Haƙƙoƙin Aure A Bisa Alƙur'ani Da Sunnah (Darasi na 32) - Mu Gyara Kuskurenmu Ma'aurata

    Akwai abubuwa da yawa waɗanda Ma’aurata suke aikatawa a lokacin Jima’insu.

    Kuma waɗannan abubuwan suna da illoli masu yawa dangane da lafiyarsu jikinsu ko addininsu. Ga wasu ‘yan kaɗan Zan lissafo.

    RASHIN GABATAR DA WASANNI KAFIN JIMA’I.

    Sam ba daidai ba ne rashin gabatar da wasanni kafin jima'i, domin kuwa Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

    Idan ɗayanku ya yi nufin kusantar iyalinsa, to a samu ɗan aike a tsakaninsu.

    Sai Sahabbai sukace:

    Wanne irin ɗan aike ya Rasulillah {s.a.w}?

    Sai ya ce: Sumba ta da runguma (Wasannin).

    Rashin gabatar da irin waɗannan wasannin yakan haifar da rashin gamsuwar Jima’i.

    Shi kuwa rashin gamsuwar Jima’i yakan haifar da matsalolin da za su kawo rabuwar auren.

    Yana daga cikin fa’idojin gabatar da waɗannan wasannin, zaisa Maniyyin ita macen ya gangaro daga ainihin inda yake, sannan kuma z ta sami cikakkiyar gamsuwa.

    Haka shi ma namiji yana taimaka masa wajen daɗewa yana jima'i baiyi saurin inzali ba.

    YIN SURUTAI A LOKACIN JIMA’I

    Shi ma wannan ba daidai ba ne, Shari’ar musulunci ta hana mutum ya rinƙa yin magana a lokacin da yake tsirara inda a bisa lurara ba.

    RASHIN LULLUBE JUNA DA MAYAFI

    Shi ma wannan ba daidai ba ne, yin hakan ya yi kama da Jima’in dabbobi, anaso mace da mijinta su ɗan rufe jikinsu da wani ɗan mayafi, sannan kuma idan da daddare ne a kashe fitila.

    RASHIN AMBATON ALLAH KAFIN FARA JIMA’I.

    Ya kamata ma’aurata su kula da yin Bismillah tare da karanta addu’ar nan wacce Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce duk wanda yake karantawa ya yin Jima’i da matarsa, to indai aka samu rabo, to shaiɗan ba zai iya cutar da yaron ba. Ga addu’ar nan:

    (BISMILLAHI ALLAHUMMA JANNIBNASH SHAIƊAN WA JANNIBISH SHAIƊANA MA RAZAƘTANA)

    Amma Namiji ne zai karanta ba mace ba a lokacin jima'i.

    SAURIN SAUKA DAGA AN GAMA

    Idan miji ya biya buƙatarsa, to bai kamata ya gaggauta sauka ba, har sai ita ma matarsa ta biya buƙatarta, kada ya yi saurin zare azzakarinsa, sai ya ɗan jira kaɗan face har sai ta buƙaci ya cire.

    RASHIN SAUYA YANAYIN KWANCIYA.

    Shi ma wannan ayar Alƙurani ta bada damar miji ya sadu da matarsa bisa kowanne irin yanayi,

    A tsaye ko a zaune ko a kwance ko a tsugunne, mutuƙar dai ba ta dubura ba ne.

    Don haka ya halatta ma’aurata su riƙa canja yanayin kwanciyarsu saboda ƙarawa juna nishadi.

    SADUWA A LOKACIN DA TAKE CIKIN JININ HAILA, KO JININ HAIHUWA.

    ALLAH {S.W.T} ya ce:

    Ku nisanci mata a lokacin haila, kada ku kusancesu harsai sun yi tsarki.

    SADUWA TA DUBURA

    Shi ma wannan ƙazanta ce wacce ko dabbobi basayi.

    Manzon ALLAH ya ce:

    Tsinanne ne duk ƙanda ya sadu da mai haila kuma ya sadu da mace ta dubura.

    ALLAH ka bamu ikon kiyayewa, ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.