Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wacce Ake Bin Ta Azumin Shekari Biyu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Mallam ya fama da jama'a Allah ya saka da gidan Aljanna Firdausi Ameen. Don Allah mallam. Ana bi na azumi na shekara biyu ban rama ba ba ni da lafiya. Yanzu na sami sauki ya zan yi da wancan Azumin. Kuma Ina so na yi azumin Monday da Alhamis shin zan iya yi ?

(Daga Amina Adam)

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

A'a Malamai sun ce bai halatta ga wanda ake binsa azumin farillah kuma ya yi azumin nafila ba. Har sai ya rama. Sai dai wasu Maluman sun yi sassauci game da azumin da yake da Ƙayyadadden lokaci kamar Sittu Shawwal da kuma azumin ranar arfa, sun ce mutum zai iya yinsu ko da ana binsa na farilla.

Game da ramukon azumin da ake binki kuma, Maluman Mazhabinmu na Malikiyyah sun ce wanda ake binsa azumi bai rama ba, har wani Ramadan ɗin ya zo ya wuce, to idan ya tashi ramawa sai ya haɗa da ciyarwa bisa kowacce ranar da ake binsa.

WALLAHU A'ALAM.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments