Ticker

6/recent/ticker-posts

Halaccin Tsotsan Farjin Mace Ko Namiji A Ya Yin Saduwa

Ya halatta a shariah mace ko mijinta su yi wasa da bakinsu a farji kafin saduwa, sai dai ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin mata, saboda yadda ALLAH TA'ALAH ya yi musu tasu halittar.

Domin kuwa guri ne da ake yin haila, ake kuma zuba maniyyi, gashi kuma yana kusa da wajan yin bahaya, wasu masana likitanci suna bada shawarar cewa: a rinƙa wanke gurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda neman kariya.

ALLAH TA'ALAH a cikin suratul Baƙara ayata: 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai ya nuna dukkan ɓangarorin jikinta ya halatta aji dadi dasu, in ban da cikin dubura wacce nassi ya togace.

Duba: Mawahibul-jalil 3\406.

ALLAH shi ne mafi sani.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu Ameen.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments