Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Ajiye Kare A Gida Saboda Gadi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Dr. Mene ne hukuncin ajiye kare a gida saboda gadi? Allah muke roƙo ya ƙara wa Dr lafiya da basira Ameen.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikum assalam, Ya tabbata a hadisin Bukhari da Muslim cewa: "Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai hoto ko kare a ciki.

A wani hadisin mai lamba ta: 2974 da Muslim ya rawaito Annabi yana cewa: "Duk Wanda ya rike kare, in ba Karen noma ba ko farauta ko kiwo, to Allah zai tauye masa manyan lada guda biyu a kowacce rana.

Da yawa daga cikin malamai sun yi kiyasin KAREN GADI a kan wadancan nau'ukan guda uku da suka gabata, don haka ya halatta musulmi ya riki Kare saboda gadi in har akwai buƙatar hakan.

Ba ya halatta a siyar da kare kowanne iri ne, saboda Annabi ya hana cin kuɗin Kare a hadisin da Muslim ya rawaito kuma ya kira Shi da dauda.

Duk da cewa an halatta wadancan nau'ukan guda huɗu saboda buƙata sai dai bai halatta a siyar da su ba, saboda Ka'ida sananniya a wajan malaman Fiƙhu wacce take cewa:

ما جوز للحاجة لا يجوز أخذ العوض عليه

Idan mutun yana buƙatar ɗaya daga cikin wadancan nau'uka na karnuka guda huɗu da suke halatta, kuma bai samu wanda zai ba shi kyauta ba, ya halatta ya siya, Amma zunubin sayarwar yana kan wanda ya sayar tun da shi ne bai bayar ba, kamar yadda Ibnu Hazm ya fada a littafinsa na Muhallah 4/793, Ka'ida tabbatacciya a wajan malamai tana cewa:

ما حرم سدا للذريعة يباح للحاجة أو المصلحة الراجحة

Allah ne mafi sani.

Amsawa

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

HUKUNCIN KIWON KARE 🐕 (DOG)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, barka da wannan lokaci. Mallam ina son karin bayani akan hukuncin mutumin dake kiwon kare (dog).

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ajiyar kare agida yana daga abubuwan da addini ya hana sai har in da dalili mai karfi. Saboda ingantattun hadisan dake nuna hakan. Misali hadisin Sayyiduna Abdullahi bn Umar (radhiyal-Lahu anhuma) wanda ya ce : Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce "Wanda ya ajiye kare (agidansa) in banda karen dake kiwon dabbobi ko domin farauta ba, to ana ragar Qirati biyu daga ladansa a kowacce rana" Bukhariy da Muslim suka riwaitoshi).

Qirati ɗin nan, Malamai sunce wani yanki ne na ladan mutum wanda girmansa da fadinsa yakai kamar girman dutsen Uhudu.

Acikin wata riwayar kuma wacce Imamu Muslim ya karɓo ta hanyar Sayyiduna Abu Hurairah (radhiyal-Lahu anhu) Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam cewa yayi : "Wanda ya ajiye kare in banda karen daje kiwon dabbobi ko domin farauta ko domin (gadin) amfanin gona, to a kullum ana ragar Qirati guda daga ladansa.

Kamar mutumin da shi farautar ita ce Sana'arsa, ta wannan hanyar yake cin abinci, ko gadin wata dukiya, to wannan zai iya ajiyar kare agidansa ko wajen da yake gadin amma bisa wasu Qa'idodi kamar haka

1. Kada ya rika sakinsa sai in fita zaiyi dashi zuwa wajen farautarsa. Saboda ba ya halatta ka saki karenka yana shiga gidajen makobtanka yana chutar dasu ta hanyar yi musu ɓarnar dabbobi ko kajinsu ko kayan abincinsu. Wannan yana daga cikin cutarwa kuma Allah ya haramta chutar da makobci.

2. Kada ka saki karenka yana tsorata mutane masu wucewa ta kofar gidanka. Shima wannan chutarwa ce. Kuma haramun ne tsorata Musulmi ko chutar dashi.

3. Ya zamto wajen da za ayi kiwon karen a cikin daji ne, ko gefen gari, ko wajen wani kampani ne ko Ma'aikata ko wani wajen da aka ajiye wata dukiya kuma babu hada-hadar jama'a sosai awajen.

4. Ya zamto ana bashi cikakkiyar kulawa da tsafta cewa yadda ba zai rika tsoma bakinsa cikin abinci ko abinsha na mutane ba. Saboda kazantar dake cikin yawunsa (har gashin jikinsa ma bisa ra'ayin wasu Maluman).

Dangane da ajiyar kare domin yin gadin amfanin gona, wannan dalilan halascinsa afili suke. Ajiyarsa domin farauta ma, har a cikin Alqur'ani Allah yayi maganar halascinsa (a farkon suratul Ma'idah)

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَوْفُوا بِالْعُقُودِ أُحِلَّتْ لَكُم بَهِيمَةُ الْأَنْعَامِ إِلَّا مَا يُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ غَيْرَ مُحِلِّي الصَّيْدِ وَأَنتُمْ حُرُمٌ إِنَّ اللَّهَ يَحْكُمُ مَا يُرِيدُ

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! ku cika alkawurra. An halatta muku dabbobin jin dãɗi fãce abin da ake karantãwa a kanku, bã kunã mãsu halattar da farauta ba alhãli kuwa kunã mãsu harama. Lalle ne, Allah Yanã hukunta abin da yake nufi. (Suratul Ma'idah Aya ta 1)

Amma ajiyarsa domin yin gadi agida, Malamai sun ce idan a cikin daji kake zaune kamar gidan gona ko rugar fulani, to wannan babu laifi ayi kiwon karen bisa wadancan Qa'idodin da na fada abaya. Amma ga wanda ke zaune a cikin gari ko birni, suka ce wannan bai halatta ba. Musamman wanda ke zaune a cikin unguwa atsakiyar jama'a. Saboda chutarwar da yin hakan zai janyo wa jama'ar da ake zaune tare dasu.

Malamai sunyi saɓani game da shin gashin jikinsa da yawunsa najasa ne, ko ba najasa ba ne?

Imam Abu Hanifa da Imamu Ahmad (acikin daya daga fatawoyinsa biyu) sunce gashin kare ba najasa ba ne. Amma yawunsa najasa ne.

Imam Shafi'iy da Imamu Ahmad (acikin daya fatawar tashi) sun ce gashin kare da yawunsa duk najasa ne. Duk su ukun nan sun dogara ne da ingantacce hadisin Abu Hurairah wanda a cikinsa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yayi umurni da wanke duk kwanon da kare ya sanya bakinsa, wanki bakwai ko takwas awata riwayar.

Imamuna Malik shi kaɗai ne yake ganin cewar gashinsa da yawunsa ba najasa ba ne. Ya dogara da ayar cikin suratul Ma'idah wacce ta halatta cin naman farautar da kare ya kama. Kuma Allah bai ce sai an wanke kafin adafa ko agasa aci ba.

Ta kowacce fuska dai rashin yin kiwon nasa shi ne abinda yafi alkhairi ga Mumini. Musamman idan mutum yasan cewa yanayinsa bai dace da kiwon karen ba, bisa wadancan Qa'idodin da aka fada abaya.

Daga illolin da kiwon nasa je haifarwa dai akwai

1. Tauyewar ladan ayyukanka a kowacce rana.

2. Mala'ikun rahama basa shiga gidan da ake ajiyar kare, kamar yadda wasu hadisai da dama kuma ingantattu suka tabbatar.

3. Ya'duwar chutattukan dake kama hanta da hunhun Ɗan Adam. Kamar yadda likitocin musulunci suka tabbatar.

4. Chutar da makobta ta hanyoyi da dama. Bayan kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya lissafa chutar da makobci a cikin manyan zunubai kamar dai yadda kowa ya sani.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa... 

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments