Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Sadu Da Matarsa, Alhalin Yana Azumin Nafila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamun alaikum malam ina hukuncin wadda yana azumin nafila, sai sha'awa ta zo mai sai ya karya kuma ya sadu da matarsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikum assalam to ɗan'uwa malamai sun yi saɓani game da wanda ya sadu da matarsa, alhalin yana azumin nafila, akwai wadanda suka ce sai ya sake, saboda ya ɓata aikinsa wanda ya faro. kuma Allah yana cewa: "Kada ku ɓata Ayyukanku" (Muhammad aya ta: 33).

Akwai malaman suka tafi a kan cewa ba zai sake azumin ba, kuma ba shi da laifi. Wannan maganar ta ƙarshe, ita ce daidai, saboda Annabi s.a.w. yana cewa: "Mai azumin nafila sarkin kansa ne, in ya ga dama ya cigaba da azumi, in ya ga dama kuma ya karya". (Albani ya inganta shi a sahihul-jami'i hadisi mai lamba ta: 3854).

 

Wannan hadisin sai ya nuna ba shi da laifi idan ya karya azumi yana tabbata da cin abinci ko abin sha, ko jima'i.

Don neman Karin bayani duba Tuhfatul- Ahwazy 3/356

Allah Ne Mafi Sani.

Amsawa: Dr. Jamilu Zarewa.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments