Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Da Yabar Azumin Ramadan Har Wata Shekara Ta Zagayo Bai Biya Ba.

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam miye hukuncin Wanda ya bar azumi guda ɗaya har wata shekara ta zagoyo shin biya zai yi ko kuma akwai ciyarwa kuma yaya ake ciyarwa?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa'alaikumussalam Warahmatullah Wabarakatuhu.

Malaman mazhaban Malikiyyah suka ce.: Idan mutum ya bar azumin da ake bin sa bashi da gangan ba babu wani uzuri har wani azumin ya zagayo bai biya ba, sai bayan azumin wannan shekaran ne zai biya. Ko mace ita ma ta bari har na wani shekara ya samu na bara.

Sukece mutum zai biya wannan azumin sa'annan ya yi wa azumin Kaffara.

Kaffarar shi ne ya ciyadda miskini ga kowani azumi guda ɗaya. Wato in azumin guda biyar ne misali, to zai biya azumi biyar sannan duk randa ya yi azumi sai kuma ya ciyadda miskini ɗaya. ke nan zai ciyar da miskinai biyar. Amma idan ya biya wannan azumin bara ɗin kafin Ramadan ta kama, misali a ce ya biya a watan Sha'aban to wannan babu kaffara a kan sa. Amma in har ya sake wata Ramadan ta kama ana binsa na bara. To in ya tashi biya zai yi kaffara.

 

Dukda wasu malamai suna ganin cewa ba zaiyi wani kaffara ba saboda babu hujja a kan haka. Ammadai fatawan Malaman mazhaban Malikiyyah shi ne Rajihi, saboda Saddun Lizzariy'ah

WALLAHU A'ALAM.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

 ************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments