Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Addu’a Bayan Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aslmalaikum mlm ina da tanbaya. tanbayata ita ce kamar haka addu'a idan anka idar da Sallah haramci ko halaci ina son mlm ya yimain bayani a kan haka Allah yakarama mlm lafiya

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Allah yana cewa a cikin suratul bakara aya (186)

"UJIYBU DA’AWATUD DAAIY IZA DA’AAN"

"Ina amsa rokon mai roko ya yin daya roke ni”.

wannan ba wani lokaci da Allah ya ware ya ce ban dashi.

Ya Ɗan'uwa: musulmi yana da lokuta muhimmai da Allah (S.a.w) yake amsa adduarsa musamman in ya idar da sallar farillah. Abin da zai tabbatar maka da haka shi ne fadin Allah (s.w.t)

" FA’IZA FARAGATA FANSAB, WA ILAA RABBIKA FARGAB "

”Idan ka idar da “sallarh” ka kafu ka yi kwadayi izuwa ubangijinka” suratul sharhi aya ta(7-8).

Malaman tafsiri sun fassara wannan aya da ma’ana biyar amma kunzumin malamai sun tafi a kan cewa ma’anar wannan aya shi ne (FAIZA FARAGATA MINAS SALATI FANSUB LID DUAA’I )” idan ka idar da sallah ka kafu kaita addu’a”.

 

Manya manyan sahabbai kamar ibn abbas da tabi’ai kamar dhahhaku da mukatilu da mujahidu sun fassara wannan ayar da wannan ma’ana, malaman tafsiri kuwa da suka fassara wannan ayar da wannan ma’ana akwai:- imamul mufassirina (addabari)juz’I na 12 shafi na 760, faharaddinir raazi akicin “mafatiyhul gaib”juz’I na 32 shafi na 8,ibn kasiyr a cikin “tafsirul kur’an”juzu’I na 4 shafi na 530.khur dabiy juz’I na 20 shafi na 74, dabriysi a cikin “mujma’ul bayaan’shi kuwa cewa ya yi:- wannan shi ne ra’ayin yayan Annabi (s.a.w) ya ce ma’anarsa (FAIZAA FARAGATA MINAS SALAATIL MAKTUUBATI FANSUB ILAA RABBIKA BID DU’AAI WA RAGABA ILAIHI FIL MAS’ALATI YU’UDIKA)” idan ka idar da sallar farilla ka kafu izuwa uban gijinka da addua kai kwadayi gareshi cikin roko zai baka “

Sannan annabi (s.a.w) yana cewa:( IZAA SALLAH AHADAKUM FAL YABDA BI TAH MIYDULLAHI TA’AALAH, WASSANAAI ALAIHI, SUMMA YUSALLI ALANNABIYYI, SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA, SUMMA YAD UW BIMA SHAA’A)

”Idan ɗayanku ya yi sallah ya fara da godiya ga Allah, sannan ya yi masa kirari sannan ya yi wa Annabi (S.A.W) salati sannan ya yi roko da abin da yaso. Amma wasu gwanayen kauce kauce sukance ba addu’ar suke musawaba a’a jam’inta suke musawa. ta shi ma jam’in addu’ar bayan sallar ga dalilinsa daga Allah (swt) da Annabi (s.a.w)Allah yana cewa (YA BUNAYYA AKIMIS SALAATA WA’AMUR BIL MA’ARUUFI ) surah lukman aya 17” ya dana ka tsai da sallah ka yi umarni da kyakyawa” a harshen lukman.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments