
- _Azanci
- __Karin Magana
- __Kacici-Kacici
- _Waƙoƙi
- __Waƙoƙin Baka
- ___Na Gargajiya
- ___Na Mawaƙa
- __Rubutattun Waƙoƙi
- __Waƙoƙin Zamani
- _Zube
- __Almara
- _Wasan Kwaikwayo
- __Finafinai
- HARSHE
- _Ƙirar Sauti
- _Tsarin Sauti
- _Ƙirar Kalma
- _Ginin Jimla
- _Ilimin Ma'ana
- _Walwalar Harshe
- _Fassara
- _Ƙa'idojin Rubutu
- _Kimiyya da Fasaha
- BIDIYOYI
- HOTUNA
- EDUCATION
- _Courses
- Humanities
- _Poems
- _Linguistics
- _Literature
- _Translation
- _History
- SOCIAL SCIENCE
- _Theories
- _Sociology
- _Psychology
- _Economics
- _Philosophy
- _Political Science
- SCIENCES
- _Agriculture
- _Crypto
- _Health
- _ICT
- _Mathematics
- Jokes
2 Comments
Na ji daɗi sosai da ziyartar wannan shafi, saboda na sami ƙarin ilimi game da harshe Hausa. Ina jinjina ma masu sarrafa wannan shafi. Naku, Abdou Magawata, manazarcin harshe a Nijar.
ReplyDeleteMun gode sosai Malam Abdou Magawata.
ReplyDeleteKana iya turo mana rubuce-rubucenku domin ɗorawa saboda amfanar sauran manazarta daga faɗin duniya.
Post your comment or ask a question.