Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne ingancin hadisin: “Duk wanda ya sanar da mutane watan ramadan, za a haramta masa shiga wuta”?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne ingancin hadisin: Duk wanda ya sanar da mutane watan ramadan, za a haramta masa shiga wuta?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah.

Hadisin da ake jingina shi ga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wai cewa "Duk wanda ya sanar da mutane game da watan Ramadana to ba zai shiga wuta ba" wannan hadisin ba ya cikin litattafan Sunnah kaf!!

Kuma babu wani ɗaya daga cikin malamai da ya yi rubuce-rubuce a kan falalar watan Ramadan da har ma ya gargaɗi mutane a kan zuwan ramadan, kamar yadda babu wanda ya ambace shi a cikin ko da hadisai raunana ko cikin wanda aka ƙago. Don haka bai inganta ba!

 Imam Al-Suyuti ya ce a cikin “Tadrib Rawi” (1/327):

 Ibnul Jawzi ya ce: “Ya yin fadin wanda ya ce: “Idan kuka ga hadisin da ya saɓa wa hankali, ko ya saɓa wa abin da aka (saba) ruwaitowa, ko ya saɓa wa ƙa’ida, to ku sani ƙagaggen hadisi ne.

 Sai ya ce: Abin da ake nufi da saɓa wa ƙa’ida shi ne kasancewar hadisi ya kasance a wajen Musulunci daga sanannun isnadi da littafai.” 👌

 Don haka bai halatta a tura ko yaɗa wannan hadisin ba sai dai don manufar a gargadi mutane akansa cewa karya ne yana da illa bai inganta ba. Domin faɗin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa "Karya a kaina ba ta zama kamar yi wa kowa karya ba, duk wanda ya yi min karya da gangan, to ya nemi wurin zamansa a cikin Jahannama" Bukhari (1229) ya ruwaito. Muslim ma ya ruwaito shi a cikin gabatarwar littafin sa (3).

Haka a cikin hadisin Ibn Abbas a cikin Tirmizi: “Ku kiya yi magana daga gare ni sai dai abin da kuka sani, don haka wanda ya yi min karya da gangan, to ya nemi wurinsa a cikin Wuta." Allah ya tsare mu

 A rubututtuka na, a baya na yi bayani kan falalar watan Ramadan, da azumi a cikinsa da tsayuwa a cikinsa da sauran manyan ibadu masu lada a cikinsa, za a iya dubawa shafukan mu don gani.

 Allah ya sani.

✍️Abou Khadeejatu Assalafeey

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments