Ticker

6/recent/ticker-posts

A Bakin Aurenki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam tambayata ita ce miye hukuncin wannan auren a musulumci? Miji ya ce wa matarsa idan kika je anguwarki ki dawo karfe 4, idan kika wuce haka a bakin aurenki. To malam sai ta kara minti ɗaya to wai shin saki ɗaya ne ko uku? Shi miji ya ce ɗaya ita kuma ta ce uku tun da a bakin aurenta ya ce. To malam miye mafita?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa'alaikumus Salamu, duk lokacin da aka yi saki, sai kalmar da aka yi amfani da ita wurin yin saki ɗin ba ta bayyana saki nawa ake nufu a zahiri ba, to a nan miji ne yake da ikon faɗin ko saki nawa yake nufi ba matar ba, idan kuma duk aka kasa samun daidaito, to sai a garzaya zuwa wurin ƙuliya, domin shi idan ya ba da hukunci dole ne a sallama.

Sannan kuma game da mijin da ya ce wa matarsa idan ta aikata abu kaza a bakin aurenta, sai ko ta aikata ɗin, to irin wannan matsalar malamai sun yi mata kallo ta fuskoki guda biyu, idan miji ya ce wa matarsa haka da nufin ya sake ta ne, to wannan mata ta saku da ijma'in malamai.

Amma idan miji ya ce wa matarsa haka da nufin tsoratar da ita ce da hana ta aikata wannan abin, ba manufarsa sakinta ya yi ba, sai kuma aka yi rashin sa'a ta aikata hakan, to wasu malamai sun ce wannan hukuncinsa shi ne hukuncin kaffarar rantsuwa ba hukuncin saki ba, kamar yadda Shaikh Ibn Baáz ya yi bayani.

Majmú'u Fataáwá na bn Baáz 22/106.

Saboda haka lamarin saki yana hannun miji ne ba mata ba. Duba amsar tambaya ta 119 don ƙarin bayani a kan hukuncin wanda ya ce wa matarsa idan ta aikata abu kaza a bakin aurenta.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments